← Book details Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 19

Sashe 18

Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

******

Jirgin Azman ya sauke su a Abuja da yamma lis. Direban Dr. Sageer da na abokinsa Dr. Ziyad su suka zo suka kwashe su a manyan motoci zuwa gidajen malamai na NTNU. Tunda suka sauko daga jirgi yake ta gwada kiran lambar Sultana tana ta ringing amma ba ta dauka ba. Ya san duk inda ta ke zuwa yanzu ta dawo gida. So yake ya gaya mata tahowarsu tare da su Maimartaba don ta sa Uche ya tanadi abinci na musamman, amma ga wayar tana ta ringing ba ta daga ba.
Ya yi tsaki, sannan ya kira Uche, wanda ke Baskwata a lokacin yana wanka, ita ya kamata ta bai wa Uche umarni ba shi ba, amma da bai same ta ba dole ya kira shi.
Uche, Im already on the way with his Royal Highness, cook to your best, deliciously. Madam ta dawo?
Uche ya yi shiru da waya a kunne, ta ya ya zai ce masa ta dawo, amma tun shigowarta tana main falo tana drinking kada ya zo da iyayensa yanzu? Kafin ya hada amsar da zai bai wa ogan nasa Sageer ya kashe wayarsa. Da sauri Uche ya hau sake kiran shi a waya amma rashin kyawunnetworkyasa yakasa samun shi. Kuma kafin ya sanya suttura a jikin shi ya wanke kumfar jikin shi ya baro baskwata (boys quarters) zuwa cikin gidan ya ji saukar dirin motocinsu suna shigowa get din gidan.
Duk da yake arne ya san drinking alcohol is very bad to Muslims more especially women in marital homes, its against their religion, tradition and culture. Sai ya ji tausayin ubangidansa ya kama shi, don yana son Sultana. Allah ya sa kada father din ya ce ya sake ta.
Yana daga kitchen wanda ya bi ya shigo ta kofar baya cikin mutuwar jiki yana lekensu ta window suna ta shigowa cikin nadi da amawali da kaya na sarauta a jikin kowannensu. Ga wata mace kuma an lullube a cikin alkyabba wata baiwa ta riko ta. Yarima ya bude kofar falon wadda sakayota kawai aka yi. Maimartaba shi ne farkon shiga don Yareema ya dan ja baya ya bashi hanya cikin girmamawa sannan Fulani ta mara masa baya. Suka kuwa yi kyakkyawan gani, wanda ba su jin za su taba mantawa a rayuwar su.

