← Book details Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 19

Sashe 14

Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Karo na farko da ta yi magana tun shigowarsu dakin. Domin kalamansa sun sanyaya mata zuciya.
Saadahtouh, ke matar aure ce yanzu, kuma macen arziki ba ta raba makwanci da mijinta sai bisa lalura.
Muryar Saade bata fita sosai sabida kukan da ta sha. Ta ce. Don Allah Uncle Yarima ka bar ni in koma wancan dakin, ni ba zan iya kwana daki daya da kai ba. Ta fadi da iyakar gaskiyarta.
Me ki ke tsoro? In kin kwana gado daya da mijin ki Malaiku ne za su yi ta sa miki albarka har garin Allah ya idasa wayewa, musamman if you act as my messeuse (idan kika zama mai min tausa) duk jikina ciwo yake mun saboda zirga-zirga da hayaniya. Please Saadah help me... Ya fada yana kara makalkale ta ta yadda suka dunkule wuri guda kamar curin alkaki, ba tare da Saade ta san yaushe hakan ta faru ba Saboda gabadaya muryar Dr. Sageer ta gama kashe duk wani kuzarinta. Ta saukar mata da wata irin kasala.
Ita ma ba ta san me ta ke tsoro a kwanansu daki guda bisa gado guda babut shes really-really afraid, wani abu ne STRANGE a gare ta, don bata taba ganin inda akai hakan ba. Duk da ta san a yanzu an daura musu aure amma zuciyar ta ta kasa karbar wannan sabon dingimemen sauyin da sauki.
Tana wannan tunanin mai matukar dagula zuciya, ba ta yi aune ba sannan bata tantance komai ba ta ji Uncle Sageer ya soma warware laffayar jikin ta tun daga sama cikin nutsuwa har ya sauketa kasa tsaf, ya saura daga ita sai underwear din dake jikin ta, kallo daya Dr. Sageer ya yiwa Saadatu cikin fararen under wear ya ji komai na duniya ya tsaya masa; including numfashin sa.
Daga hakan ya sunkuce ta ba tareda ya tsaya sake kallon ta ba, bai dire ta a koina ba sai a royal bed din su, ya ja wani lallausar duvet ya lullube su, tare da latsa makunnin lantarki daga nan inda ya ke kwance. Fitilu shudaye suka maye gurbin masu haske (dim light).
A dirowar jikin gadonsa ya bude ya fiddo turarensa Invictus (Paco Rabbanne) ya soma feshe su dukkan su, ya ce.
Bana son wadannan turarukan matan barebarin da aka gumbuda miki, daga yau kada ki sake shafa su, we will be using the same scent, wadannan sun cika karfi da yawa hawa min kai suke yi.
Daga yau za mu dinga using nawa tare (Paco Rabbanne), you can use it too ba shi da karfi.
Saade ta zumburo baki kamar yana ganinta, ai kuwa ya gani ta cikin dan hasken dim din wanda hakan ya sa shi yin abin da bai shirya ba. A hankali ya soma sumbatar Saade tun daga yatsar kafarta
At first hes doing it gentle kafin gabadaya ya koma hungrily, da gani za ka san abu ne da ya dade yana fatan kasancewar sa. Ya dauki Saadatu diyar Fulani Bilkisu ya kai ta wata kololuwar duniyar soyayya da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba.
A yadda Saade ta yi amanna ta mika wuya ko me Yarima ya nema a lokacin tabbas zai samu, domin ba ta san inda Yarima Sageer ya dauke ta ya kai ta ba. Amma sai me? Kalaman Ya Gumsu ne suka fado cikin kwakwalwarsa suka katse duk wani hanzari nasa.
Ban yarda ka taba yar Bilkisu ba, ban yarda ka hada shimfida da ita ba.
Sai kuma na Fulani Bilkisun
Ina neman alfarmar ka daga mata kafa har ta kare makaranta.
Yarima ya rasa inda zai sa kansa a wannan lokacin. Ji ya ke tamkar ransa zai bar gangar jikin sa. A hankali ya mirgina ya koma can karshen gado ya runtse idanunsa yana ambaton sunan Allah.
