← Book details Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 19

Sashe 17

Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

kwantar da kanta bisa cinyoyinsa yana shafa kanta hankali. Saade sai ajiyar zuciya ta ke, amma bacin ran Sadiya bai gushe daga zuciyarta ba. Kamar Yareema ya fahimci hakan sai ya ce, Me ya sa ki ka kori yarinyar can? Da jajayen idanunta ta harare shi. Ba ka ji me ta ce ba ne? She wantto be your concubine bayan na ce kada in kara ganinsu daga karfe shidda, amma shi ne don ta raina ni ta dawo da ta ji dawowarka. Wani murmushi ya subuce wa Yareema, mace ba ta kishi sai a kan mijin da ta ke so, ko ta fara so. Ya ce, To me ye abun damuwa anan? Za ta taimaka miki ne ta dauke dukkan lalurorina har zuwa lokacin da za ki karbe ni a matsayin miji, tunda ba ki sona Saadatu ba laifi ba ne don sauran mata sun so ni, beside ba haramci ta fada ba. A hankali Saade ta janye kanta daga jikin Yareema Sageer, ta kwanta daya barin akan pillow, sabida yadda zuciyarta ke tafarfasa. A wannan lokacin ta tabbata da za ta ga Sadiya sai ta yi mata mummunan lahani. Yareema Sageer ya je ya kwanta a barin da ta maida fuskarta, ya yi mamaki da ya ga cewa kuka ta ke yi. Im sorry idan maganata ta bata ranki Saadatu. Gaskiyar magana ita ce, ba kya sona, ban san dai wa ki ke so din ba. Amma jikina yana ba ni wannan siririn yaron fari da na ke yawan ganinku tare nemai wuya uwa marikin lema. Ni na gaya maka? Ta tambaya cikin rishin kuka. Ban taba ce maka bana sonka ba Yaya Sageer, kuma ni ban taba son kowa ba. Karatu kawai nake so in yi. Auren ya yi min wuri, ka ga fa duka shekaruna sha tara, level 2 nake. Akwai sauran shekaru biyu a gaba kafin in yi nutsuwar da zan iya daukan marriage responsiblities, sannan baa nemi amincewa ta ba aka daura mana aure, ba mu fahimci juna ba in this aspect ta ya ya ka ke tunanin hankalina zai karbi wannan auren? Sosai Yareema ya fahimce ta, ya sanya hannu cikin jelunan kitsonta yana murzawa a hankali, ya ce, Na fahimce ki Saadatu. Ni kuma na ba ki dama ki ci gaba da yin rayuwarki yadda ki ka saba gudanar da ita a Abuja banda kula wannan yaron. Ni bazan takura miki ba. Insha Allahu ba abin da zai canza har sai lokacin da ki ka ji cewa you are ready to accept me as a husband, kafin nan ina so ki ba ni dama in zama malamin ki kuma aminin ki, mai koya miki karatu kuma abokin shawarar ki mai kula da dukkan alamuranki. Alfarma daya za ki yi mun, duk lokacin da zan sumbace ki kada ki ce min aa, ina matukar son in sumbace ki, na yi miki alkawarin ba zan wuce hakan ba. Da sauri Saade ta wara ido cikin jin kunya ta dube shi. A hankali ta ce, Yaya Sageer ina jin kunya!. Ya janyo ta gabadaya zuwa jikinsa, ya ce, I will take care of that daga yau, a hankali zan cire kunyar dukkanta har watarana da kanki za ki zo ki ce, Yareema Sageer.. Saade ta yi maza ta rufe idon ta. Ta cusa kai kasan filo. Shikuma ya yi amfani da wannan damar ya dauke filon ya kuma hade bakinsu wuri guda yana kissing din nata gently, softly, affectionately. Tun Saade na kokarin janyewa har ta soma lumshe yan idanunta. A zuciyarta tambayar kanta ta ke, wato bayan kissing din akwai abin da ya fi shi kenan anan gaba,tunda gashi Yareema yana cewa, ba zai wuce sumbar ba? To ko mene ne? Ko wace rana ce Yarima zai nemi hakan? Wannan din kadai sai ta rufe ido ta kuma kai zuciya nesa sabida nauyin sa..Idan akwai abin da ya fi shi a nan gaba ba ta san ya ya za ta yi da ranta ba. Sauran kwanakin su a Askira sai suka zamo na jinyar kafa da sassanyar soyayya, wadda Yareema Sageer yake matukar kokari wajen ganin bai wuce gona da iri ba. He is not going far beyond what he begged for. He is only kissing her, sumba mai sunan sumba in dai ga Saadatu ne ba ya taba gajiya, baya taba koshi. Rannan ya ce mata, “theres charisma in kissing You. Kwanansu shidda a gidan su na Askira kafarta ta kame, ya ce ta hada duk abin da ta ke bukata gobe za su bi jirgi tare da Maimartaba da Fulani zuwa Abuja. Alkawarin da Askirama ya yi na kaita Abuja gidan mijinta da kan sa ya ce zai cika shi da yardar Ubangiji. Washegari tunda asubahi an shirya motocin da za su kai su Maiduguri (filin jirgi) sannan an zabi wadanda za su yi wa Maimartaba da Fulani rakiya, cikin masu rakiyar Fulani har da Fanna wanda hakan ya faranta ran Saadatu sosai, fargabarta ta komawa Abuja ta ragu kashi sabain cikin dari ganin irin wannan rakiyar gata da zaa yi mata.
Chapter 17 · 0% Book details