← Book details Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 19

Sashe 5

Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abin da Saade ta fara tambayar Hanne kenan. Hanne ta idasa rushewa da kuka, ta ce,
Baba ya jima da rasuwa Saade. Baba ya dade a kushewar sa. Mu kuma ba mu san garin da ki ke ba da tuni mun zo, shekara da shekaru muna kewarki.
An yi min aure shekaru hudu baya da saurayinki Naziru, tunda na samu ciki ya gudu birni ya bar ni yau shekaru hudu ba mu kara jin labarinsa ba, kin ga dan da na haifa masa nan, Inna ta sa masa sunansa Naziru.
Jiya kawai muna alwala a gindin rijiya sai ga sako daga gidan Maigari wai mu zo an zo daukarmu za a kawo mu inda ki ke. Inna Laure ta ce ba zaa zo da mu ba, ita kadai zaa dauko, sai da direban ya ce an ce masa iyalin Baba Saleh da Inna Laure, sannan ta yarda aka taho da mu.
Saade ta rungume dan Hanne a jikinta tana tuno Naziru don kamar su daya, ta ce, Yanzu ina Innarmu da Inna Lauren?
Aka bude kofar dakin aka shigo, Fulani ce, sai tsofaffin guda biyu biye da ita. Duk sun tsufa sun yamutse a idon Saade. Tana kuka ta ke rungumarsu daya bayan daya, ta ce,
Inna, ku yafe min. Na dade ban neme ku ba, ajizanci ya tabbata gare ni, wallahi karatu ne ya sha kaina sam bana samun hutu.
Inna Laure da Innar Hanne suka rike ta suka zaunar a tsakiyarsu suna fadin, Babu komai Saade kin ji? Allah ne ya nufa sai yanzu za mu sake haduwa, komai kana da niyya sai Allah ya nufa.
Innar Hanne ta ce, Shi ma Babanku yana ta wakar zai dawo ya sake duba lafiyarki, sai cuta ta sarke shi, bai jima yana jinya ba mutuwa ta raba mu. Mu kuma ba mu san garin ba, mun dai san masarauta ce a Borno. Sai yau da ki ka sa aka tura har Tsanyawa aka dauko mu cikin mutunci a mota.
Ashe Saade aure ya zo? To Allah ya sa an yi ke nan, Ya ba ku zaman lafiya.
Saade kamar jira take sai ta rushe da kuka, ta ce, Innar Hanne ku roki Fulani, don Allah ta bai wa Maimartaba hakuri, bana son auren.
Inna Laure ta ce, Kul Saade! Aure sunnar Annabi ne, wanda ba ya son sunnar Manzon sallallahu alaihi wasallam hakika Manzon rahma ya ce ba ya tare da shi. Ni dai rokonki zan yi ki yafe mini, na ga babbar ishara a kanki, duk abin da na yi miki kin manta ki ka ce a je a dauko miki ni har Tsanyawa. Ta saka kuka sosai.
Saade ta ce, Inna Laure, ni ba ki yi mini komai ba sai alheri, rike ni da ki ka yi tun ina karama shi ne babban alherinki gare ni, don haka ni komai ya wuce a wurina.
Daga nan hirar ta koma kan yadda auren Hanne da Naziru ya kasance, Innar Hanne ta ba ta labarin Naziru ya sha kuka bayan tafiyarta Askira, A karshe da ya tabbatar ba za ki dawo ba ya like wa Hanne, Baba Saleh ya cire ta daga makaranta ya ba shi aurenta cikin mutunci. Amma tunda Hanne ta samu ciki aka neme shi aka rasa a Tsanyawa sanadin kamuwar Babanku da hawan jini ke nan.
Hanne ta haihu a gida, ba ta jima da haihuwa ba Babanku ya cika, ni na yi ta dawainiya da su da sanaoin hannu iri-iri har kawo yau.
Fulani ta ce, tunda ya shekara hudu bai dawo ba kuna da damar kai kara kotun muslunchi a ba ta yancinta, ko ta samu ta yi wani auren. Shi kuma in da gangan ya gudu ya barta Allah zai saka mata, in kuma wani uzurin ne ya rike shi, Allah ya sada su da alkhairi. Zan yi magana da Maimartaba ya shige muku gaba Hanne ta samu yancinta.
Hanne ta ce, Burina kenan, ban san ina da wannan damar ba da tuni na yi amfani da ita. Ina matukar son in koma makaranta in raini Naziru shi ma in sa shi makaranta.
Fulani ta ce, Kada ki damu Hannatu, insha Allahu komai zai yi daidai bari mu kare bikin Saade.
Sai da suka raba dare suna hirar yaushe gamo, a dakin Saade duk suka sauka don saboda zuwansu ta manta da damuwar ta, ta cire wa ranta kunci, ta ware suna ta hira da Hannenta.
Washegari Fulani ta raka su suka yi gaisuwa wajen Askirama, ya ji mutuwar Baba Saleh sosai, Fulani kuma ta gaya masa maganar Hanne, Askirama ya ce zai shiga maganar bayan biki insha Allahu.
Tun zuwansu Hanne, Saade ta samu walwala, amma ta ki kunna wayarta. Tabbas da ta ga sakonnin Yarima Sageer har guda uku. Sako na farko ga abinda Yarima Sageer yace.
“Thank you for being the PRINCESS Im waiting for.Thank you for coming to my life when my heart is desperate to have you..(Madallah da zamowar ki GIMBIYAR dana ke jira tuntuni, madallah da zuwan ki cikin rayuwa ta a lokacin da zuciyata ta dimauce ga son mallakar ki).
- Sageer.

