← Book details Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 19

Sashe 15

Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Me ya sa ki ke guduna ne Saadatu?

Ta sadda kanta kasa.
Ya ce, Ki kwantar da hankalinki kin ji, za mu zauna mu yi magana ta fahimta kafin mu tafi Abuja, yanzu nan da awa guda za ki ga gidan nan ya cika, don haka ki yi hakuri ki ba ni one hour in yi ta tare da ke, kada ki bar ni ni kadai.
Murya can kasa kamar an shake ta ta ce,
Zan dawo, abu zan dauko.
Gaya min ko mene ne in dauko miki, amma ba za ki bar dakin nan ba sai na miki umarni.
Kamar ta fashe da kuka, ta ce, Ba ka san inda yake ba, besides abin na mata ne.
Yarima ya ce,
Okey. I can relate. To mu je tare, kada ki yi min wayo ki shige daki ki rufe.
Ta turo baki, ta ce,
Na yarda. Sannan ya bude kofar suka sauka zuwa downstairs.

Bayin da aka ba su suna ta hidimar tsaftace gidan suka wuce su bayan sun gurfana sun yi gaisuwa, yana kallo ta bude lokar ta dauko ledar sanitary pad ya sa ta a gaba suka koma upstairs dinsa.
Suna shiga dakin ta wuce toilet, kafin ta fito Yarima ya zuba mata shayin da ya sha yana firfita mata between two cups. Ta fito tana taku a hankali kamar mara gaskiya ta zauna a kan sofa bed can nesa da shi ta zuba uban tagumi da hannaye bibbiyu.
Yareema ya taso zuwa inda ta ke, ya rusuna ya mika mata shayin, sannan ya zauna daidai kafafunta, kai ka ce ita ce Yariman ba shi ba. Ta sa hannu ta karbi shayin don ba ta yi wa yunwa fulako.
Ganin yadda ta ke shan shayin da sauri duk da zafinsa ya sa shi tambayarta.
Tun yaushe rabonki da abinci?
Saade ba ta ce komai ba, sai shan shayinta ta ke yi, kan ka ce me ye wannan ta zuke shi. Da gaskiyar sa bata taba shan shayi mai dadin nasa ba da wartsake makoshi. Ya mike zuwa ga bed side fridge dinsa, ya dauko danyar madarar oldenburger mara sanyi, ya zo ya bude ya tsiyaya mata a tambulan ya zauna dab da ita ya kai kofin bakinta.
Da farko kunya ta ji, amma kuma an ce mata suna son kulawa irin wannan daga mazajensu, kulawar da ba duk maza ke iyawa ba sabida girman kan su. Sai ta ji ta kasa tankwabe wannan kulawartasa, ta bude baki tana shan madarar sosai daga hannun Yareema, sai da ta shanye madarar tas, zai kara mata ta ce a hankali,
Ya isa.
Sai ya ajiye kofin ya juya ya kwantar da kai a cinyoyinta. Hannayensa zagaye da kugun ta.
Now, tell me Saadatu, why dont you love Sageer?
Ta rasa inda za ta sa kanta, sabida Uncle Sageer ya yi kwanciyarsa akan cinyoyinta, ya mike kafafunsa bisa sofa din.
Uncle Ta fada a hankali very upset and unease. So take ta ce ya daga ta kada wani ya shigo, amma kunya ta hana ta.
Kada ki kara ce min Uncle, ban san ta ina na zama Uncle dinki ba. Ni ba kanin Fulani ba, ni ba kanin Baban ki ba...
Ni, (ya nuna kan sa) ni ne SAGEER kawai, Sageer Askira, ba ni da wani lakabi bayan wannan.
Ya sa tafukan hannunsa a fuskarta.
Very smooth and supple. In ji dai ba shafe-shafen zamani ki ke ba? I love natural skin shi ya sa nake son Sultana.
Ai ba ta san lokacin da ta ture kansa daga cinyarta ba ta mike. Allah ya so ta bai cire mukullin daga jiki ba, ta bude kofar ta yi ficewarta.
An ce ko babu SOYAYYA kishin cikin AURE daban yake. Haka ta wuni ranta a bacea kan yar maganar da Dr. Sageer ya fada akan Sultana, yayin da Dr. Sageer ya wuni cikin matsanancin nishadi da bai taba tsintar kansa a ciki ba.
A yadda ya fahimta insha Allahu ba zai sha wahalar samun soyayyar Saadatu ba, tunda har ta fara kishin matarsa. Dama ya fada ne don ya ga reaction din ta.
Ya canza kayan jikinsa zuwa Jabba da hular data dace da kalar kayan wato deep-brown, ya fesa turarensa ya fito. Tuni bayi sun cika tebir da abinci naui-naui. wanda aka kawo daga unguwar Fulani Bilkisu.
