Sashe 16
Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yareema da Awaisu sun je sun gaida Alhaji Kyari, bayan sun gaida Maimartaba, sannan suka wuce cikin gida, unguwar Ya Gumsu suka fara zuwa suka kwashi gaisuwa, ta amsa musu kadaran-kadahan sai kallon Yareema ta ke da wutsiyar idanu kamar mai son gane cewa ya bi umarnin ta ne ko aah? Ya maida Saadatu cikakkiyar matar sa? Tsoronta Allah tsoronta ranar da Sageer zai hada shimfida da Saadatu, don ta san daga ranar ba za ta sake gane kansa ba,kamar yadda ba ta kara gane na ubansa ba tunda ya auri uwarta, kai ba ita kadai mahaifiyarsa ba, har waccan baturiyar tata ta kare. Ita ta san sirrin matan BAGGARA, ta san ta inda Fulani Bilkisu ta bi ta birkice musu kan miji kenan. Allah kadai ya san iya abubuwan da ta koya wa yarta, da sirrin mallakar da ta dankara wa Saaden(Allah Sarki ZATO. Mu kasance masu kyautata zato ga yan uwanmu musulmi, in ba haka ba za mu kare ne da daukar nauyin zunubansu. TAKORI). Daga wajen Ya Gumsu suka nufi unguwar Yaakirjiloma, Mairam Murjanatu na shirin tafiya tare da yayanta, tana ganin Yarima faraarta ta fadada, ta ce, Ka ga ango sha kamshi. Angon Saa da Aisha-Sultana. In ce ko an rago min kazar amarci? Dariya Yareema Sageer ya yi, don yana son Yayarsa Murjanatu sosai, tana da son zumunci da hadin kansu, shi sai yanzu ma ya tuna wai ana kai wa amarya kaza, shi haka ya tafi hannun sa na dukan cinya, dan banzan Awaisun nan kuma bai tuna masa ba, amma babu komai bari lokacin ya zo su koma Abuja, zai yi komai don Saadatu. Ko dawisu ne zai sa a gasa mata ba kaza ba. Ya ce, Mairam Murja, ba dai shirin tafiya ake ba? Na dauka za ku zauna har ku raka amarya Abuja? Murjanatu ta ce, Na so hakan, amma Ambassador ya yi waya maza-maza in koma sabida yara sun koma makaranta, kada ka damu za mu zo suna next year in Allah ya yarda. Yarima ya ji kamar ya nutse kasa don kunya, amma a zuciyarsa ya ji dadin wannan fatan nata, fata na gari lamiri in ji masu iya magana, kuma babu wanda zai so ta haifa masa Da a duniya irin Saadatu. Wani disappointment din is a blessing (Aisha Sultana da ta cire mahaifa) don an ce yaya suna tsotso dabiu da halaye na mahaifan su. Ya ce, Wa zai kai ku Maiduguri (airport)? Ta ce, Maimartaba ya bada mota da dogarai su kai mu, Humaira da Najaatu za su raka mu har su ga tashinmu sai su dawo. Ya fiddo wayarsa daga aljihun gabansa yana fadin, Bari in kira Suhail da Ahmad duk su raka ku, tafiya da maza za ta fi dadi. Ya yi magana da Ahmad da Suhail, sannan suka yi sallama da Murjanatu, suka karasa falon Yakirjinoma suka yi gaisuwa ta sa musu albarka. Ta kawo turaruka ta ce a kai wa Saadatu. Daga nan sai Unguwar Fulani Hibbani. Najaatu da Humaira suka gaida yayyun nasu, Sageer da Awaisu. Humaira sai faman dauke kai ta ke don tsananin haushinsa da ta ke ji, ya rasa wadda zai aura sai yar Fulani Bilkisu don kawai a wulakanta iyayensu? Ita tun filazal ta tsani Saadatu sabida son da