← Book details Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 19

Sashe 11

Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

SAADE A GIDAN YAREEMAN ASKIRA
Daga ita sai Hanne da Raheema a bedroom din da aka zaba aka shigar da ita, wanda shi yafi kowanne kayatuwa, sai kuyangi da bayin Fulani da ke ta kintsa duk inda aka bata. Fadin dukiyar da Askirama ya dankara a gidan Yareema Sageer bata baki ne, ki sa a ranki gidan Yariman Askira mai jiran gado, shi ke nan zance ya kare.
Gida ne ginin sarauta (royal mansion) wanda aka yiwa zubi na zamani,turawa suka zana shi suka kuma zo suka gina daga Amsterdam, da aka yi wa sassan matan aure har hudu, komai da ke cikin wannan sashe shi ne a wancan sai bambancin kalar fenti. A sashen kowacce mace manyan faluka ne bi-da-bi har guda Uku da dakunan barci Uku. Babun ce kawai babu a gidan Yarima Sageer Yusuf Askira.
Sassan Aisha Sultana shi ne na farko, sai na Saade sannan wasu guda biyu a rufe. An ware bangaren bayi da hadimai daga can karshen gidan.
Sassan Yarima kuma yana upstairs wanda girmansa ya yi a hada sassan matan nasa guda biyu. Komai da ke cikin sassan Yarima ya zo da shi ne daga Amsterdam kuma duk bayan shekaru biyu ake fidda komai na gidan a sake, a yo odar wasu. A raba wa talakawan gari, ko bayi da hadimai.

A can gidan Wazirin gari Ibrahim a dakin Awaisu Yarima Sageer ne tsaye jikin mudubin dogon yaro yana sanya links din hannun farar shadda kal da ya saka, sai tashin kamshin invictus dakin Awaisu ke yi. Awaisu ya kasa danne dariyarsa ganin irin kwalliyar da Yareema ke yi wadda ko ranar da zai raka shi dakin Aisha-Sultana bai yi irinta ba, ya karkata hula ya sake karkatawa yafi sau biyar, ya ga bata yi kyau ba ya cire ya sake canza wata, [to wancan aure ne da aka riga aka kwashe albarkarsa tun a waje]. A ransa Awaisu godiya yake wa Allah yana kuma adduar Allah ya sa auren nan ya zamo karshen duk wasu matsaloli na dan uwansa Sageer.

Amma dai sai gobe za mu je sayen baki ko? Ka ga yanzu dare ya yi sosai, na san duk sun yi barci bai kamata mu tada amarya ba tana barcin gajiyar biki irin wannan.
Inji Awaisu cikin seriousness.
Wata harara da Yarima ya juyo ya zuba masa sai da ta sa Awaisu durkushewa a inda yake yana dariya. Kafin ya dago daga dariyarsa Yarima ya gama saka takalmansa ya fice yana fadin.
In ka ga dama kada ka je, da ma ba ni na gayyace ka ba, aure dai ka sani ba yau na fara ba balle ka ce rawar kafa na ke yi.
Awaisu bai bar dariya ba da ma gwanin ta ne, ya saka takalmansa ya bi bayan Yareema Sageer yana cewa,
Ko don in bata maka lokaci kafin ka shiga dakin Sa'adatu dole in bi ka.
Yarima ya girgiza kai jin abinda Awaisu ya ce, ya ce, Awaisu! Mind your language. Saadatu is my step-sister rainon ta na yi wa uwarta alkawarin zan yi, kuma shi zan yi din. Zan ba ka mamaki, jibi-jibin nan zan koma wurin mata ta.
Awaisu don dariya har da hawaye, ya ce, Aah Yarima, kada wata tara ta cika kuma mu zo bikin radin suna, wannan rainon in dai kai za ka yi shi Saadatu ba za ta taba girma ba.
Suna ta barkwancinsu na aminai har suka karaso gidan sarki, don Yareema ya ce sai ya je ya yi wa Ya Gumsu sai da safe, ya kuma nemi albarka kafin ya karasa wajen Saadatu.
[Da ya san abinda zai tarar, da ya yi wucewar sa kai tsaye dakin amaryar sa, in ya so da safe ya zo tasani].
Dazu da yamma Yaa Maira ta kira shi cikin sirri sun yi magana, inda ta ce ya bi Ya Gumsu a hankali da duk abin da ta ke so, don ba karamin yaki ta yi da ita kafin ta amince a yi bikinnan cikin dadin rai ba.

