← Book details Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 60

Sashe 50

Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yarima da Tina an sake dinkewa,a zuciyarsa yana kara shige matane da tsawonta da tsawon gashinta suna tuno masa da beauty, ita ma ta fahimci yana da wata a cikin zuciyarsa domin in suna kwance sunan beauty kawai yake kira.sannan inya shiga wanka takan dauki wayarsa ta masa bincike tana son sanin wacece beauty din nan?Yaya take ne don ta samu matsayi mai girma gurin wannan tsadaddan yaron.Kimanin wata hudu kenan da tafiar Yrm,cikinta kuwa yana wata biyar kenan tana zaune tana cin kwakwa da tasa aka siyo mata, Sumayya ce ta shigo tana sanye da leshi ja da kuma ratsin baki yaune zuwanta na uku gidan,ta zauna tare da cewa Maman biyu,Bily tayi ‘yar dariya tace,Allah amin ya biya bakinki Sumayya tace amin.nan suka soma hira duk data hakura da Yarima amma duk sanda ta gansa ko taga hotonsa sai taji ma kanta haushin rashin samunsa, yanzun ma da take zaune kallon hotonsa takeyi tare da yaba kyansa, cikin zuciyarta. Bily tace,Sumayya kina kallon wuta ne fa,yakamata ace yanzun kin cire Yarima acikin rayuwarki,sannan ki godema Allah daya baki Magaji matsayin miji,tace ai tuni na hakura anty Bily, matsalata daya yanda zan cire shi daga zuciyata,ki dinga addu‘a inji Bily,ki rike mijinki Sumayya so da yawa abinda ka kwallafa rai kansa baka samesa ba to sai kiga alkairi ne rashin samun,ni kaina ban taba tunanin zan auri kamar Yarima sa‘ana ba,babu irin takaicin dabanyi ba game da auren amma yanzun sai ina ganin alkairai da dama acikin aurenmu.don haka ki kama mijinki ki samu ladan aure,Sumayya tace to nina rasa sam sai inga sam Yarima yafi Magaji komai, Bily ta hade fuska Sumayya lallai zaki daina zuwa gidana,domin babu wanda yafi wani gurin Allah face wanda yafi tsoronsa,in dai kina so mu shirya to ki kama mijinki. Sumayya tayi ‘yar dariya ganin ran Bily ya baci,tace na daina anty Bily,shima Magaji cewa yake duk ranar dana zo nan gidan wai bana bata masa rai,shiyasa yake son inzo gurinki,ina aiki da shawararki,nan dai suka cigaba da hirarsu.Wani dare Bily tana bacci sai kawai tayi mafarki wai ga Yarma an kawosa ya rasu,nan take ta farka duk tayi sharkaf da zufa,ta kalli agogo sha biyu da ‘yan mintuna duk da lokaci ba daya ba ne ji tayi bazata iya komawa bacci ba har sai taji muryarsa nan take ta kira layinsa daidai lokacin ya shiga wanka,Tina ce kwance rigingine a tsakiyar gadonsa,don haka wayar tana yin ringing ta dauka ta duba(beauty)taga an rubuta,da sauri ta daga wayar tare da cewa, wacece ke?Cikin harshen turanci. Bily ta tsorata, gabanta na faduwa tace,kiba mai wayar,Tina tace sai ta fada ko ita wacece,ran Bily ya baci dama Yarima yana nan yana harkarsa da matan banza,shine yace mata ya daina?Wani tukuki taji azuciyarta nan take ta kashe wayar cikin tane ya shiga murdawa,ji take tamkar zata haihu Yarima yana fitowa daga toilet din yaga phone dinsa ahannunta,nan take tayi saurin cewa an kiraka amsar wayar yayi ba tare da yace mata kalaba,koda ya duba yaga beauty ce ta kira kuma har ta daga nan da nan sai yaji hankalinsa ya tashi,da sauri ya soma kiran layinta,tamkar kada ta daga amma sai ta kasa tana dagawa sai ta saki kuka ya rasa me zaice,sai yace kiyi hakuri beauty na kasa controlling din kaina ne yau amma insha Allah bazan sake ba,na amsa laifina kiyi min addu‘a kinji?Cikin shesshekar kuka tace, Yarima baka min adalci ba,yaya na tsare kaina a gida kaika dinga bin wasu,ina tsoron kada Ayar Allah ta sauka akaina,domin Allah yace in har kabi matar wani sai anbi taka,in ‘yar wani kabi kaima za‘a bi tak,haka kuma mazinaci baya aure face sai da mazinaciya ‘yar uwarsa,ban kasance mazinaciya ba. Yarima ma jikinsa yayi sanyi yasan gaskiya ta fada ina ma gata gashi ne ya rungumeta tare da lallashinta, duk da haka sai yace na sani beauty ban kyauta miki ba,amma kada kiyi fushi dani zan shiga damuwa kinji?Tayi ajiyar zuciya,sannan tace bazaka daina ba Yarima ,yace ki daina fadin haka,insha Allah zan daina nidai kimin afuwa, tace Allah zaka roka donshi kayiwa laifi,da sauri yace zan rokesa,don Allah beauty kadaki kashe min waya kinji yanayin yanda yayi maganar sai taji dadi,tace bazan kashe ba
[2/19, 10:07 AM] ‪+234 803 225 4928‬: 🏵MEKE FARUWA 83🏵