Askirama ke mata, balle yanzu da ta zama surukarsa kuma matar Yarima dungurugum. Shi bai kula Humaira na ciccin magani da shi ba, ya dube ta da kulawa, ya ce, Auta, sai yaushe za a shigo mana? Ta yi wani dan murmushi na dole, ta ce, Matarka Yaya Yareema Junior ta ce fa, ya za a yi ni in je gaishe ta? Ai sai dai in ta zo nan mu gaisa. Cikin mamaki ya ce, Junior? Don sam bai gane me ta ke nufi ba. Ta ce, Kwarai, tare aka kai mu makaranta a El-Kanemi, ina aji uku tana aji daya, she has been washing my pants and undies, kai har gugar kaushi ta ke min, everything. Yareema ya kufula iya kufula saura kadan ya kai mata mari Awaisu ya rike shi. Ya ce, Saadatun? Wa ya ce miki baiwar gidanku ce? To yadda ki ke ya a gidan nan haka ita ma ta ke, idan watarana na ga kafarki a gidana sai na kakkarya ki, sakarai kawai. Ya Hibbani ta fito daga dakinta tana daura dankwali, ta ce, Yareema mene ne? Ina barci na ke jin tashin fadanka. Nan ya gaya mata a gajarce. Hibbani ta kyabe baki, ta ce, Kada ka ga laifin kanwarka Yareema, saboda da farko mu ba mu san yarta ba ce, boye mana ta yi. Cewa ta yi yar riko ce ta karbo, so don Humaira ta sa ta aikatau a makaranta ba ta yi laifi ba. Kada ka manta Humaira yar sarki ce, jikar Sarki. Wannan kuwa ko asalin ubanta ba mu sani ba. Idanun Yarima suka kada kamar gauta, ya bude dukkan idanunsa yana duban kishiyar mahaifiyarsa Fulani Hibbani, zai yi magana ya ce ita ma sun san nata asalin ba yar kowan ba ce, sadakarta aka kawo wa Askirama, Awaisu ya toshe masa baki, ya ja shi suka bar sassan gabadaya. Humaira ta ce, Humm! Aka ce auren hadi ne na Askirama, ashe da ma can yana sonta, dubi yadda yake neman dukana. Hibbani ta ce, Tabdijan! Ya Gumsu ta ga ta kanta, ai zama bai gan ni ba, bari in je in gaya mata Yareema ya gama afkawa har fiye da ubansa sai ta yi da gaske, kin ga yadda jijiyar kansa da ta wuyansa ke tashi? Humaira ta ce, Ni tunda nake ban taba ganin makiran mutane irin wadannan Baggaran ba, kyawunsu ke rudarSarakuna, amma wallahi kyawun da babu asali aikin banza ne. Hibbani ba ta saurare ta ba ta figi mayafi ta nufi Unguwar Ya Gumsu. Karya da gaskiya duk ta gaya mata, Ya Gumsu mai neman kuka an jefe ta da kashin awaki ba ta san sanda ta fashe da kuka ba tana fadin, Tawa ta same ni, ni Gumsu. To ba inda za ta bi shi a nan za ta zauna a Askira, ya je can wajen baturiyar ya zauna, ko ba komai su ba sa mugun abu, zuciyarsu ba muguwa ba ce. Bangaren Fulani suka nufa, Awaisu na ta cooling dinsa yana cewa ya yi hakuri, mata ne haka suke, sun gaji kananan maganganu wadanda bai kamata a biye musu ba. Sabida yadda ransa ke bace, duk tsokanar da Fulani Bilkisu ke masa ya kasa tankawa sai murmushi kawai yake. A karshe ta yi musu addua da fatan alkhairi. Ya sunkuyar da kai da ganinshi ka ga wanda ke gaban surukar da yake matukar girmamawa, ya ce, Allah ya taimaki Fulani, ina ganin fa gobe za mu wuce Abuja, nan hayaniya ta yi yawa ba ta barin mutum ya