← Book details Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 19

Sashe 1

Masarautar Mu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read


MASARAUTAR MU!.

3

SUMAYYAH ABDULKADIR
[email protected]
[email protected]

SADAUKARWA
Ga 'yar uwar da muka rasa a TAKORITES. Allah ya jikan ki da rahma HASNA'U yasa aljannah ce makomar ki. Ya bamu guzurin tadda ke. Takorites bazamu taba mantawa da ke ba. Da zaman amincin da muka yi tare.Muna son ki Hasna.

JINJINA
Har kullum jinjinar taku ce dukkan members na TAKORI'S ONLINE FORUM whtspp, littafin MASARAUTAR MU jinjina ne a gare ku, nagode da kauna da kwarin gwiwa, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah.

GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba batare da iznina ba, tun daga radio, youtube, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali.

MASARAUTAR MU 3
Cikin raunin murya marar amo da rashin karsashi kamar ta wanda ya sha duka sabida yadda tayi kasa sosai, Yarima Sageer ya duka gaban mahaifin sa Askirama tamkar zai shige cikin sa, ya soma magana cikin sanyin murya da hardewar harshe.
Allah Kawun jo (Allah ya baka yawan rai) amma me ya sa tun lokacin da na dawo daga Amsterdam din, na kuma zo da bukatar auren Sultana baa tambayi raayi na a kan Saadatun ba? Allah ya ja da ran ku da a ce kun bayyana min kudirin ku akan mu tun farko, tun a wancan lokacin, a kan zabin da ku ka yi min, zan hakura ne da nawa zabin duk son da nake masa in karbi zabin ku. Saboda na san duk wani hukunci da za ku yi a kaina alkhairi ne wanda ni duk yawan shekaru na ba zan taba iya hangowa kaina ba!!!.
Sai hawaye suka fito sharr! Daga idanun Yareema Sageer, wadanda a yanzu Askirama ya tabbatar na farin-ciki ne ba na komai ba; hawayen wani irin contentment da Dr. Sageer bai taba ji a rayuwarsa ba.
Sai ya ji rayuwarsa a yau ta cika, ta zama cikakkiya, duk wani gibi dake cikin ta ya cika, amma a baya incomplete yake jin ta somehow shattered. duk da tarin dimbin achievements din da ke cikin ta. kamar akwai wani wawakeken gurbi a can kasan zuciyar sa da a da can, yake jira a cike, gurbin da bai san ko na menene, ko kuma na wanene ba, ya samu aka cike masashi yau unexpectedly. A yanzu ya gane cewa ya jima yana jiran shigowar Sa’adatu cikin rayuwar sa, he'spatiently waiting for her to come to his life ba tare da ya sani ba, sai a yau ya gane hakan.
A can baya kafin zuwan wannan ranar jin sa yake tamkar bashi da komai tamkar bai taba mallakar komai a rayuwar sa ba, duk da ba abinda bai mallaka din ba a rayuwar tasa including ASIAN WIFE.
Amma a yanzu da yake durkushe gaban Mai Askira yana yi masa wannan bushara sai yaji tamkar Askirama ya mallaka masa dukkan mulkin matan duniya, da mulkin dake cikin duniyar, mulkin da ya fi na garin Askira girma da ilahirin El-Kanem Borno Empire, da duk wani nau'in farin cikin dake cikin duniya da dan adam ke burin samu da ya mallaka masa Saadatu diyar Bilkisu da Mallam Hashimu.

Na gode da wannan gatan Mai Askira, Nagode ZAKIN Askira, ina mai rokon Ubangiji da ya fi ni godewa, na kuma karba da hannu bibbiyu. Ina rokon Allah Ya sa daga yau ba za ku sake jin wani abu a kaina wanda ya jibinci laifuffukana na baya ba.
Hakika na sani Askirama ni Sageer mai yawan laifi ne, mai saba muku ne, mai ketare tarbiyyar da kuka yi masa, amma hakan bai sa kun yi fushi da ni ba, kullum burin ku da fatan ku shine in dawo hanya madaidaiciya, wanda hakan yasa a kullum nake cikin tuba da neman gafarar Ubangiji. Ina rokon Allah ya fidda ni kunyar ku, Ya ba ni ikon rike muku yar ku da amana.
A yi min godiya wurin Fulanin Sarki (yana nufin Fulani Bilkisu), kodayake bari in je in same ta da kaina.
Askirama sai gani ya yi Yarima Sageer ya mike cikin wata irin azama, jikin sa har bari yake, gabadaya ya zama ba cikin nutsuwar sa ba, ya rude saboda excitement din da ya samu kan sa a ciki. Wanda Mai Askira zai iya rantsewa bai taba ganin sa cikin kwatankwacin irin wannan farin-cikin ba.
Sai Askirama ya mika hannu ya kamo hannun sa, kada ya je ya yi abun kunya a gaban bayi da kuyangin Fulani Bilkisu, kuma dai Fulanin ta gaya masa Saade ta dau fushi tun jiya ta kulle kanta a daki. Wanda ke nuna ita bata murna da auren ko kadan. Kamar yadda nasa dan ke neman shidewa sabida farin-cikin hakan.
Zo zauna in kirawo Fulanin ka yi mata godiyar nan a gabana, kada ka je sassan ta yanzu har sai bayan biki. Baa zuwa. Zuwa lokacin Saadatu ta huce daga laifin da muka taru muka yi mata.
Yareema ya yi murmushi yana sosa kai, laifi? Auren sa ne ya zamo laifi ga Saade? Kodayake bai kamata hakan ya zamo abin mamaki ba a gare shi duba da cewa daga shi har ita respect ne a tsakanin su, babu wata magana bayan wannan, koda ace akwai din ita a gareta babu komai tunda bai taba furta mata ba, ko nuna wata alama da zata gane cewa he sincerely admires her tun farkon rayuwar ta a gidan sa.
A lokacin suka hada ido da mahaifin sa wanda ya kura masa ido kawai yana murmushi, yana karanto duk abinda yake son karanta. Yareema Sageer yayi hanzarin dawowa daga duniyar tunanin da ya fada cikin jin nauyin kaifafan idanun Askirama. Kada dai ya zamanto cewa Mai Askira ya gane a rude yake gabadayan sa? Kuma already a rijiya yake? A rayuwar shi babu farin cikin da ya taba ruda shi irin na yau, kai mawuyaci ne wani abu yasa ya kasa mallakar kan sa amma yau? Saadatu a matsayin matar sa! Wani al'amari ne da bai zata ba. It comes abruptly. And it touches him more than he can imagine. Wani abu ne da bai taba kawowa zai samu da sauki haka ba, duk da zuciyar sa ta dade tana buri, kwakwalwar sa na kiyasta masa, ruhin sa na kwadayi da mafarkin kasancewar hakan.
Ba don bashi da gatan samun ta ba, sai don yana ganin hes not worth enough ga mallakar ta matsayin mata, in yayi laakari da tarin aibubbukan sa.

