← Book details Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 19

Sashe 7

Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Fanna ta fita da kamar minti biyu, angon na Saadatu ya bayyana gabadayan sa cikin falon. Yana takun sa na kasaita tamkar mai tafiya akan gajimare. Shalelen Askirama da Ya Gumsu. Kanin Ya Maira da Mairam Murjanatu. Mijin Aisha Sultana. A yanzu kuma angon Saadatu saar mata. Wato [Dr]Yareema Sageer Yusuf Askira. Kamar dama yana falon dake bin wannan tun dazu yana jira.
A yau sanye yake cikin royal attire dinsa, shudiyar alkyabba da jamfa na wani rantsattsen yadin filtex, hular kan sa Dara ce baka gashin jikinta na reto daga gefen damana fuskar sa ba karamin kyau tayi masa ba.
Tunda Saadatu ta ke a tsayin rayuwar ta ba ta taba ganin mutum maabocin cikar zati, ilhama da kwarjinin Yareema Sageer da ke tsaye nan a gabanta a yau ba. Gabadaya ya canza mata, daga wayayyen dan bokon nan da ta sani mai tsukewa cikin suit da necktayil zuwa hakikanin BASARAKE na gasken-gaske, sarautar ma ta Askira wadda duk yankin Borno babu kamarta.
Ji ta yi kamar ta narke a wurin lokacin da Yareema ya tako ya tsaya a gabanta, kamshinsa na Invictus (Paco Rabbanne) da ke hargitsa ta ya mamayi hancinta. Ta sunkuyar da kai ta kasa ko kwakkwaran motsi.Dr. Sageer ya yi taku daya, biyu, ya tsaya a gaban Saadatu, kwalliyar da aka yi mata bai taba ganin ta da ita ba haka kalar kayan jikin ta ya matukar karbar lafiyayyar fatar jikin ta, ya kara fiddo zahirin kyawun ta da kwarjinin ta na Shuwa Arab, duk wani fushi da ya zo da shi da niyyar sauke mata a kan rashin kunna waya tunda aka daura aure, sai ya ji yana melting yana bin rariya, yayin da wata matsiyaciyar soyayya ke maye gurbin sa.
Ya zuba hannuwansa duka a cikin aljihun sa, lumsassun idanun sa a kan ta, murya a sanyaye kamar ba Uncle Yareeman da ta sani ba, ya ce,
Saadatu laifin me na yi miki ki ka ki kunna wayarki? Atleast mu gaisa ko? Rabo na da ke tun zuwan mu garin nan. Kin san yadda na azabtu a kan hakan? This is sheer punishment! Ba don Yaa Maira ba kenan har mu koma Abuja ba zan ganki ko na ji muryarki ba Saadatu, me yasa? Do you know how difficult and tortured is this to me?
Maimakon ta ba shi amsa sai hawaye suka zubo. Ganewa da ta yi cewa Yarima Sageer bai cikin irin bacin ran da damuwar da ita take ciki akan auren bazatan da aka yi musu. Karewa ma ya karbi alamarin da hannu bibbiyu. Har yana fadin rashin ganin ta tun zuwan su gidan ya azabtar da shi. To dama can yana jiran hakan ne ko yaya ne? Ko dama akwai wani abu makamancin so a ran sa da bai taba nuna mata ba sabida girman kan sa? Aka dauke ta a bagas aka bashi don shi dan gatan Askira ne?
Hawayen da suka sa Yarima saurin durkusawa a gaban Saadatu ba tare da ya san lokacin da ya yi hakan ba. Ya dora tafin hannun sa akan kafar ta. Zuciyar sa cike da fargabar kada dai Saadatu bata farin-ciki da kasancewa cikin iyalin sa? Kada dai hawayen ta na nufin..bata yi naam da zamantowa matar sa wani bangare na rayuwar sa ba? Idan hakan ne a ran ta shi yaya zai yi da rayuwar sa yanzu? Ya riga ya afka a rijiyar da zurfin ta ya fi na gaba dubu. Babu mai iya fito da shi sai Saadatu.
Already Saadatu ta dade da mamaye shi, ta mamaye kowanne gurbi da kowanne sako na zuciyar sa ba tareda ya san lokacin da hakan ya fara ba…
Ya wayi gari ne ya gan shi dumu dumu a soyayyar Saade. A wannan lokacin hes helpless idan Saade ta ce bata auren sa yaya zai yi? Bai iya sakin ta! Baa saki a gidan su, ko ana yi bai taba sakin Saadatu. Ba kuma ya so ya nuna mata weakness din sa.
Ya daga hannu zai rike natafor the first time a tarihin rayuwar su don ya korewa kan sa shakkun kasancewar ta mallakin sa a yanzu, ta yi saurin ja da baya cikin matukar razana! As if lantarki ya jona mata. Tare da maida hannayen ta duka baya ta sarke su a bayan ta. Yareema Sageer Ya daga lumsassun idanunshi yana kallon Saade, a galabaice, a susuce cikin wani yanayi na damuwa da rashin sanin abin cewa.
A lokacin ne Saade ta soma shesshekar kuka a hankali, kukan da ya ratsa har cikin kwanya, ruhi da zuciyar Yareema ya hargitsa shi, ya sake kai hannu zai rike ta, ta yi maza ta sake ja da baya.

Kada ka kuskura ka taba ni, ni ba zan auri mai yin ZINA ba, Allah ya tsare ni, kuma ba zan kuma bin ka Abuja ba!.
Chapter 7 · 0% Book details