← Book details Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 19

Sashe 2

Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fulanin Maimartaba, Allah ya baki yawan rai, na gode. Allah ya jikan magabata, insha Allahu ba zan ba ku kunya ba. Na karbi auren Saadatu da hannu bibbiyu. Allah ya ba ni ikon yin adalci a tsakaninsu.
Sosai Fulani ta ji dadin kalaman Yarima Sageer, suka wanke damuwarta kaso hamsin cikin dari na tunanin Yarimazai wulakanta mata Saade tunda yar talaka ce kuma yana da mata Baturiya, damuwar hakanta ragu daga ranta, don ba ta zaci haka zai karbi maganar ba with due respect, tunda uwar shi ma ba ta so. Ta ce,
Da kai da Saade duk daya ne a wurina Yarima, kamar yadda Askirama bai taba bambantata da ku yayan da ya haifa ba. Rokona daya gare ka Yarima ina so ka raba musu gida, sabida Saade ba za ta iya zama waje daya da Aisha - Sultana ba, shekarun su, tunanin su, akidunsu da halayyar su ba zai taba zuwa daya ba. Ka ga kuwa zama da juna zai musu wahala.
Ya saci kallon Askirama ta kasan idanun sa,sabida tsoron ko ya ji abin da Baggarar matar san nan ta ke fadi? Sai ya ga hankalin shi ba ya kan su sam, waya yake yi ma da yar sa Yaa Maira lokacin, wadda ke aure a masarautar Biu. Tana gaya masa cewa sun taso suna hanya har sun wuce Maiduguri.
Wani sigh of relief Yarima ya sauke da ya fahimci Askirama bai ji ta ba. A ran sa fadi ya ke na tabbata sanda aka yi miki aure da Baban Saade baki yi girman ta ba kuma kin haifeta lafiya. A fili kuma ya ce,
Insha Allah zan nema mata nata muhallin, daya bukatar kuma zan duba insha Allahu ran ki ya dade. Ai ba abinda zai gagara.
Da wannan ya yi musu sallama ya mike zai fita. Sai Askirama ya sake yafito shi.
Be a man also, after being a Prince (ka zama namiji bayan zama Yarima) wanda ba mai iya juya raayin sa, wanda ya san cewa mata da karkataccen haqarqari aka halicce su tunanin su ba kamar na maza bane, ka san yadda za ka lallaba mahaifiyarka har ta sauko daga dokin fushinta, ta karbi Saadatu matsayin diyar ta, ta sanyawa auren ku albarka. Tashi ka je ku tsara komai kai da Awaisu. Allah ya yi wa rayuwarku ku duka albarka.

*****

Yaa Maira ta iso daga masarautar Biu kamar yadda mahaifinta ya kira ta don ta zo su yi shirye-shiryen bikin dan uwansu. Haka Murjanatu ta taso dagaIstanbul tun jiya ta sauka Abuja. Zata biyo connecting flight zuwa Maiduguri yau.
Kamar yadda Maimartaba ya yi mata umarni cewa, idan ta iso kafin ta shiga koina ta fara ganinsa tukunna. Yaa Maira, ta bi wannan umarnin na mahaifin ta, ta yi saa babu kowa tare da Mai Askira lokacin da ta shiga falon ganawarsa da iyalinsa.
Ta same shi yana cin abinci. Ita dai ta ji an daura wa kanin ta Yareema aure, amma ba ta san da wa Askirama ya daura ba. Yanzu da ta ke durkushe a gabansa suna magana ta Da da mahaifi, bayan ya kare cin abincin sa sun gaisa, ta fahimci ko wace ce Maimartaba ya zaba wa kanin ta Yareema Sageer. Ba kowa bace face Saadatun Fulani Bilkisu!!!
Yaa Maira, wadda sunan ta na sarauta kenan, tana da wata baiwa ta daban kamar yadda na fada a baya ta sunsunar kaddara. Tun ganinta da Saadatu na farko jikinta ya ba ta wannan yarinyar will some day become part of them, za kuma ta zamo wani jigo a rayuwarsu. Zubin halitta da komai nata na Fulani Bilkisu ne, Bilkisun da ke juya zuciyar Maimartaba a halin yanzu. Bilkisun da babu tauraruwa mai hasken ta a idanun Mai Askira. Sai ba ta yi mamaki ba ko kadan da wannan zabin na mahaifin su domin BAGGARA matan manya ne. Abu daya ta ke so ta tantance yanzu shi ne hakikanin alakar dake tsakanin Bilkisu da Saadatu.
Mai Askira sai bai boye mata ba, ya gaya mata hakikanin alakar da ta hada Bilkisu da Saadatu.

Yar ta ce ta cikin ta!

Mamaki, alajabi da tuajjibi kamar ya zauta Yaa Maira, kodayake dama ta dade tana kiyasta hakan, kawai sai ta ji ta karbi Saade da dukkan zuciyar ta matsayin suruka. Duk da aibanta ta da Humaira ke yi duk sanda suka taru bata taba fadin wani mugun hali a tare da ita ba, in ka fahimci duka kushen Humaira akan Saade to kishi ne na son da Askirama ke mata da daidaita musu matsayi da yake yi lokacin suna makaranta. Sai ko taya uwar ta Yaa Hibbani kishi da Fulani Bilkisu. Sai kuma kyawun Saaden da take cewa irin na shegu ne.
Ita ta sani uwar Saade mai nagarta ce, cikin matan gidan kaf babu mai kirkin ta, saidai kishi ya hana aga hakan a kare da fadin aibun ta. Maimartaba ya sa mata albarka domin ta ce ta karbi amanar Saadatu a dakin su, ita ce uwardakinta daga yau, za kuma ta yi duk irin kokarin da za ta iya wajen ganin cewa mahaifiyarsu (Ya Gumsu) ta sauko ta sanya wa alamarin albarka.
Da wannan ta bar falon Askirama zuwa unguwar Ya Gumsu. Tana tafe tana saka irin lallashin da zata yi mata.
*****