Zuciyarta tayi sanyi domin lokutan baya Yrm yana neman matansa a gabanta, zai iya kwanciya da mace a gabanta,amma yau gashi wayarta kawai mace ta daga duk ya birkice, ta san ko har yanzun Yrm yana neman mata to ta samu wani matsayi agurinsa tunda yake boye mata baya son ta sani,bugu da kari Yarima ne harda bata hakuri,tayi mamaki domin tasan sa sarai baya daga cikin mazan da suke bawa mace hakuri,baya lallashin mace amma ita sannu a hankali ya soma yi mata abubuwan da yake ikirarin bazai iya yiwa mace ba, zata dage da rokon Allah har Allah ya shirya mata shi. Shi kuwa Tina ya tsirama idanu cike da bacin rai irin wanda bata taba gani ba,don haka ta tsorata har ta shiga bashi hakuri,cewa yayi ta fita kawai.tana fita ya fada kan gado yana rubuta ma beauty dinsa text na ban hakuri, sai daya gama sannan yayi shiru yana mamakin kansa,shine Yrm kuwa?Shine mai ja ma mata aji? Shine wanda mata suke bi bashi ne ke binsu ba? To menene yasa shi rikicewa kan beauty?Yanda ya dade dasu Vicky bai dade da Bily haka ba me yasa zuciyarsa bata shaku dasu kamar yanda ya shaku da ita ba?Me yasa ita baya jin ta gunduresa?Me yasa baya son bata mata rai ne? Domin inya bata mata rai zuciyarsa sai ta ringa yi tamkar zata fashe,bai saba da damuwa ba,don haka baya son zama cikin damuwa,inya bata mata rai sam cikin damuwa zai zauna shiyasa yake kiyayewa.

A kwana atashi babu wuya agurin Allah, yau gashi Bily an shiga watan haihuwa.duk wani abu daya kamata mai jego da jariri ‘yan gata su bukata, tuni Umma ta tanadeshi, can ma Zaria su Mama suna ta shirye-shiryensu na talakawa. Yrm ko hankalinsa ya kasa kwanciya ina ma a hannunsa beauty zata haihu baya son ya rasata,wayewar garin Alhamis ta tashi da ciwon haihuwa,tuni Umma tasa akayi asibiti da ita,inda take awo wato asibitin Doctor Aisha.har zuwa yamma shiru Modibbo ne yayi mata wasu addu‘o‘i ya tofa su cikin ruwa aka kai mata daidai lokacin Yrm ya kira wayarta har ya gaji,ya kirata cikin gida,Asabe ce ta dauka ya tambayeta Bily,nan take shaida masa tana asibiti zata haihu,yace tun yaushe? Tace tun jiya,nan take ya kira Magaji,Magaji yace duk suna asibitin ance nan da awa daya zata haihu,tsaki kawai yayi nesa bata maganin kusa,amma in yaga za‘a bata masa lokaci xai bar komai duk da suna tsaka da karatu,kasancewar sun kusa gama course din ya kira wannan ya kira wancan har awa dayan ta shige ya kara minti talatin duk yaji babu bayani,nan take sai ya soma shirin zuwa gida. nasa ganin likitar bata san aikinta ba,domin in shi zai amshi haihuwa ne yana ganin cikin awa daya mace zata haihu. sai washegari sannan ya samu tasowa, bai sanar da kowa cewa yana hanya ba kuma yana cigaba da kiran waya suna sanar dashi ta kusa harma ya soma tunanin ko ta mutu ne suke boye masa? Yana dira dama daga shi sai kayan jikinsa,yayi wa Magaji waya,wane asibitin?Suka masa kwatance ya nufa, doguwar nakuda Bily tayi likitar tace su kwantar da hankalinsu zata iya haihuwa da kanta. ana cikin haka sai ga Yrm,duk suka cika da mamaki, office din likitar ya nema ya shige ya nemi son ganin matarsa kasancewar tasan aikinsa ne bata musa ba,suna tafe tana masa bayani shiko saurarenta baiyi ba shi dai burinsa shine ya isa gurin matarsa.yana shiga ya ganta tana ta fama ga Nurse kanta a tsaye ya isa gurin da sauri ya kamota lokacin abun ya kan kama sosai,nan ya shiga aikinsa cikin minti tara dan ya sawo kai,nan Yrm ya jawosa ya mika ma Nurse bayan ya yanke cibi.bai ko tsaya kallon yaron ba shita matarsa yake,duk abinda ya dace shine yayi mata,sannan yayi mata allurar hutu. Koda ya fito ana ta kallon jariri wannan yaba wannan, wannan yaba wancan duk sai yaji sun bashi haushi,su ta yaro sukeyi ma ga matarsa can a galabaice.shi kam me zaija masa kara haihuwa?Gida kawai ya nufa,ya watso ruwa,yana dawowa tana farkawa. Ta dubesa da dan murmushi,me muka haifa?Ya dan daure fuska bakiyi murna da ganina ba sai abinda kika haifa ko?Ta yunkura ta tashi,yayi saurin riketa kada ki tashi tace naji karfi fa ya zauna kusa da ita,tace naji dadin zuwanka sosai mana.
[2/19, 10:08 AM] ‪+234 803 225 4928‬: 🏵MEKE FARUWA 84🏵
Chapter 50 · 0% Book details