← Book details Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 19

Sashe 8

Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin wata irin razana Yarima Sageer ya wara manyan idon sa ya dubi Saadatu, da iyakacin girman su, a ina ta ji wannan maganar? Ya bude baki zai yi magana, ga dukkan mamakin sa maganar ta makale ta kasa fita, kafin ya ankara Saadatu ta mike ta nufi kofa da zummar ficewa.
Da wani irin zafin nama Yarima ya sha gabanta, ya kama duka kafadunta biyu ya girgiza ta da karfi. Sai da kashin kafadar ta ya amsa. Bata san sanda tace,
zaka balla ni!. A kausashe Dr. Sageer yace.
“Kin san da wa ki ke magana Saadatu? Are you scolding me?
Hawayen da ke tare cikin idanunta suka idasa gangarowa akan kuncin ta, ta ce cikin karyayyar murya marar amo da rashin karsashi.
Im not scolding you. Kawai ina gaya maka abinda na dade da sani ne a kan ka. Na san da wa na ke magana mana; Yarima ne, Yariman Askira, Yarima Sageer mai jiran gadon Askira, amma ba mai halin real Askirama ba
Shi Askirama ba ya zina, matan sa ba sa shan giya, ba sa zuwa Bar, sannan suna yin sallah”.
Ta bude dukkan idanun ta dake jike da hawaye ta cigaba da cewa A gidan Yarima duk ana yin wadannan abubuwan dana lissafa, don haka babu ni a wannan gidan. Matattarar shaidanu da sabon Allah.
In kuma aka takura min sai na bi ka, wallahi zan gudu! Ba za ku kara ganina ba, da ma ba ku san daga ina na zo barana daya kawai kuka ganni a gidan ku, don bani da gata ubana talakane kuma ya mutu, ni sai a yi min aure ba izini na.
Saadatu ba ta yi aune ba idanun ta bakidaya a rufe, tana ta zubda rashin kunyar ta ta hanyar fadin duk abinda ya zo bakinta wa Yarima, ta hakan ne kawai zata amayar da kuncin dake zuciyar ta, tunda in ba shi din ba wa zata iya gayawa wannan? Burin ta ya ji haushi ya bar musu sassan su, in yaso kada ya kara dawowa.
Ba zaton ta ba tsammani ta ji Sageer ya janyota jikin sa gabagadi da wata irin azama da zafin nama, jikin sa na shaking [tsuma] kamar kamar bai taba rike mace ba a tsayin rayuwar sa sai wannan karon. Har kuma ran sa da zuciyar sa abinda yake ji kenan a zahiri. Kafin ta yi kokarin zamewa ko kwacewa sai jin taushin bakin Yarima Sageer ta yi ya sauka a kan nata ya sima sumbatar ta in an abrupt manner, wanda hakan ya rufe sauran bakar maganar da ta ke so ta furta. Cewa ita a rasa wanda zaa aura mata sai mai yin zina? Ba gara Saidu ba? Kafin ta tantance what is going to happen next? Dr. Sageer ya soma hawaye, bai taba nadama ba akan rayuwar sa irin yau, gabadaya jikin sa yayi sanyi da kalaman Sa'adatu, ba tare da yayi shawara da zuciyar sa ba ya fara sumbatar ta gently, expertedly, and then by dragging her closer, sai ya cigaba da kissing dinta softly, then a urunce wato [da sauri da sauri].
Tun daga karkashin zuciyar sa sautin sumbar take fitowa tana bada sauti. Duk kokarinta na kwatar kanta hannun Yareema ta kasa sai da ya yi sumbar mai isar sa tukunna, ya sanyata cikin jikin sa a hankali ya rungumeta tsam-tsam ta hanyar hada bugun zuciyoyin dake cikin kirjin su wuri guda, inama zata iya jin tari nadamar dake cin ran sa daga bugun kirjin sa? Yana yi yana sauke kakkarfar ajiyar zuciya. Sai kuma ya bi hawayen fuskarta yana dauke su tsaf da lips din sa. Ya dago fuskar ta da hawaye kadai ke zuba tana kakabin abinda ke faruwa a mafarki ne ko ido biyu?
Dr. Sageer ya sanya fuskar ta cikin tafukan sa, sannan ya sake ta ya ja da baya kadan yana jifanta da wani irin sassanyar kallo, wanda Saadatu ba ta taba gani a tare da shi ba. Gabadaya ya rikide mata ya koma tamkar ba shi ba. Ga dai nadama ce fal da tsoron rasa Sa'ade a ran sa tunda ta san ko wanene shi, amma abinda ya furta ba lallashi bane ba kuma nadamar dake baibaye da shi bane. Yarima Sageer is always bold, baya yarda ya nuna weakness din sa a komai.
Kin fara da kissing mai yin zina Saadatu, kafin ku sha giyar tare ke da matar sa. Daga nan ku zarce BAR din ke da ita ku sha ku yi mankas ku dawo gida ina jiran ku. Na bar ki lafiya sai mun hadu a kauyen naku na Tsanyawa in kin gudu, amma ina rokonki don Allah in kin tashi gudun, ki fi ruwa gudu.
Ya zuba hannuwa cikin aljihu yana kara jifarta da killing smile dinsa wanda shi kadai ya iya abunsa, ya kuma san maanarsa.
Bai tsaya sauraron amsarta ba ya juya cikin sassarfa da takunsa na haiba da mulki ya bar falon. Ya bar Saadatu a tsaye kamar an kafe ta a wurin. Ta kai hannu ta shafo kasan lips dinta a hankali. Damshin yana nan. Haka kamshin mouth freshner din bakin sa yana nan. Shin abin da ya faru yanzun da gaske ne ko a mafarki ne? Ta yi kissing da mijin auren tafor the first time a rayuwar ta? Kuma ba kowa bane Uncle Yareema ne, guardian din ta na NTNU Dr. Sageer Yusuf Askira?
Ta fi karfin minti goma a tsaye, ta kasa maida nutsuwarta, ta kasa yardar wa kanta abin da ya faru ba mafarki bane, ta dauki everything as an illusion. Kafin ta ja matattun kafafunta ta zauna. Me wannan ke nufi tsakaninta da Yareema Sageer? Ba dai wannan shi ne rayuwar kusancin da ake nufi yanzu zasu yi tare har abada ba, maimakon tasu ta Guardian da step sister irin ta baya?
Koda take yarinya karama ta san me aure yake nufi a darasin biology. Kawai sai ta ji kuka ya kwace mata. Shikenan ita tata ta kare. Ta zauna a dandaryar kafet ta yi kukanta mai isarta. Kanta cikin cinyoyinta, kan ta har sarawa ya shiga yi.
Fanna da ke jiran fitowarta daga daya falon, ta ga fitar Yarima da sassarfa da jimawa, da ta ji shiru-shiru Saadatu ba ta fito ba, sai ta biyo bayanta ta same ta a zaune tsakiyar kilishin falon tana ta kuka.
A zuciyarta ta ce, Dole ki koka Saadatu, wannan mutumin ya fi karfinki ta koina. Da dai sun barshi da bayahudiyar matarshi ita kadai zata iya dashi, amma ina innocent yarinya irin Saade ina fitinannen Yariman Askira? Tun suna yara suke da labarin sa cikin gidan nan, wa ya san irin rayuwar da yake yi a Abujar?
Fanna ta tsugunna da gwiwa bibbiyu a gaban Saade, cikin lallashi da ladabi ta ce,
Ranki ya dade ki yi hakuri ki tashi mu koma daga ciki.
Tana so ta gaya wa Fanna damuwar ta. Don ta san ita kadai ce a yanzu zata saurareta har ta fahimce ta. Ko ta fada mata abin da Yarima ya yi a gare ta yanzun nan, da abin da ya ce da ita, amma sai ta ji ta kasa. Maganar ta yi mata nauyin da ba za ta iya furtata ga kowa ba koda kuwa Fulani ce.
Ta mike cikin mutuwar jiki, Fanna ta kama hannunta suka koma ciki.
Ta gaban Fulani da su Inna Laure da ke zaune suna raba kayan daFulani ta diddinka musu suka wuce zuwa dakin Saaden. Fulani ta daga kai ta dube su. Idanun Saade jawur da alama ta ci kuka ta koshi. Ko me aka yi mata kuma? Fulani ta fada a ran ta.
Suka wuce zuwa dakin Saade inda suka tadda Hanne tana gyara dinkunan Saaden da aka kawo daga wajen dinki. Fanna ta koma bayan shigar Saade daki.
Bisa gadonta ta haye ta ja duvet ta rufa har saman kanta. Ba ta son magana da kowa, don ko Hanne ba ta jin za ta iya gayawa abin da Yarima ya yi mata wanda ya kara tsoratata da auren.
Ita ma Hanne har ta gama abin da ta ke ta yi wa danta shirin kwanciya ba ta tambaye ta komai ba.
Fulani ta so ta kira ta don ta ji dalilin kukan da ta fahimci ta yi, wata zuciyar ta hane ta. Gara ta bar Saade ta koyi rike sirrin auren ta yanzu girma ya hau kanta. In dai ba matsala ce wadda ta zama dole su sani ba.

