← Book details Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 60

Sashe 27

Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sannan ta koma yiwa Bily hirar kayan gyaran jiki,Bily tace don Allah ki kyale ni kina yi kamar baki san wanda na aura ba,wannan yaron ne zan tsaya ina damun kaina saboda shi?Ta dan ja tsaki kinsan Allah koda ina son shine wallahi bazan bata kudina ba gurin wani gyara jiki saboda me ma ya sani game da auren?Ballantana ma ni bai min ba,ba sonsa nake ba shima haka. Mansu tayi dariya har da kwanciya, sannan tace,Bily baki san matasan yanzun ba kenan?Bily ta kwanta tana fadin barni da zancan nan kinji in huta,bacci nakeji. Mansu tace gobe ai ba kya yi shi ba,in mun watse, Bily tace sai ki hanani.Mansu ta kwanta tana cewa,in ban hanaki ba ai Yarima ya hanaki. Cike da tsokana tayi maganar,irinta kawaye. Banza Bily tayi mata taci gaba da addu‘o‘inta na bacci,ta rumtse idanunta duk da cewa bata da tabbacin cewa baccin zai dauketa ko a‘a.Washegari sabon biki ne ya tashi gidan sarki dama su Umman Mansu suna can gefen Umman Yarima tare da su Gwaggo Ladiyo duk dai iyayen suna can matasan ne kurum anan gun amarya.Misalin sha biyu ‘yan yiwa amarya kwalliya suka shigo,sai da sukayi mata turare kusan kala goma daga ita sai vest da skirt,hatta gashin kanta yasha turare iri-iri,sannan ta saka wani leshi marar nauyi aka nade ta da laffaya,zobuna sarkar kafa,‘yan kunne,abin hannu. Subhanallah,haka mutane suketa fadi aka fito da ita zuwa falo ana jiran Yarima zasu je gurin sarki yasa musu albarka,sannan azo ayi budar kai.Shi ko gogan yana can ana fama dashi, jakadiya da Magaji sun tasasa da lallashi suka koma masifa.Magaji yayi zuciya ya fita,jakadiya cewa tayi bari taje ta sanar da Umman shi har takai bakin kofa yace jakadiya ta juyo yace yanzun me kike son inyi?Ta dawo cike da fara‘a da kirari,sannan tace ranka ya dade da guda tamkar da dubu wanka zaka soma yi kayi shiga ta alfarma,gimbiya fa na jiranka a falo,na gode ranka ya dade sai ka fito.Ya bita da kallo har ta fita,sannan yaja tsaki ya shige toilet kusan awa biyu ya dauka sannan ya fito yana shigowa falo kuyangi suka mike jakadiya ta tasasu lallai ga zara ga wata, Suka ratsa jama‘a har fada inda sarki yake zaune tare da fadawa da kuma manyan baki ‘yan taya sarki murna.Sun zube sunyi gaisuwa suna zaune gaban sarki yayi musu addu‘a sannan yasa musu albarka ya umarci waziri da a miko masa alkyabba ta musamman ce ya tanade ta don yau,nan take yasa ma Bily.Wayaga gimbiya Bily,sarki da kansa yasan dan nasa yayi dace,nan malamai sukayi addu‘o‘i,sannan marokan sarki suka dora busa da kirari,su Bily suka fito mata suka dau guda ga kuyangi cikin ado suna biye dasu,sai gurin da aka gyara don budar kai,wani katon fili ne nan cikin gidan yasha decoration nan akayi budan kai.Ango da amarya sun samu kudi babu ma kamar ango inda matan sarakai kawan Ummansa da matan Gwamnoni zuwa masu fada aji,banda kyautar kuyangi daya samu daga sakkwato.Ana gamawa dama kamar yana kan kaya ne,suka nufi masallaci da suka dawo wanka yayi sannan ya saci jiki ya fita,wani guest house ya nufa ya kama daki yayi kwanciyarsa da nufin hutu.Su ko can gidan anci gaba da ‘yan bukukuwa,yayinda wasu bakin suka soma nade kayansu don tafiya gida.Ciki har da dangin Bily wadda hakan yayi mugun daga hankalita, musamman da taga Mansu ma tana hada kaya,ta zuba ma Mansu idanu tace,Mansu me kike nufi ne? Tace Gombe zanbi mijina,Bily tace ki daina min wannan magana,gaskiya bazaki tafi ba,kuna nufin ni kadai za‘a bari bansan kowa anan ba?Mansu tana dariya tace,ba auren kenan ba?Bily tace amma ke ai na zauna miki. Mansu tace a ina? Tuna dai haka kuka kai ni Gombe kuka baroni,nan take Bily ta soma kuka tun Mansu tana tsokanarta har tazo tana bata magana,itama tana hawaye yanda Bily take kuka duk su Umma Mansu babu wanda baiyi hawaye ba,amma suka ki su kara kwana.Amma Faruk yace kafin su koma Kaduna zasu biyo su Sakina da Maryam suna kuka suka tafi,amma an bar mata auta kafin hutunta na makaranta ya kare,duk daba azo mata da kaya ba tunda ba‘a shirya za‘a barta tun daga gida ba,Umman Mansu ce tace abarta kafin Magariba duk an gama tafiya sai Bily kwance kan gadonta tana ta kuka,auta ko tana falo tana ta kallonta.
[2/19, 9:58 AM] ‪+234 803 225 4928‬: 🏵MEKE FARUWA 47🏵