Saade na jin shi, amma ba ta san dalilin sa na janyewar ba. Da nutsuwa ta soma dawo mata sai ta ji wata matsananciyar kunya ta kama ta. What happened like this? Wannan wane irin abu ne mai tsauri da nauyi yake faruwa tsakaninta da Uncle Yarima haka?
Kanta ta tusa cikin pillow kamar ta roki gadon ya tsage ta shige. Tana jin saukar numfashin Yareema a hankali har daga baya ta gane ya yi barci. Ta yunkura da zummar ta nemi mukulli ta fice, amma sai ta ji caraf! Hannuwan Yarima sun maida ta kwanciyar, ya kuma sake mirginowa ya rungume ta sosai a jikinsa. Bai kuma kara attempting komai ba, tun tana fargabar faruwar wani abu makamancin na dazu har ta gane barcin sa ya yi nisa sosai.
Akai-akai Saade ke sauke ajiyar zuciya tana tambayar kanta, wannan shi ake nufi da auren ke nan? Su dunkule su zama abu guda in every aspect kuma marufar sirrin juna? Sirrin da yafi karfin kwatance ko fadar sa ga wani. As a university student ba za ta ce kwata-kwata ba ta san manufar aure ba duk da babu wanda ya taba zaunar da ita ya gaya mata, duk sakewar da ke tsakaninta da Fulani magana irin wannan ba ta taba hada su ba. Baggara akwai kunya tamkar Fulani suke, sai dai kuma sun fi Fulani ilmin addini.
Sai goshin asubahi ta samu barci, kuma ko na minti daya Yarima bai yarda ya raba ta da jikinsa ba. In ma ta yi kokarin zamewa tsaf cikin barcin zai kara kanainaye ta. Tun tana jin kunya har ta gaji ta yi barcin ta a jikin sa. Ko don wannan turaren nasa mai dadin kamshi da sanyaya zuciya za ta so su wayi gari a haka.
Daren yau bakidayansa wani yanayi ne da ba za ta taba mantawa ba a tarihin rayuwarta. Ba ta maraba da auren Yareema Sageer, ba ta kuma taba mafarkin faruwarsa ba, amma daga daren jiya zuwa yau sai ta ji dama su dauwama a haka! Ba tareda wani dan adam ya kara ratsa tsakanin su ba.
The moment is awesome because its strange but pleasant ga Saade, don haka image din ya tsaya a kwakwalwarta. Hoton ta makalkale cikin jikin Yarima Sagir, ya kasa bacewa dagascreen na zuciyarta. A haka aka yi kiran assalatu.
Da yake ba ta dade da samun barcin ba, ko motsi ba ta yi ba. Har Yarima ya mike ya je toilet din da ke makale da dakin ya kammala abin da zai yi ya fito Saade ba ta da alamar farkawa. Duk da bahagon halin Ya Gumsu, a baya na gaya muku cewa yayanta akwai sallah.
Sai ya tsaya a daidai fuskar Saade yana taje jikakkiyar sumar kanshi. Yarfin ruwan a fuskarta ya sa ta bude ido kadan, sai idonta cikin na Yarima. Da fari ta dauka a dakinta ta ke na Abuja, amma ta san Uncle Yarima bai taba shigar mata daki a irin wannan lokacin ba.
Ta sha ganinshi da pajamas ko a gidanshi, amma ya kan daure tsakiyarta da igiyar jikinta, amma yau bai daure ba, physique chest dinsa dauke yake da suma a kwance luf, wanda hakan ya sa ta saurin kauda kanta. Sai kuma ta tuna wai fa ashe su din yanzu miji da mata ne.
Ajiyar zuciya ta kwace wa Saade daga kwancen da ta ke. Har sai yaushe kwakwalwarta da zuciyarta zasu karbi reality na kasancewar ta matar Yarima Sagir ne?
Yareema ya mika mata hannu da nufin ta kama ya taimaka mata ta tashi, amma sai ta juya daya barin ta rabu da shi.
Ya ce, Tashi Saadahtou mu yi jamin sallah kina makarar da ni.