Yarima ya yi sallama a hamshakiyar turakar mahaifiyarsa Ya Gumsu, Awaisu bai biyo shi ba ya zauna a mota don ya ba shi dama ya gana da Ya Gumsu. Tana hakimce bisa kujerar mulkinta sai karkada kafa take yi cikin izza lokacin da Yarima ya yi sallama. Ta hadiye wani malolon abu da ya tokare ta a makoshi ganin irin kwalliyar da ya caba da bata taba ganin sa cikin irin ta ba, wanda ke nuna yana farin ciki da auren diyar Fulani Bilkisu.
Har kasan kafafunta ya isa ya gurfana yadda suke gaida iyayensu, ya yi gaisuwa ta amsa cikin dacin rai. Daga nan duk suka yi shiru. Yarima ya kasa ce mata ya zo neman albarkarta ne zai shiga dakin amaryarsa, aka ce wargi ma wuri shika samu. Ita kuma tana ta kitsa abubuwan da ta shirya fada masa ba tare da tunanin me zai je ya zo ba.
Ya Gumsu ta dubi dan ta Dr. Sageer wanda kansa ke sunkuye a gabanta. Ji yake kamar ya yi fiffike ya fice ya tadda Saadatu. Shi kansa ya rasa ko wane irin excitement yake ciki mai neman karar da numfashinsa. Zuciyarsa har wani irin bugawa ta ke yi in ya tuna Saadatu zai je ya tadda a matsayin matarsa yau, ba yar amanar da yake riko a gidansa ba kullum yana fama da zuciyarsa a kanta.
Sai jin muryar Ya Gumsu ya yi a tsakiyar kansa.
An yi aure na gani, kuma na sa albarka kamar yadda Yaa Maira ke so. Maimartaba ma yake so, amma Yareema ban yarda ka taba yar Bilkisu ba.
Ina nufin ban yarda ka hada shimfida da ita ba, don kuwa jinina ba zai gogi jinin Bilkisun Askirama ba. Balle in hada zuria da ita. Na ba ka watanni uku ka zo ka kara aure, aure na mutunci na gidan mutunci, duk wadannan matan naka tarkace ne, tunda babu jinin sarauta ko daya a cikinsu.
Na samo maka mata yar Sarkin Bauchi, sunanta Hajjaju, mun gama magana da mahaifiyarta ta ce kana iya zuwa ku fara fahimtar juna, in dai da gaske ni na haife ka Yarima wannan shi ne umarnina.
Ta mike ta shige turakar barcinta ta rufo kofa ta bar Yarima sai tsiyayar zufa yake daga tsugunne, ya rasa inda zai sa kansa. Don kwata-kwata bai fahimci inda zancen Ya Gumsu ya dosa ba, ko kuma ya ce ya fahimta, kwakwalwarsa ce ta kasa fassarawa.
Ya Gumsu na da masaniyar cewa weakness dinsa shi ne Mace. Macen ma ta aurensa wadda zuciya da ruhinsa ya dade yana so da kwadaituwa akan ta, to in ta ce ba zai tabbatar da aurensa da Saade ba, neman matan ta ke so ya koma wanda ya yi wa Maimartaba alkawarin ya daina? Ya yi wa Ubangijinsa alkawarin daga ranar da ya mallaki Saadatu ya daina? Wane irin aure sai ka ce namamajo, aure wata uku ya zo ya kara aure wai Hajjaju? Yo shi ko sunanta Makkah ina zai kai ta duk son matansa?
Guda biyun sun ishe shi sabida shi ba wai mata yake so ya tara ba, in ya samu abunda yake bukata a guda daya zai iya kama kan sa. Abin da ya rasa daga matarsa Aisha-Sultana (sai jar fata da yalolon gashi) wanda ya kai shi ga bin son zuciyarsa da zugar aboki Ziyad maimakon ya nemi karin aure.
Rana daya Mai Askira ya hutar da shi da yake shi uba ne mai tsinkaye, mai son gyara rayuwar yayansa ba ya dagula ta ba irin Ya Gumsu. Shi bai dauki wannan auren da ta ke son yi masa gata ba, sai hanyar huce haushinta a kan auren diyar kishiyarta Fulani Bilkisun Askirama.
Amma ya sani a yadda Ya Gumsu ta ke kan dokin zuciya irin wannan, ba wasu kalaman lallashi da zai yi amfani da su da za su sa ta saurare shi. Mafi aala ya nisance ta har sai ta huce, tunda dama ga alfarmar da ita ma Fulani Bilkisun ta nema daga gare shi, na cewa zai bar Saadatu ta gama makaranta kafin ya dora mata nauyin aure.
Chapter 11 · 0% Book details