← Book details Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 17

Sashe 3

Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ƙaton family house ne da zaa iya kimantashi da unguwa ɗaya saboda girman shi, gidan duka yana ɗauke da zanen sarauta a jiki, ga dawakai ciki da waje, kallo ɗaya zaka yiwa gidan ka tabbatar gidane na sarauta, fadar sarkin abin kallo ce daga abubuwan da aka ƙawatata da ita tamkar baa nan gidan mu nigeria ba, falon gidan ƙaton gaske ne yasha kujeru na alfarma masu kyau da tsada irin na sarauta kusan kala uku kowane rukuni, sannan kalar kujerun kala daban daban ne duk inda kaje ka zauna sai ka ɗauka wani falo daban ne kake ciki, akwai ɗakuna bazasu ƙirgu ba, sai dai daga cikin su manya ƙwara biyar ne, na sarki, modibbo, uwar gidan sarki, amaryar sa da babbar yayar sarki Hajiya kilishi. Hajiya Amina itace uwar gidan sa tana da yara biyu Laylah itace babba sai (modibbo), Hajiya Maryam itace mata ta biyu a gurin sarki tana da ƴa ɗaya farhana ita ɗin ta girmi modibbo bayan haihuwarta ne aka haife shi. Modibbo wani irin shagwababben yaro ne tun yana ƙarami, da wuya ka gane kansa idan ya rikice, soyayya da kulawar da yake samu a gurin iyayen sa ta saka shi yin duk abinda yaga dama a masarauta, kaifi ɗaya ne baya magana biyu kuma baka sanya mashi ra'ayi akan nasa, gabaki ɗaya rayuwar karatunsa yayi tane a spain ko hutu baya zuwa gida sai da ya kammala ya dawo, tun daga sanda ya dawo gidan komai ya sauya kusan shi yake controlling kowa a gidan. Hajiya kilishi tana da yara biyu Yaƙub shine babban yaron ta tantiri ne sosai musamman da yake jin kansa shi ɗan gidan sarauta ne, sai ƙanwarsa Hamida, su ɗin mahaifin su bai jima da mutuwa ba bayan rasuwar sane suka dawo masarauta da zama. Hajiya kilishi tana da babban buri a rayuwar ta na kasancewar ta sarki, hakan bai samu ba dalilin ita ɗin macece sai aka bawa ƙaninta sarautar bayan mutuwar mahaifin su, tun daga lokacin da aka bawa Sarki Muhammad sarauta take cike da baƙin ciki a zuciyarta da neman hanya ko tayaya ne ta raba sarautar da ƙaninta ta dawo hannunta, babu abinda take so kamar ganin Yaƙub ya gaji sarauta ba modibbo ba, wannan dalili ya saka ta ɗauki aniyar haɗa auren modibbo da hamida ta yanda idan ya auri ƴarta zasu samu sanadiyar karbe sarautar daga gare su. Laylah babbar ƴar sarki yaya a gurin modibbo tana auren ɗan wani hamshaƙin ɗan kasuwa, auren ma bai jima ba duka wata huɗu da suka wuce duk tare akayi auren su da Farhana ƴar wajen Hajiya Maryam amaryar sarki. Modibbo bai taba kallon wata ƴa mace da sunan soyayya ba, bai san so ko akasin sa ba babu abinda ya sani illah mulki da izza, a duk lokacin da mahaifiyarsa zatayi masa mgnr aure zai yi murmushi yace duka duka ni na nawa ne Umma? Am just 30yrs ban isa aure ba kuma ni bani da wacce nake so. Tace " akwai waɗanda suke son ka Yarima shekara talatin kace baka isa aure ba, to sai yaushe? Yace " sai na girma, ni baxan iya kula da mace a yanzu ba, bansan yanda zan dubi wata mace nace ina son ta ba, ni bansan yanda zan zauna da mace nayi mata wasu kalami da zasu faranta mata ba, ban iya soyayya ba Umma" tace " ka nemi matar ni zan koya maka soyayyar zan nuna maka yanda zaka tafiyar da ita tunda duk baka sani ba" ya tabe bakinsa yana faɗin " da kin bar mgnr babu macen da zan so a yanzu banganta ba har yanzu" ta jinjina kanta a hankali cikin izza tace " sanarda ni kalar matar da kake so yarima" yace " mai shagwaba irina, wacce ra'ayin mu zai zo ɗaya da ita bata da tsoro kaifi ɗaya kamar ni" tace " idan na fahimce ka kana son mace da zaku nunawa juna izza ba mace mai tarbiya da kowane namiji yake ƙoƙarin nemowa ƴaƴansa ba." yayi shiru alamar zancen ya ƙosa da shi, tun daga lokacin bata ƙara masa mgnr aure ba ganin baya so illah addu'a da take yi a koda yaushe Allah ya haɗa shi da