Sashe 8
Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
"Mamee dan Allah ki barni naje da gaske bazan jima ba dana karbo zan dawo yanzu pls" Hajiya Asiya ta girgiza kanta tana faɗin " ki duba time Am'baby ƙarfe tara yanxu gidan waye zaki je, gobe da safe idan kun haɗu a school kin karba" ta marairaice fuska kamar zatayi kuka tace "Mamee ke kike ganin dare yayi, kafin 10pm zan dawo idan banje na karbi Assignment ɗin ba gobe da sassafe yaushe nake da lokacin yin sa, pls mamee bazan jima ba nayi maki alqawari dan Allah" ta dafe goshinta kaɗan kafin ta dubeta tana faɗin " kinsan halin babanki yanzu ne daya dawo yaji bakyanan zai soma yi min faɗa kada ki kuskura ki bata lokaci ina jiran ki yanxu". Ta saki wata qarar farin ciki haɗe da sumbatar ta a goshinta cikin tsananin farin ciki ta ɗauki makullan motarta ta fice da sauri.
Fitowar sa harabar gidan bai tsaya neman kowa ba ya fice daga masarautar cikin gudu kaɗan kaɗan, bai fiye son zuwa Gym ba yafi son motsa jikinsa haka kowane dare in dai yana qasar, yana fita batare da kowa a tare dashi ba tun yana yaro ɗabi'ar sa ce, yayi nisa sosai da Masarauta, ya tsaya kaɗan yana maida numfashi a hankali kafin ya waiwaya bayan sa, babu kowa gurin shiru, ya furzar da iskar bakinsa kafin ya cigaba da Jogging, kamar daga sama yaji saukar abu a goshinsa, cak ya tsaya tare da dafe goshinsa cikin tsananin zafin daya ji ya ratsa kansa sosai, ya juya bayan sa babu kowa ya waiwaya ta ko ina ba alamar mutum, ya maida hankalinsa ga raunin goshinsa ganin jini na zuba sosai da alama dutse ne ya fasa masa goshi, cikin mamaki ya qara cira kansa dan duba waye babu zato yaji saukar duka a bayan kansa, yayi baya kamar zai faɗi cikin rangaji duk suka zagaye shi kusan su biyar, ya cira idanunsa kaɗan yana kallonsu ta cikin farin wata daya haske gurin duka fuskokinsu a rufe yake da mask banda ƙwayar idonsu babu abinda kake gani, ya lumshe idanuwansa a hankali cikin raɗaɗi dai dai lokacin da ɗaya daga cikin su yayi qoqarin kai masa wani duka, cikin zafin nama ya riqe hannunsa kafin yayi yunqurin yi masa wani abu daga bayansa aka ƙara kai masa wani dukan wanda babu shiri ya saki hannun ɗayan, suna qoqarin kai masa duka a tare hasken mota ya haske su wanda babu shiri suka tsaya suna kallon motar, dawowar ta kenan daga karbo Assignment ɗinta sai faman sauri take kada 10pm tayi bata isa gida ba kamar yanda tayi wa mahaifiyarta alqawari, ganin abinda ke faruwa ya bata tsoro sosai gani take ko waye ake duka kanta zasu dawo kamar masu fashi ne akan hanya, duk fuskokinsu a rufe, ta qara hasken motar tana tafiya a hankali yayin da suka fara matsawa baya cikin tsoron rashin sanin waye, alama yaqub yayi masu da hannu dasu bar gurin da sauri ba shiri suka fece, ta qarasa gurin wanda ake duka ta fito daga motar da sauri ta nufe sa cikin tsoro kada su dawo su same ta gurin, hankalinta ba qaramin tashi yayi ba da ganin irin jinin daya wanke fuskarsa, tsayin shekarunta bata taba ganin accident irin wannan ba ballantana duka, jikinta ya ɗauki rawa " zaka iya tafiya ka shiga mota muje asibiti da wuri kafin su dawo" babu yanda ya iya a hankali ya gyaɗa kansa kamar baya so, bata tsaya