Can dai taga bata da nayi sai hakuri,don haka ta tashi ta shiga toilet ta dauro alwala tazo ta tada sallah,Asma‘u itama tazo ta tada tana zaune har isha‘i tayi,tana idar da sallah kuyangi suka shigo suna shaida mata batun cin abinci,tace ita kam alhamdulillah,sai dai ga kanwarta nan su bata. Yinin ranar ma ita banda ruwa babu abinda tasha, balle abinci,haka nan suna kwance ita da Asma‘u bacci ma yayi gaba da ita ko kayan jikinta bata cire ba,duk ta gaji take jin jikinta tana cikin baccin taji muryar jakadiya tana cewa,ranki ya dade har kin soma bacci ne?Bily ta tashi zaune,jakadiya tace wanka zakiyi yanzun.Bily kamar tace ki barni inyi baccina,amma sai ta daure tace to ta mike taje tayo wanka sannan tazo zata sa kayan bacci kenan sai ga jakadiya,tare da wasu kuyangin suna dauke da wasu kaya cikin kwalaye,nan take suka shiga yi mata kwalliya, shafa wannan goga wancan fesa wannan gashi kai ma yasha turare yafi kala goma.Jakadiya tana gefe sai data bada izinin su bari sannan ta mika mata wani kwali,kisa wannan ina dawowa.Ba musu ta amsa,jakadiya ta tasa su suka fita,Bily ta bude kwalin nan ko ta dago wata shegiyar rigar bacci bata taba ganin irinsu ba,koda yake yaushe ma ta shigo garin?Cewarta nan take ta saka har da takalmi,jim kadan jakadiya tayi sallama tare da neman izini.Bily tace shigo bayan ta shigo tace ranki ya dade kinyi kyau yanzun sai ki zo muje gurin Yarima.Ita kuma ‘yar uwar taki zanje da ita can gurin Umma mai babban daki.Kamar ta gaddame amma sai ta tuna da maganarsu Umman Mansu,inda suke cewa,ki zama mai biyayya musamman kasancewarki acikin gidan sarauta su ba‘a gaddama don gidan ilmi ne da tarbiya,don haka sai ta mike tabi jakadiya.Suka fita ta cikin falonta suka shiga wata kofa nan ma wani dan madaidaicin falone sannan suka kara shiga kofa,nan ma karamin gurin hutawane ko yin karatu,sai kuma ga kafar bene tayi sama.Bily dai tana biye da jakadiya suka hau sama nan ko wani hamshakin tafkeken falo ne mai tsari.Jakadiya tayi sallama shiru ta nufi wata kofa daga cikin kofofi ukun dake falon ta kwankwasa. jim kadan aka bude,Yarima yana sanye da jallabiya,ya dubi jakadiya kafin yayi magana tace,ran Yarima ya dade,amarya na kawo maka.Ta juyo ta yafito Bily da hannu,Bily tazo ta tsaya kusa da jakadiya. Jakadiya ta nuna mata dakin tare da cewa,mu kwana lafiya.Yarima dake bakin kofar ya hana hanya tare da cewa,haba jakadiya, kuna tirsasani da yawa,shin bata da daki ne?Tana dashi ranka ya dade,amma addini yana tafiya daidai da al‘adar gidan nan,ga al‘adar wannan masarautar gimbiya Bily bata da gurin kwana sai dakinka,kuma saba ma hakan laifine babba.Jakadiya ta dubesa in kaji zafi Allah ya huci zuciyarka,mu kwana lafiya,ta fita.Yarima kam falo ya fito,Bily ta shige ciki.Subhanallahi!!Ta furta afili tare da hangame baki tana kallon dakin,afili tace jama‘a kamar baza‘a mutu ba? Gado ne gashi nan kamar na zinare,in ma ba gold bane to kalar ce asaman gadon.Akwai wasu fitilu kusan guda sha biyu kaloli daban-daban,gadon kawai suke haskawa sannan ga wani net mai ruwan madara ya rufe gadon ruf.Ta tsakiyar net din fitilun suke,ta kai duba kan gadon yana liliye da shimfidu na alfarma ga fuloli da yawa kanana da kuma manya.Kujera daya ce adakin katuwa,sai madubi suk seti suke da gadon,kafet zuwa labule masu kalar madara ne kila ma tare suka zo har da net din.Tana ciki tana wannan juyayin shi ko Yarima yana falo shaidan na tuno masa da sa‘in‘sar su shi da Bily,kalmar jahilci data tofa masa da kuma kiransa yaro sune suka dinga yawo cikin kansa nan take zuciyarsa ta shaida masa cewa ka nuna mata aikin jahilci dana yarinta zunbur ya mike ya nufi fridge din sa ya ciro wani jus na kwalba ire-iren wadanda yafi sha,ya dau kofi ya nufi dakin.Bily tana tsaye ta jingina bayanta da bango,bai ko kalleta ba ya nufi kujera ya zauna, sannan ya jawo dan tebur din gabansa ya jawo wata durowa ya ciro fakitin magani,ire-iren magungunan da suke sha da su Chelen in zasu aikata masha‘arsu,ya balle hancin kwalbar ya tsiyaya jus din cikin kofi ya afa kwayoyin ya bi da sassanyan jus din
[2/19, 9:59 AM] ‪+234 803 225 4928‬: 🏵MEKE FARUWA 48🏵
Chapter 27 · 0% Book details