Na biyu kuma yace.

“Saadatu save a soul by picking my call(Saadatu ki cece ni ki daga kira na).
- Sageer.

Sakon Yarima na karshe ga Saade cikin harshen hausa ne, ga abinda Yareema ya rubuta ma Saade.

Kin ki bude waya saboda ni ko Saadahtouh? Bonono kenan rufe kofa da barawo. Bari in tuna miki wani abu guda daya da baki sani ba ko kika manta; daga rana irin ta yau mun zama abu guda,tare zamu kare rayuwar bakidayan ta,daga nan har gaban abada, ko makwanci bazamu kara rabawa ba sai bisa unvoidable reason..

Duka wannan bidirin da Yarima ke yi shikadai yake yin abinsa Saade bata san yana yi ba don kememe ta ki kunna wayar ta kamar ta san tashin hankalin dake jiran ta cikin ta daga zafafan kalaman sa [ba raba makwanci har karshen rayuwa].
Da ga karshe Yarima ya kasa hakuri, Saade ta kure dukkan hakurin sa, idan ba ganin ta yayi ba ba zai samu nutsuwar fuskantar bikin nan dake gaban su ba, ba zai koma nitatstsen Sagirun sa ba, matukar son ganin Saade yake anyhow ko jin muryar ta, don ya ga da fuskar da ta karbe shi matsayin miji ne ko akasin sa? Ko har yanzu kallon Uncle take masa?
Ya aiko a gaya wa Fulani ta yi ma Saadatu magana ta kunna wayar hannunta su yi magana, mai muhimmanci. Da Fulani ta sa Fanna ta gayawa Saade, sai Saade ta ce ma Fanna ta ce da Fulani ta kunna har sun yi maganar, bayan kuma ko taba wayar daga inda ta yi mata kyakkawar maboya ba ta yi ba.
To me Uncle Yarima zai ce mata? Na ji auren da aka yi mana bagatatan ni ma bana so ko me? Ko ki kama kanki ni ina da mata ta da nake matukar so? Ba ta bukatar wata sabuwar muamala a tsakanin su bayan official one irin wadda ke tsakanin su a baya, cuta ce an gama yi mata tunda an hada ta da shi, don haka ta yi kememe ta yi kemadagas ta ki kunna waya. Kulawa ma yabawa ce inji 'yan magana.
Ya gaji da trying wayar Saade a daren yau, ana cewa a kashe, sosai yake son ya gan ta don ya ga da fuskar da ta karbi wannan babban alkhairin da ya same su. Yes shi a wajen sa alkhairi ne, GIANT (katoton) alkhairi ma kuwa, da bashi da yadda zai iya bayyana farin cikin sa da muhimmancin sa gare shi!
An bashi abinda ya dade yana so yana kwadayi batare da ya cancanta ba, ba kuma tare da ya furta ba kuma ba tare da ya sha wahala ba sannan cikin girma da daukaka. A ganin sa hes not worth enough (bashi da darajar da zai mallaki Sa'ade) innocent soul kaman Saade, in yayi laakari ga tarin nakasun sa da laifuffukan sa na baya. Ya dade yana sunsunar takalmin, bai san ta yadda zai yi ya dauka ba. Sabida ganin cewa Sa'ade tafi karfin sa.
Chapter 5 · 0% Book details