tunanin komai ko sanin ko waye ba ta riqa hannunsa da sauri ta ja sa xuwa mota, babu bata lokaci ta bar gurin kai tsaye Jos University Teaching Hospital ta nufa dashi, ganin yanda jini ke zuba a goshinsa babu bata lokaci suka karbesa domin bashi taimakon gaggawa. " Yana buqatar jini, ya zubar da jini sosai" likitan ya faɗa yana kallonta, ta shagwabe fuska a hankali kafin ta dubi agogon dake maqale a siririn hannunta almost to 10pm hankalinta ya tashi ta dube sa kamar zatayi kuka " Doctor bayan wannan taimakon da nayi banajin zan iya wani a yanzu, Mamee zata min faɗa ko ta dakeni idan na jima a waje, ka same shi ya kira family ɗin shi koma menene sai su zo, taimako kawai nayi na kubutar dashi daga hannun masu dukansa". Yayi murmushi kaɗan yana faɗin " hakan bazai yiwu ba Hajiya, baxaki kawo patient kije ki barmu dashi ba, komai zai iya faruwa and again babu wani abu da zamu iya masa a yanzu sai kinzo tare da police mun tsayar da jini, idan family ɗinsa sun zo zaki iya tafiya amma tabbas yanxu sai kinzo da police ko ɗaya ne" wani zufa na soma karyo mata jikinta ya ɗauki rawa ta nuna kanta da qaramin yatsa cikin tsananin ruɗewa saura kaɗan ta fashe da kuka " ni Doctor ina zanga Police iya gaskiya ta nake gayama taimakon sa kawai nayi bani ce nayi masa hakan ba". Hawayen da take qoqarin dannewa suka soma zuba, ganin hankalinta ya tashi sosai yace " kada ki damu babu wanda zaice kece kika masa haka, illah qa' idar asibiti ne irin wannan case dole sai police sun xo sun ɗauki report, taimako ɗaya zan maki a yanzu ganin yanda kika tada hankalin ki, zan haɗa ki da ɗaya daga cikin staff ɗina yanxu kuje tare sai kuzo da police ɗin". Tace " Meyasa shi bazai je shi kaɗai ba sai tare dani? Likitan ya bata fuska kaɗan yace " Malama ki ɗauki patient ɗinki ki fitar dashi daga asibitin nan idan har bazaki bi ƙa'ida ba." ta marairaice fuska " Sorry pls, yazo mu je". Ba bata lokaci ya kira ɗaya daga cikin Staff din Ayuba ya haɗata dashi, bayan sun je police tayi bayanin komai suka ɗauki report, kafin su zo asibitin, acan ma suka ɗauki report da komai, suna qoqarin tafiya su kayi mgnr abinda zata basu, ta dafe kanta kaɗan cikin baqin cikin wannan taimakon da tayi da tasan haka zata wahala da bata tsaya taimakon sa ba tafiyarta zata yi, tace " Nawa ne kuɗin? " ko nawa kika bayar zamu karba " ɗaya daga cikin su ya faɗa, ta nufi motarta bata tunanin tana da kuɗi jikinta a sanyaye ta buɗe motar, jakarta ta gani ta saki ajiyar zuciya kaɗan bazata rasa wani abu aciki ba, kudin dake ciki ta ciro ta basu batare da tasan ko nawa ne ba, yanxu babban burinta duk bai wuce doctor yace ya sallameta tabar asibitin ba, kai tsaye ɗakin da aka kwantar dashi ta nufa, Doctor tsaye akansa yana rubutu a file ɗinsa, tace " Doctor shikenan zan iya tafiya, idan ya farfado ya nemi family ɗinsa, iya abinda zan yi nayi a barni haka" likitan ya juya kaɗan ya dube ta kafin ya maida hankalinsa kan rubutun da yake " ki jira akwai kuɗin da zaki bayar na services ɗin shi kuma na gayamaki yana buqatar jini ya zubar da jini da yawa, babu kowa a tare dashi yanzu wa kike tunanin zai zauna dashi yayi jinyar sa, kin taimakesa da farko kin kawo sa asibiti