Saadatu ta yi shiru, ta ya ya za ta iya gaya masa cewa, period ta ke yi?
Ba za ki tashi ba?
Ya fada for the second time yana mamakin abin da zai hana ta yin sallah, sai kuma ya tuna mace ce, don haka ya juya ya tada sallarsa.
Har gari ya soma haske Yarima na sallah, ita kuma ta kasa komawa barci. Tunanin rayuwar da za ta riske ta a gaba ta ke yi. Tunda yanzu rayuwarta ta zama dependent upon Yareema. Sai yadda yayi da ita.
A baya shi din guardian ne, amma a yanzu matsayinsa ya zarta na kowa kenan including iyayenta. Wannan ba karamin nauyi ba ne aka dora mata, wanda ba ta san ya ya za ta yi da shi ba.
Ta duba ta laluba cikin tsokar zuciyarta ko za ta ga SO ko akasin sa a kan Yareema Sageer? Amma sai ba ta samu ko guda dayan su ba, babu soyayya haka babu kiyayya tsakanin ta da Yarima, sannan daga daren jiya zuwa yau alamuran Yareema Sageer masu ban mamaki ne da suka soma rikita hankali da nutsuwarta.
Tana nan kwance har Yareema ya gama sallolinsa, ya sunce ya shiga wanka. Da ya fito ya tambayi Saade,
Manyan kaya zan sa ko kanana?
Ta yi masa shiru.
Ya ce, Alright. Bari kawai in sa kanana, ban sani ba ko saboda tsufana ne ba kya so na.
Ta juya masa baya bata ba shi amsa ba. Ya gama sanya kayansa riga da wandon BALANCIAGA ruwan goro masu ratsin black. Sai ya fito a Georgeous Prince dinsa. Kai bazaka ce ya taba aure ba.
Ya hawo bisa gadon daidai inda ta juya fuskarta yau zaki sha tea irin wanda baki taba shan irin sa ba.
Sai ta rufe idanun ta gabadaya daga barin kallon sa, don ji ta yi zuciyar ta na racing.
A cikin dakinsa akwai karamar butar dafa shayi, ya jona kettle din bayan ya yi hade-haden shayinsa na naa-naa da girfa, yadda Saadatu ta juya masa baya ta ki juyowa yana taba ransa, sabida shi dai ba haka matarshi ta sabar mishi ba. Da sun wayi gari da ta soma haba-haba da shi har sai ya ce ta dame shi.
Ya zuba kakkamsan shayinsa a dan karamin farin kofin shayi na karau, ya zauna a gefen gadon daga daidai kafafunta yana sipping a hankali.
Kamshin shayin da yake sha duk ya cika ta, ya kuma tayar mata da appetite na abinci, sai lokacin ta tuna rabonta da abinci. Tun na safiyar jiya da Hanne ta matsa mata ta ci lomar sinasir guda biyu. Akuyar cikinta har wani irin kugi ta ke yi cikinta na murdawa da yake tana da ulcer kadan tun a El-Kanemi. Dole ta mike ta nufi toilet ta yi brush, ta yi wanka ta kuma nemi pad din da za ta canza ta rasa.
Kayan jikinta ta maida, wato doguwar riga mai bin jiki ta roba wadda ake sa wa a kasan laffaya (underwear), ba ta nada laffayar ba ta fito gashin kanta da ya sha kitson nan jelunan sun kwanta lambam a wuyanta. Kai tsaye ta nufi kofa don ta tuna Raheema ta gaya mata ta sa mata pad din a lokar jikin gadon dakinta da suka kai ta jiya.
Amma me? Kofar a kulle gam, kuma ya zare mukullin jiki.
Ta juya a sanyaye ta dube shi suka hada ido yana kurbar shayi, ya ga damuwa karara a tare da ita. Ya ajiye kofin hannunsa a kan lokar gadon ya taso a hankali ya iso gabanta.
Hannayensa duka biyu ya zuba a cikin aljihun wandonsa, ya dube ta keenly, murya raunane ya ce,
Chapter 14 · 0% Book details