A cikin bayin da Maimartaba ya ba su akwai wata kuyanga Sadiya, burinta kawai Yarima ya yi kwarkwara da ita ba tun yau ba, don haka ba karamin dadi ta ji ba da aka hado da ita cikin hadiman gidansa.
Yanzun ma yana fitowa ta fadi gabansa,
Gyara kimtsi da kyau, lafiya dan zakin Duniya lafiya dan malafar duniya, lafiya dan mai fada da cikawa lafiya dan mashasha lafiyarka dama da hauni mai nasara zauna daidai dan bawan Allah zauna daidai dan masu alheri.
Yana zama bisa dining table ba tare da ya dago ido ya dube ta ba, ta hau yi masa firfita da maficin gashin Dawisu tana ci gaba da zubo kirarin. Daidai lokacin da Saade ta bude kofar dakin ta fito cikin wata irin sassaukar kwalliya ta riga da zane dark blue na yadin karen miski wanda ba a samunshi koina sai gidan sarauta.
Wani kallo da ta sakar wa Sadiya ya sa ba shiri ta juya tana mata nata kirarin.
An fito lafiya uwar masu gida, zauna daidai uwar alheri taka lafiya matar Zakin duniya.
Saade ta kira sunanta a hankali kafin ta wuce ta ce,
Sadiya!
Kada ku kara zuwa nan in ba ni na kira ku ba. Lokacin aikinku daga karfe shidda ne zuwa bakwai na safe, da kun gama jera abincin karin kumallo shi ke nan na sallame ku.
Sadiya ta amsa a matukar ladabce, sannan ta fice.
A ranta tana fadin, Ta Allah ba taki ba. Insha Allahu ni ce Sa-dakarsa ta farko duk boyon da za ki yi masa, me ya kai ki auren Basarake in kin san kishi gare ki?
Yarima yana jinsu kansa a duke yana danna wayarsa, sai ya ji murmushi ya kwace masa. Ya dauka zuba masa abincin ta fito ta yi, amma tunda ta kori Sadiya sai ta juya ta koma daki abinta ta barshi a nan zaune.
Sai ya ji ya kasa ci. Ya zuba abincin daidai misali a kan plate, ya dauka ya bi bayanta.
Ta zauna kenan a bakin gado ta yi tagumi, wadannan yammata da aka cika mata gida da su kullum suna sintiri a gaban Yareema yaya zata yi da su? Ta isa ta ce zata zauna babu kuyanga? Ko cewa zata yi a kwashe su a kawo mata tsoffi? Kowa ya ji hakan a take zai fassara ta da kishi. Ita kuma ta san ba kishi take ba tsoro ta ke ji, tunda ta san wa aka aura mata. Tana wannan sake-saken sai gani ta yi tattausan hannun Yarima mai daure da agogon ‘Swatch Blustery’ ya miko mata plate cike da soyayyen dankali da sauce din koda da hanta.
Saade ta dago ido a hankali ta dube shi. Ya daga mata gira, ya ce,
Karbi.
Sai ta kasa tankwabe wannan kulawar a karo na biyu. Ta sa hannu ta karba cike da jin nauyi, ita ba ta ba shi ba shi ya dauko da kansa ya kawo mata, ta tuna wane ne Yareema Sageer a masarautar Askira gabadaya da yadda kannensa da yayyensa duka ke sonshi da girmama shi. In ta ce ba ta ji wani iri a ranta ba kan rashin kyautawar ta ta yi karya, sai ta ji somehowkamar abin da ta ke yi ba daidai ba ne. Don haka ta motsa dan bakinta a hankali yana shirin ficewa daga dakin tace.
Uncle kai ba za ka ci ba?
Ya juyo gabadaya ya fuskance ta sabida ya tsani wannan Uncle din da ta ke ce masa.
Ya ce, This will be the last time da za ki sake kirana Uncle tunda dai ni ba kanin Fulani ba ne, idan ba za ki fadi sunana ba ki sa ma min wani. Amma ki ka sake ce min Uncle Allah zan cire hijabin da ke tsakaninmu Saadatu, wanda ke sa ki yi min kallon kanin Babanki.
Maganar ta bata dariya amma bata yi ba.
Ya juya ya fice yana cewa, Mun tafi Ta-Sani ni da Awaisu.
Murmushi ya subuce wa Saade, kowanne irin hijabi ne tsakanin nasu? Oho! Ta maida hankali ga cin abincinta, kunnenta har motsi yake sabida yunwa da dadin abincin wanda daga jin kamshin sa ta san daga unguwar Fulani Bilkisu yake.
Chapter 15 · 0% Book details