ki qarasa ladar jinya zuwa gobe da safe sai ki tafi idan ya dawo hayyacinsa", ta zaro manyan idanuwanta sosai tana kallonsa cikin kaɗuwa jin ya ambaci safiyar gobe, Modibbo dake kwance idanunsa a lumshe cikin tunanin abinda ya faru dashi da son sanin kosu waye ya buɗe idanunsa a hankali yana kallon inda take tsaye, kamar yasan fuskar, ya yatsina fuska kaɗan tuna inda ya santa, itace ta taimakesa kenan? Tunaninsa ya katse lokacin da yaji tana faɗin " Nawa ne duka kuɗin zan maku transfer saboda kuɗin hannuna duka na bawa police ɗinnan" Doctor yace " kije reception zasu nuna maki inda zaki yi payment ɗin" bata qara saurarar sa ba ta juya ta fice xuciyarta har wani qunci take mata ga kanta dake ciwo kaɗan kaɗan saboda wannan stress. Ya dubi Doctor kamar bazai yi magana ba yace " Doctor ko da zaa saka min jini bana son na siyarwa." yace " kana da wani da zai baka jinin ne a yanzu" ya lumshe ido kaɗan kamar bazai yi magana ba ya buɗe yana kallonsa yace " a yanxu babu shi amma idan zaku jira zuwa gobe ɗin nasan family ɗina duka zasu zo" "to me zai hana Su xo yanxu wannan yarinya ta je ga iyayen ta, mgnr gsky tayi qoqari ya kamata ka gode mata" da kyar ya buɗe baki saboda jikin dake masa ciwo sosai yace " Doctor babu waya a tare dani da na kira abokina yazo, and bana so na kira gida na sanar saboda mahaifina bashi da cikakkiyar lafia a yanxu haka, kayi haquri xuwa gobe i.....yayi shiru saboda numfashinsa dake sama yana dawowa da sauri da sauri, doctor ya ajiye file ya ɗaga murya sosai yana kiran Nurses kafin ya soma taba jikinsa, wannan patient yana buqatar jini da gaggawa Pls kira yarinyar da taxo dashi. Patient da kika kawo zai iya rasa ransa yana buqatar jini da gaggawa, doctor ya faɗa yana kallonta, ta zaro ido kafin ta ɗora hannu akanta sai ga hawaye " innalillahi, daga taimako wace irin jarabawa ce wannan, ynxu idan ya mutu nice zaa yi holding responsible ko Doctor? ya gyada kai cikin tabbatarwa, tace nawa ne kuɗin jinin? ta tambaya dai dai lokacin da idanunta suka sauka akan fuskarshi, ta matsa sosai xuwa gareshi cikin son tabbatar da abinda idanunta suka hango, shine wannan ɗan gidan sarkin, xuciyarta ta faɗa, shine ta taimaka? to ko iyayensa zata je ta sanarmawa ta tambayi kanta, noooo wata zuciyar ta amsa, ki qarasa taimakonsa idan ya farfaɗo dole ya sauke izzar sa yayi maki godia kin ceto rayuwar sa, ko ba komai kinci riba akansa, ta share hawaye da bayan hannunta tana faɗin Doctor a saka jinin zan biya ko nawa ne ." Doctor yayi jim kaɗan kafin yace " bansan dalilinsa na roqona cewa kada na saka masa na siyarwa ba yafi so daga wanda ya sani" tace " a ɗebi nawa Doctor idan zai yi" duk suka kalle ta cikin mamaki ko a ido sun san she's young bata kai age ɗin da zaa ɗebi jininta a saka wa wani ba, sannan menene dalilin sauyawarta lokaci ɗaya a ynxu? ta katse tunanin sa " kana mamaki ne dan nace a gwada nawa idan zai yi, am 18 ai na isa and beside kace emergency ne kuma baya son na siyarwa a gwada nawa idan zai yi pls kada mu rasa shi a kaini kotu" Doctor zai yi magana tayi saurin katse sa " pls Doctor aje a gwada a saka mashi kada mu rasa shi" doctor ya bayar da umarni aje a gwada nata ɗin.