Maimartaba ya kira Fulani ta wayar hannun sa, suka yi magana ya aje, ya dubi Yarima wanda jikin sa ke ta (tsuma) ya kasa nutsuwa a waje daya, ya zama very upset, bai taba ganin dan sa Sageer cikin kwatankwacin irin wannan halin ba.. daga haihuwar sa har girman sa. Wanda ke nufin....(already Sageer na son Sa'adatu)!!!

Ba abin da ya furta a zuciyar sa sai godiya ga Ubangijin talikai, ya ce da Sageer a hankali cikin muryar sa ta girma da sanyawa dan adam nutsuwa, yana murmushin kasaita irin nasa ta kyakkyawan gashin bakin sa da farin gemu ya zagaye;

Be a Prince!". (Wato ya koma Yariman sa).
Yareema ya dafe goshin sa yana yar dariya da jerarrun hakoran sa bakidaya a waje, wannan ma wani abu ne da Mai Askira bai taba gani ba, iyakacin sa murmushi ga duk abinda yayi impressing din sa, sannan ya kuma koma cikakken Yariman sa ta hanyar kokarin sarrafa kan sa da komawa cikin nutsuwar sa.
Sai ga sallamar Sarauniya Fulani Bilkisun Askirama cikin kwalliyar ta ta kasaita, ta shigo ta kofar da suka saba shigowa bangaren Askirama ita da sauran matan sa, kowacce akwai kofar da ta bulla unguwar ta, zuwa turakan Mai Askira. Takun ta kadai abin kallo ne ga mijin ta.

Yarima na ganin shigowar ta ya dukar da kai kamar tsohon da ya yi wa sarki karya. Surukuta sosai yake nunawa yau ga Bilkisu. Bai taba jin kunyar ta matsananciya ba irin yau. Kafin zuwan wannan ranar, jin ta yake kamar Yayar sa Yaa Maira, ba matar mahaifin sa ba.
Alal hakika yana son matar nan ba tun yau ba, sau-tari, mantawa yake kishiyar Ya Gumsu ce sabida kirkin ta, mantawa yake da duk wani sabani da ke tsakanin ta da mahaifiyar sa sabida son da yake mata da kulawar da itama take bashi. Ashe Allah ya rubuta Kakar yayan sa ce masu zuwa nan gaba cikin kudurar Ubangiji.
Jinin su ne zai zo ya cakude wuri guda ya kara binding din su together. A can gaba. Ya kara dunkule su matsayin iyalin Sarki Yusufu Mai Askira. Ya kara nutsuwa a wurin da yake tankwashe zaman Rakuma akan kafafun sa, sannan ya gaishe ta da sassanyar murya, bayan ta zauna kusa da Mai Askira tana zolayar sa.
Ango! Ango ka sha kamshi.
In ji Fulani cikin murmushi.
Maimartaba ya juya gare ta yana tambayar ta,
“Fulanin Askira Me ku ke shiryawa ne game da biki?
Fulani Bilkisu ta gyara zama,sannan ta kaskanta murya cikin yanayin ladabin da Askirama kadai take yiwa magana da shi ta ce.
Alanguburo, ai ni rabon da in ga Saade tun jiya da na gaya mata. Ta shige daka ta kulle kofarta, watakila idan ta ji mutanen Tsanyawa sun zo ta bude, kuma dai dama bukukuwan gidan nan Ya Gumsu ce ta ke tsara su ga shi kuma tana fushi da ni a kan laifin da babu ruwa na.
Maimartaba ya ce, Zan turo Yaa Maira (babbar yarsa) ku tsara komai, Murjanatu ma tana kan hanya za su zo su same ki. Wannan kiran kuma na Yarima ne ba nawa ba, shi yake son ganinki, zai bi ki unguwarki na ce ya bari in kirawo ki nan, na ga yana ta bare-baren jiki kada ya je ya yi abin kunya a gaban bayi.
Dariya Fulani ta yi, shi kuma Yarima ya kara dukar da kai, murya a raunane ya ce.
Chapter 1 · 0% Book details