macen kirki. Alhaji Aliyu shine ɗan Galadiman Sarki Muhammad, babban amininsa ne tun ƙuruciya yana da mace ɗaya Hajiya Asiya da ƴarsu ƙwaya ɗaya tal suna kiran ta da Am'baby kasancewar sunan mahaifiyar ɗan galadima aka sanya mata. She is just 16yrs a shekarar ta ƙare secondary school ɗinta ana kiciniyar fitar da ita waje karatu taƙi ita lallai a nigeria tare da friends ɗinta zata cigaba da karatu, gata da kulawa suke nuna mata duk abinda take so shi suke mata basa son bacin ranta ko kaɗan, sai ta taso marar ji kanta a tsaye kuma sangartacciya, kuma tana jin kanta da sarautar mahaifinta, ko acikin frnds ɗinta yanda take so haka suke mata, bata da wani saurayi wanda zata ce tana sonsa da gaske har cikin ranta duk samarinta kallo ɗaya take masu friends kawai idan ka matsa mata da soyayya sai tayi blocking naka wannan dalili ya saka mazan da suke tare da ita suke lallabata sosai, Am'baby macece mai shiga zuciya sosai saboda wasu kyawawan ɗabi'un ta, idan ka zauna da ita ko na minti goma dole zaka ji kana son sake zama da ita, duk wannan halin nata bata da wulaƙanci ko girman kai, tana da tausayi sosai kuma ko a ƙawaye bata da zabi cewa sai masu kuɗi ko mulki, kowa nata ne da talaka da mai kuɗi ko a class bata raina kowa dalilin haka take da alot of friends da suke son kasancewa da ita. Sosai tana zuwa masarauta inda Hajiya maryam mahaifiyar farhana saboda ƙawaye ne da mamanta, bata san modibbo ba bata taba ganin sa ba tana jin sunan sa a bakin mutane da mahaifinta haka ta taba ganin mahaifiyar sa sau ɗaya shima dalilin bikin yayyunsa da akayi. Hajiya Amina ma sau ɗaya ta taba ganinta a sashen Hajiya maryam tana barci sanda taje duba abokiyar zamanta bata jin daɗi (a tsakanin su zama ne na amana babu baƙin kishi tsakanin su sai wanda baa rasa ba, haka suna ziyarta juna idan ɗaya baya jin daɗi) sanda taga Am'baby kwance tana barci tayi mata kyau a ido tace " Hajiya ina kika sami cute yarinya haka" tace " baki san Am'baby ƴar gidan galadima ba, aikuwa tana zuwa nan sosai" Hajiya Amina ta girgiza kanta " bansan yana da yarinya mai girman wannan ba" Hajiya maryam tace "aikuwa gatanan sarkin rigima," . Alhaji Bello Aji sanannen ɗan kasuwa ne a Gombe mutum ne mai dattako da sanin mutuncin ɗan adam, yana da taimako sosai ko a unguwar su anyi masa wannan shaidar, yana da mata ɗaya Hajiya Hauwa da ƴarsu ɗaya Zaynab wacce suka ɗauki son duniya da buri suka ɗora mata, irin soyayyar da suke nuna mata ya saka yarinyar take abubuwa sosai a boye wanda basu da labari, zama da ƙawaye ya saka take shaye shaye duk basu sani ba, zuwa friends party kowane iri ne aka gayyace ta zata je abu ɗaya ne bata taba bari namiji yakai ga jikinta ba bata yarda a taba mutuncinta ba. Kamaludden Shariff shine cikakken sunansa, haifaffen ɗan garin Gombe ne, iyayen sa talakawa ne sosai amma gwargwado suna da wadatar zucci domin basu taba bari saboda talaucinsu sun wulaƙanta ba, mahaifinsa malamin primary ne yana da dattako da amana, ya kula da rayuwar matarsa da ɗansa kamal ganin ya sami ilimi sosai, bayan rasuwar sa ne kamal ya kammala degree ɗinsa amma babu aiki, yayi nema wurare da dama bai samu ba dalilin haka yaje ya koyi sana'ar hannu yake ɗinkin kayan maza yana samun wani abu suna rufawa kansu asiri, anyi masa baiko da Jiddah ƴar aminin babansa tun yana raye ya nema masa auren ta, suna son junan su da gaskiya.

Ku shigo cikin daular mu domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku,

MASARAUTA tare da alƙalamin FATYMA XARAH

FATY ~ISLAM daga alƙalamin UMMI A'ISHA

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu ɗaya kacal, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.
[10/4, 4:06 PM] Baby Aysher: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt

🛕 *MASARAUTA*🏤

©️Fertymerh Xarah💞

4
Chapter 3 · 0% Book details