Aisha-Sultana ce daga ita sai half vest da wando three quarter baki, tana kwance magashiyyan cikin manya-manyan kwalaben whiskey. Ba barci ta ke ba, kuma tana jin shigowarsu amma ko yatsarta ba ta iya motsawa, idanunta a lumshe. Ba su taba ganin GIYA a fili ba, amma kallo daya suka yi wa kwalaben da kuma yanayin da ta ke ciki suka gane komai. Ko da ma can suna da labari. Kunya! A wurin Yareema kamar ya ce da kasar ta tsage ya shige. Allah ya so shi yan rakiyar sun tsaya daga waje, yau da ya gama tozarta a rayuwarshi.
Maimartaba sai kawai ya juya ya ce da Fulani, Bana zama a inda ake saba wa Allah, sannan yata ma ba za ta zauna ba. Ku juya mu tafi.
Yareema ya sha gabansa yana roko.
Alaguburo, Allah Kawun jo na tuba, na bi Allah na bi ku. Zan dauki mataki a ba ni dama ta karshe. Nan shi ne gidan Saadatu sabida cikin makarantar su ne. Ita na riga na kama mata wani gidan a Maitama, kusa da wajen aikinta.
Maimartaba ya yi tsaki ya fice, amma Fulani ba ta fita ba. Ya ce da dogarawan da ke bakin kofa a nema masa hotel din da zai sauka gobe da asubah zai juya inda ya fito.
Fulani ta ce da Yarima wanda ya zauna ya dafe kansa da dukkan hannayensa.Bai taba wulakanta irin yau ba. (Don ma ba shi aka kama a gidan Dr. Ziyad ba ke nan!) Kunyar duniya kenan da tozarcinta kafin a je lahira. Me ye riba a kin bin umarnin Allah kowanne iri ne? Bai san ya zai yi da Sultana ba, ya yi fadan ya yi nasihar, ya yi barazanar duka a banza. Har duka ya yi duk da ba girman sa ba ne. Nadamar nashi laifuffukan suka kara lullube shi. Mai yiwuwa ta nan Allah yake kama shi kan nasa laifin. Don kuwa duk da halin ta yana son kayar sa. A fili yake fadin,
Astagfirullah! Astagfirullah!!.
Ya kuma alkawarta ma ransa daga wannan ranar duk wani sabon Allah ya bar shi. Sultana kuma zai dauki mataki na karshe a kanta.
Fulani ta dafa kafadarsa, Ka kwantar da hankalinka Yareema, zan ba shi magana. Amma tunda ya ce ba zai zauna ba, to da gaske ba zai zauna din ba. Ka yi hakuri ka tashi mu je ka nema mana masauki, ita Saa zata zauna tare dasu Fanna zan bashi hakuri.
Tuni Fanna ta janye Saadatu zuwa dakinta wadda ke rufe cikin alkyabba ba ta san a kan me ake cece-kuce ba. Yareema ya mike yana hararar Aisha-Sultana wadda ke sakar masa murmushi cikin maye.
“Darling you.you are back?
Bai ce mata komai ba ya bi bayan Fulani suka fita.
Hotel din TRANSCORP HILTON ya kai su, ya kama musu daki na musamman kwana daya.
Saadatu ba ta san su Fulani sun juya ba, ita da Fanna kawai aka bari a dakin, ta dauka tare da su za su kwana cikin gidan suna wani dakin ne. Fanna kuma sai dauke mata hankali ta ke da hira don kar ta gane abin da ake ciki.
Haka ki ka tsara dakinki ranki ya dade gwanin shaawa? In mun tafi gobe sai ki kara tsara komai na gidan yadda ki ke so tunda ke kadai za ki zauna a cikin sa. Na ji maigirmaYarima ya ce Uche ya hada kayan uwargida ya sa a mota. Ki kula da cikin mijinki ta fannin girki bana jinki, na san Yareema ya gama morewa.
Haka ta yi ta hilatarta da daddadar hira har Yareema ya je ya dawo daga kai su Askirama Hilton. Ya leko kadan ya ce da Fanna,
In kin gama direba yana jiranku a waje zai kai ku inda za ku kwana.
Fanna ta gurfana tana godiya hadi da kirarin da suke yi masa, sannan ta dau jakarta tare da cewa da Saadatu.
Sai mun zo suna.
Idon Saade ya yi rau-rau kiris ta ke jira ta fashe da kuka.
Ta ce, Fanna Fulani fa?
Au, ta ce a yi miki sallama sun tafi masauki ita da Askirama, gobe kafin mu wuce za ta leko ku yi sallama.
Saade sarkin kuka nan da nan ta fara. Ya tabbata kenan ta shigo kwaryar sauran mata. Aure yau ya raba ta da Fulani, rabuwa ta har abada sai dai a je ziyara.
Ta yi kuka, ta yi kuka bayan fitar Fanna da ta gaji ta shiga bayinta ta daura alwala, tana jin Yareema yana ta yi wa Uche fada da harshen turanci kamar Charles Dickens ya diro Nigeria, kan don me sanda ya bugo masa waya bai gaya msa Sultana tana falo drunkard ba? Uche ya rasa kalaman kare kansa sai cewa ya ke,
“Im very-sorry Sir..
Yana so ya yi masa bayanin cewa wanka yake yi a baskwata lokacin, kuma kafin ya harhada bayanin da zai masa akan harshen sa ya kashe waya, ya bi bayan kiran network ya hana shi samun sa, ko kumfar jikin sa bai tsaya wankewa ba yasa wando ya fito kawai sai ganin motocin su yayi har sun shigo harabar gidan amma Yarima bai bashi damar yin wannan dogon bayanin ba sabida yadda ransa ya yi mugun baci. Wata muguwar tsawa ya buga masa ya ce ya bace masa da gani.
Saade ta kyabe baki ta tada sallah. Ai gara da Askiraman ya gani da idonsa, watakila shi in ya hana ta ta daina, tunda mijin nata ba shi da fuss a kanta, har nema yake a rufa mata asiri.
Ba ta san ya ya suka kare ba shi da matarsa. Ta fito ta shiga kitchen don ta sama wa cikinta abin da za ta ci ba ta gansu a falo ba, ba ta ga kwalaben giya ba. Ta dan tsaya tana nazarin falon ta ji tashin motar Yareema, ta daga labule ta leka ta waje sai ta hango shi ya yi ribas ya nufi get zai fita, Sultana tana gefensa kanta a kwance jikin kujera. Tsaki ta yi cikin jin kishi, ta ce a ranta,
Da kyar in ba shi ya dauke ta ya sa ta a motar ba, don in ta sha ta yi tatil din nan ko yatsanta ba ta iya motsawa, da ma ta gama gane shi gwani ne wajen daukar matarsa a hannu.
Ta zubo abinci iya wanda za ta iya cinyewa da Uche ya girka yanzun nan, ta zauna a dining tana ci. Shiru-shiru har ta gama ta koma daki babu Yareema. Tun tana duba agogo har barci ya ci karfinta, ta kishingide a kan gadonta, gadon yammatancinta a NTNU. A yau ya rikide ya koma na gidan aure! Kudurar Ubangiji ta fi ga haka.
Duk da bacci ta ke, amma zuciyar ta cike ta ke da damuwa, Yarima ya manta da ita cikin gidan ne ko kuwa? Ya dau matarsa sun fice. Ba ita ta bude idanunta ba sai da masallacin gidajen Malamai na NTNU suka tada sallar asubahi.
Ko da ta tashin ma da Yareema a ranta ta tashi. Ta yi zaton ganinsa a gefenta yana barci ko sallah, don ta gane shi maabocin sallah ne a zaman su na Askira kwanaki bakwai tare, kuma ya gaya mata muddin suna tare ba su ba raba makwanci, tun tana jin nauyi da kunya har ta saba da hakan cikin kwanaki bakwai da suka yi tare matsayin maaurata. Itama in ba sa manne cikin duvet bata jin dadin barcin.
Amma ga mamakinta har zuwa lokacin Yareema bai dawo ba. Tana alwallah tana hawaye, hawayen da ba ta san dalilinsu ba.
Chapter 18 · 0% Book details