Washegari duka gidan ya rikice da hayaniya ana shirye-shirye. Kowa da ke cikin masarautar nan ya ci wa bikin nan na Yarima buri da alwashi don huce haushin wanda ba a yi ba a aurensa na farko.
Maimartaba ya aika da goron gayyata zuwa dukkan masarautun Borno guda bakwai, (Bama, Borno, Dikwa, Gwoza, Shani, Uba sai kuma Askira wadanda su suka hadu suka bada Borno Empire. Hakan nan ya aika da sakon gayyata har fadar Shehun Borno don haka Mai Askira ba karamin shiri yake wa wannan auren ba.
Duk wani gyara da ake wa amare na kayan mata Fulani ba ta yi wa Saade, banda Su dilke su halawa da dukhan kafin a mata lalle, (mai gyaran jikin Fulani daga maiduguri ta zo ta mata gyaran jiki), a cewarta Saade yarinya ce sai nan gaba in ta kara shekaru koda zata bata kayan mata, duk da tana tantama idan Yarima zai daga kafar yadda ya alkawarta. Kodayake fa bai bata cikakkiyar amsa ba akan hakan in zata iya tunawa cewa yayi zai duba.
Ta yi ajiyar zuciya cike da tausayin Saade, ta san duk ranar data shiga hannun Yareema sai Allah. Tunda dan Askirama ne.
Chapter 8 · 0% Book details