← Book details Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 19

Sashe 6

Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sai Askirama-Mai Askira cikin dimbin alfarmominsa da karamcinsa da ba su taba karewa a gare shi ya sunkuya ya hutar da shi, ya dauko takalmin nan ya miko masa har inda yake.
Me zai ce da Mai Askira? Me zai ce da Fulani Bilkisu banda Allah ya ja kwanan su? Sun yi masa gatan da ya kasa yiwa kansa. Ba zai gushe yana rokon Allah Ya kara soyayya a tsakaninsu, ya ba shi soyayyar Saadatu kwatankwacin ta mahaifiyar ta Fulani ga Askirama!
Da ya gaji da trying wayar Saadatu ta ki kunnawa sai ya kira Yaa Maira. Ya san Yaa Maira ce kadai zata yi masa wannan taimakon, sabida yadda take son sa da tausayin sa, in ba haka ba shi da ganin Saadatu sai an gama biki.
Yaa Maira na dagawa ta ce,
Angon Saadatu ka sha kamshi.
Murmushi Yarima ya yi, cikin jin wani irin karin nutsuwa a zuciyar sa da ruhin sa wanda bai taba ji a baya ba, da wannan daddadan suna da inkiya da Yaa Maira ta kira shi da shi, ya ce,
ni bana kamshi Yaa Maira tunda amaryar ba ta son ganina ko kadan balle ta san min kamshin, ko murya ta bata son ji Yaa Maira. Ko kai na ya fara furfura ne ban sani ba? Kin san yammata basa son mai furfura, rabo na da ita tun ranar da muka zo, ko waya ta ki kunnawa don kar in kira ta in ji muryar ta in samu nutsuwa.
Dariya Yaa Maira ta yi, in wani ne yace Yarima ne wannan zata musa, Yariman da magana a gare shi sai dole, fitar kalma wannan tsada gareta daga bakin sa, amma yau shine yake joking, lallai Saadatu ta ciri tuta kaman uwarta, wane irin sirri gare su haka? Da suke juya zukatan sarakuna? Bata tantama in nan gaba kadan Saade bata juye kan Yarima ba kamar yadda mahaifiyarta ta juye na Askirama. Ita dai in auren Saa zai raba Yarima da bin mata ba ta da damuwa a kan hakan, ta tabbata dama ranar da ya auri matar da yakewa hakikanin so zai bari, musamman idan halittar su ta zo daya, tunda Mai Askira ya hakura da kwarkwarori tun zuwan Baggara Bilkisu,ta ce,
Amma Saadatu ba ta kyauta ba, an gaya mata miji wasa ne? Bari in je in samu Fulani zuwa anjima a shirya muku ganawa ta musamman, don in anka shiga hidimar bikin nan ba za ku samu ko ganin juna ba.
Tana kashe wayar ta nufi unguwar Fulani Bilkisu.
A falon ta tadda ta tare da mutane, nan ta nemi kebewa da Fulani, suka dan yi magana kuskus, Fulani ta kama baki cikin mamaki.
Ashe Saade ba ta kunna wayar ba? Na rasa me ke damun yarinyar nan???
Yaa Maira ta ce, Ki bi ta a hankali dai, Saadatu na bukatar lallashi har zuciyarta ta samu nutsuwa da auren, kada ki manta baku nemi shawarar ta ko amincewar ta ba, don haka lallashi ne naku ba tursasawa ba, shi ma Yarima gajen hakuri ne irin nasa, ina ce tare za su koma Abujan?
Fulani ba ta saurari Yaa Maira ba ta nufi dakin Saade cikin fushi.
Ita da Hanne ta same su tana ware sitturunta masu kyau kala-kala daga wardrove tana bai wa Hanne. Suna yi suna hira. Gabadaya ta manta da damuwar da take ciki sabida zuwan Hanne.
Ashe ba ki kunna wayarki ba Saa?
Fulani ta fada daga bakin kofa. Tana kokarin hadiyefushin ta.
Saade ta turo baki gaba irin na shagwababbun yaya, Babu caji ne, amma yanzu zan saka daman.
Ya yi kyau!.
In ji Fulani, sannan ta juya ta bar dakin cikin fushi.
Dakinta ta koma ta dauko wani dandatsetsen leshi cotton mara nauyi kalar maroon da ratsin golden, an yi masa dinkin riga da zani fitted, ta saka Fanna ta saka shi a kabbasa ya turaru tukun ta feshe su da turarukanta na musamman, ta kuma zabo mayafin da ya dace da su kalar golden sannan ta dawo dakin Saade, Hanne ta mika wa kayan,
Taimaka mata ta shirya Hanne, tana da baki daga Abuja.
Tana gama fadin haka ta juya. Mamaki ya kama Saade, ita yaushe ta yi kawa a Abuja? Kawarta daya Saidu ne, kuma Fulani ba za ta ce ta yi kwalliya saboda shi ba, watakila ya gaji da nemanta a waya ne ya taho har Askira, amma ta ya ya Fulani za ta ce ta yi masa kwalliya irin wannan?
Sai ta mikawa Hanne kayan.
Bar kayan nan Hanne, Fulani ba ta san wanene ne ya zo ba.
Hanne ta ce, Tunda dai ta ce ki saka, to ki saka kawai, baki ganin kin bata mata rai ne?.
Ta mika mata zanin, daya bayan daya ta sanya, sai ga Fanna ta shigo tare da wata mata, wadda Saade ta san ta mai kwalliyar Fulani ce during occassions, ta ce, Fulani ce ta turo ta ta yi mata kwalliya.
Haka matar nan ta zaunar da ita kan stool ta yi mata wani irin light serene make up, karo na farko da cute fuskar Saade ta ga sassanyan fentin bature, tana kunci tana komai matar bata biye mata ba tunda bisa umarnin Fulani take, a ganin ta ma fushin da Saade ke yi ya kara ma fuskar ta annuri, classique and gentle amaryar Yareema, [inji mai kwalliya cikin ran ta], bada jimawa ba tuni Saade ta fito a beautiful Princess dinta.
Matar wadda babarbariya ce ta feshe ta da tsadaddun turarukan humra, sannan Fanna ta kamo hannunta suka fito, Saade ta kasa magana bin Fanna kawai ta ke, Fanna ba ta tsaya da ita a koina ba sai falon saukar bakin Fulani na musamman.
Falon shimfide yake da kilisai na alfarma da tumtum a koina, da hoton Mai Askira cikin nadi da amawali windowsize a gabas maso kudu na dakin, sannan zagaye da golden din kujeru na zamani. Har bisa royal chairs na falon ta kaita ta zaunar da ita, ta gyara mata lullubi, sannan ta juya tana fadin,
A fito lafiya uwargijiya ta, takawar ki lafiya Gimbiya Saadatu.
Chapter 6 · 0% Book details