huta. Fulani ta ce, Haba Yareema, ka yi hakuri ku cika sati daya a gama miskero sai ku tafin. Ba da son ransa ba ya amince, don ba zai iya yi mata musu ba, amma kwarai maganganun Hibbani da yarta sun sa so yake ya dauke Saade su bar Askira. Ba zai lamunci kowa nasa ya taba mutuncinta ko na mahaifiyarta ba. Daga nan sai gidan su Awaisu wato gidan Wazirin gari Ibrahim, nan ma suka kai gaisuwa, sai gidan Galadima, Zanna, Shettima, Wali da dukkan king makers daya bayan daya sai da suka bi su suka kai gaisuwa, suka kuma yi musu godiya da ban gajiya. Sai goshin magriba ya dawo gida, Awaisu da ya sauke shi bai tsaya ba ya wuce gidansa. Awaisu na da matarsa Asiya har da albarkar yara biyu. Sanda Yarima Sageer ya shigo gidansa koina tsaf-tsaf sai tashin kamshin turaren wuta yake kuma koina shiru. Kuyangi da hadimai sun kulle koina sun wuce bangarensu. Saadatu ta gaya musu daga karfe shidda na yamma ta sallami kowa. Ita da za a raba ta da wannan tarin yammatan masu jini a jika daga gidanta da sai ta fi jin dadi, to ta san ba ta isa ta zauna babu kuyangi ba a matsayinta na matar Yariman Askira mai jiran gado, ba ta isa ta karya aladar masarauta ba. Zai wuce ke nan zuwa upstairsdin sa da zummar yayi wanka sannan ya zo ya duba Saade, sai ya ji motsin mutum, da sauri ya juya, wata siririyar kuyanga ce ta sha hoda da jambaki ta zube a gabansa. Allah ya taimake ka dan zakin duniya, sunana Sadiya ko da ana bukatar kwarkwara (sa-daka). Kamar daga sama sai ga Saadatu ta bullo daga kitchen din falon za ta wuce, ta yi wannan kyakkyawan gani ta kuma ji abin da Sadiya ta ce. Kofin tangaran na (mug) da ta hado zazzafan shayi mai kauri ta saki ya fadi kasa ba da saninta ba, ji-ka ke tush! Kofin ya tarwatse, gilashin da ruwan zafin duka a kan kafarta. Da sauri ta durkushe ta kama kafar wadda har ta soma fidda jini. Sadiya da Yarima suka yi kanta a tare. Wata irin tsawa da ta daka wa Sadiya sai da hantar cikinta ta kada, Dont touch me, get out! Ki hada kayanki duka ki koma cikin gida, kada in kara ganinki a sassana. Da gudu Sadiya ta fice ta san yau kashinta ya bushe, ta yi shuka a idon makwarwa. Babu bayani ga sauran bayi yan uwanta ta hada kayanta ta koma gidan Sarki a daren. Yarima ya sunkuya ya kama kafar, ta ture hannun sa tana kokarin janye kafarta. Azaba ba yar kadan ta ke ji a cikin tsokarta ba amma ta fi jin zafin tayin da Sadiya ta yiwa Yareema fiye da ciwon, kawai sai ya sunkuce ta ya yi saman benen da ita, duk inda suka wuce sai jini ya disa. Shi ba likita ba, amma ba ya rabo da first aid box a gidansa, toilet ya kai ta cikin jacuzzi ya wanke jinin ya cire kwalbar da ta makale tana kuka tana kankame shi, sannan ya sa mata iodine don azaba ba ta san sanda ta rungume shi ba. Ya dauko ta suka dawo daki bisa sofa ya shimfidar da ita yana ta faman jera mata sannu. He looked worried and disturbed kamar a jikinsa ciwon yake. Ya dauko pain reliever da gorar ruwan Faro ya ba ta ta sha. Ya