Yaa Gumsu ta yi mamakin ganin Yaa Maira a daidai wannan lokacin, don dai ita da kanta ba ta gaya ko dayan su zancen auren Yarima da Saade ba saboda tsananin kiyayyarta ga auren. Yaa Maira ta kwaso gabadaya yayanta maza da mata sun taho, kallo daya ta yi wa Ya Gumsu, ta tabbatar da abin da Askirama ya gaya mata na cewa tana matukar adawa da auren, ba kuma don komai ba sai don kishinta da Fulani Bilkisu.

Ya Gumsu hakimce cikin royal chair ta babban falon ta, kuyangi na yi mata firfita da maficin gashin dawisu. Wasu na tausa mata kafafu, wasu na zubo kirari amma duka basu ishe ta kallo ba sai kumburi take kamar zata fashe. Ta daga ido tana kallon Yaa Maira da ke warware lafiyayyar laffayar jikinta don ta ji dadin hutawa, sun sha zaman mota daga Biu zuwa Askira. Take gayawa Yaa Gumsu. Ya Gumsu ta harare ta sosai, sannan a hassale ta ce.
To da ki ka kwaso bataliyar yayanki ku ka zo kuka cika min gida me ku ka zo yi? Wa ya gayyato ku? Na ayya gayyar sodi?”
Dariya Yaa Maira ta yi, ta ce,
Allah ya taimaki Gumsun Gari, mu ai ba sai an gayyace mu ba. Su Murjanatu ma duk suna hanya.
Ya Gumsu ta kara shaka sosai, amma ta ja bakinta ta yi shiru sabida kuyangin da ke zazzaune wasu a tsaitsaye, zuciyar ta na tafasa. Ta kara ganewa Mai Askira bai dauki auren nan da ya daura da sauki ba tunda har da kan sa yake gayyatar yayan sa abinda bai taba yi ba. Allah kadai yasan iya gayyatar da yayi da irin hamshaqan sarakunan da ya gayyato akan auren nan. Bata kara magana ba sabida kunar zuci. Kallo daya Yaa Maira ta yi wa kuyangin da ke wurin duk suka mike suka bar falon, suna masu yi mata kirari irin wanda suke yi wa diyan Ya Gumsu.
A tashi lafiya Yaa Mairar gida,
A gana lafiya uwar marayun Askira,
A fito lafiya cikin alheri Yaa Maira uwar diyan Yaa Gumsun Askira bakidaya..

Daidai kafafun ta Yaa Maira ta zauna suke kara gaisawa a nitse, gaisuwa irin ta Da da mahaifi, Yaa Gumsu na kokarin hadiye fushin ta, yaran duk sun bazama cikin gida, kowa ya tafi wurin saanninsa yadda suka saba in sun zo gidan. Yaa Maira ta ce da mahaifiyar ta cikin sanyin murya.
Sai muka ji abin alheri Yaa Gumsu, da ma zaman Yarima da mace daya ai ba yi ba ne, Yarima fa, Yariman Askira Mai jiran gado! Balle wadda ba ta fito daga jinsinmu ba balle addinin mu.
Na yi farin ciki kwarai da gaske don dama ni auren nan na farko na Yarima bai kwanta min ba ko kadan, babu wani biki na alaadunmu da muka yi sabida abin kunya ne ma mu fito mu fadi ga wadda ya aura a cikin masarautun da ke zagaye da mu.
Sai kuma ku yo gayya a auren shegiya mara asali? Tukunna ma kin san da wa ya daura masa auren da kike wannan giringidishin?
Subhanallah, Yaa Gumsu tofar da miyan bakinki tun kafin malaiku su rubuta. Saadatu ba shegiya ba ce, diyar Bilkisu ce ta cikinta
Tayi aure ta haife ta da mijin ta na fari kafin ta auri Askirama..!.
A razane Yaa Gumsu ta dago ta dubi diyar ta Yaa Maira. Sai Yaa Maira ta yi amfani da wannan damar data samu wajen luguiguita zuciyar ta.
Tiryan-tiryan ta soma bai wa Ya Gumsu labarin Bilkisu da yadda ta haifi Saade, sak yadda mahaifin su ya bata labari, ta kare da labarta mata Bilkisu ta boye musu Saade yarta ce sabida ba ta son gori musamman daga ita Yaa Gumsu in ta ji cewa ba a budurwa Mai Askira ya aure ta ba ta kade har ganyen ta da gori. Karshen maganar da Ya Maira ta fada shi ya kara sanyayar da jikin Ya Gumsu.
Dangin mahaifinta na hanya, wan mahaifinta uwa daya uba daya Alhaji Kyari Babagana, na tabbata kin san wannan sunan, don kuwa shi ne yake bai wa Bulama fatun da yake kai wa kasar Italiya. (Bulama kani ne ga ya Gumsu, wanda suke sanaa daya da Alhaji Kyari). Ita ma Ya Maira Askirama ne ya gaya mata hakan. A binciken da yasa aka yi masa akan asalin mahaifin Saade.
Ya Gumsu da ke ba ta son nuna karayarta, sai ta hau mitar rashin dalili.
Chapter 2 · 0% Book details