← Book details Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 17

Sashe 17

Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Modibbo sam baka kyauta ba, atleast ka amsa mata ko da bazaka mata magana mai daɗi ba, and babu kyau ka fito ka nuna wa mace baka sonta da gaske, i feel her pain" Sadiq ya faɗa zuciyarsa babu daɗi, Modibbo yace " Then ka aure ta mana, a hakan ma ai kun fahimci juna, idan kana son ta ka gayamin wallahi zan shige maka gaba wajen auren And zanyi matuƙar farinciki bani da masoyi kamar kai, ka ƙare min komai Pls Sadeeq" tsaki Sadeeq yayi kaɗan yayi gaba yana faɗin kaji tsoron Allah a koda yaushe, ka tuna amana aka baka su. Modibbo bai yi magana ba ya nufi part ɗinsa, Sadeeq ya dube sa cikin mamaki bayan ya juyo yace " ita waccan bazakaje gurin taba ka sanar da zuwan ka, wai meyasa kake hakane, taya zaka aikawa yarinya zaka zo tana can tana jiranka sa'anan kayi tafiyarka kana so tayi maka duban maƙaryaci? Modibbo ya juyo yana kallonsa " Na manta ne, lets go".
Hamida lafiya kika zauna anan kina kuka, tun ɗaxu nake jiran shigowar ki naji shiru shine naxo na duba, ta faɗa jikin mahaifiyarta tana kuka sosai tace " Mummy baya sona, wlhy baya sona ya gayamin da bakinsa, Mummy sai kinga wulaqanci da yake min, ko magana mai daɗi bai faɗamin ba, kallo ma ban ishesa ba". ta shafa bayanta cikin murmushin ƙasaita tace " shine zaki zauna kina bata ranki da hawayen ki haka akansa, dama tunanin ki zai so ki a yanzu? Not now Hamida, baki san waye  Modibbo ba, And ta yaya kike tunanin mutumin da aka tilastawa auren ki zai so ki da wuri haka? "Mummy sai yaushe zai so ni, wallahi ina matuƙar ƙaunarsa" ta faɗa tana kai hannun kilishi gefen zuciyarta "kinji zuciyana tana bugawa, ina sonsa da gaske, kome zan iya akansa ki taimakeni kada na mutu" " baxaki mutu ba, kuma dole zai so ki, share hawayen ki, naga abincin kamar baa taba komai ba". Cikin hawaye ta rausayar da kanta " Umma bai ci ba, abokinsa ne kaɗai yasha fruits ina tsoron ya kamu da soyayyata". Cikin murmushi kilishi tace " ai abu yana tasiri akan wanda akayiwa, duk abinda muka saka aciki da sunan modibbo akayi bada wani ba, saboda yaci babu abinda zai faru, shi modibbo idan baici anan ba ai zaici a gidan auren ku, sai ya zubar da hawaye dalilin ki ni na gayamaki, ki kwantar da hankalin ki". Yakub ya shigo da barasa a hannunsa kallonsa suka yi lokaci ɗaya, Kilishi tayi tsaki kaɗan tana faɗin " ashe baka daina shan wannan abar ba, bakaji gargaɗin da Sarki yayi akanka game da wannan ba, kaji ya rantse idan aka ƙara ganin ka da ita a gidannan zaka bar masarauta, meyasa baka jine? taya kake tunanin zakayi gadon sarauta bayan kowa ya san kana shan barasa? " shi shikenan shikenan na daina, afuwan Hajiyata dagaaa wannannn bazaaa koma ba" yayi shigewarsa kamar zai kife a qasa, ta girgiza kanta tana kallon Hamida, " kije ki cire waɗannan kayan, kici abinci". Hamida ta fice da sauri.
*
Tun a bakin gate na gidan ya haɗu da Modibbo da Sadiq, cikin sakin fuska ya tarbe su tare da masu iso zuwa babban falonsa , bayan sun zauna suka ƙara gaisawa kafin Galadima yace " nayi mamakin ganin ka a wannan gidan a yau, muna masarauta ɗaya amma rabon daka shigo gidannan tun kana ƙarami, Allah yasa lfy na ganka a yanzu? Kafin Modibbo yayi magana Sadiq yayi caraf yace " dama munzo gurin tane"(yayi mgnr yana sosai kansa kaɗan saboda bai san sunan ta ba). Nan take galadima ya gane zuwan na Am'baby ne, ya washe baki cikin farinciki yace " babu damuwa, bara na turo maku ita' ya tashi ya fice, Sadiq ya dubi Modibbo yana faɗin " ka sakani jin kunya, sunan tama na kasa faɗa". Modibbo yayi masa banza, kusan minti goma suna zaune a gurin babu alamarta, ransa yayi matuƙar baci bai taba jiran kowa ba sai dai a jirasa, a fusace ya tashi da nufin tafiya Sadiq yayi saurin riƙo Hannunsa yana kallon sa, " yi haƙuri nasan baka taba jira ba, amma atleast kayi tunani laifin mune, ƙarfe nawa muke zuwa past 10 fa, meyiwuwa tayi jira ta gaji taje ta kwanta, just 5 minutes idan bata zo ba sai mu tafi". Batare da yayi magana ba ya zauna cike da bacin rai yarinyar ta gama rainasa saboda kawai jininta yana jikinsa, bai jima da zama ba ta shigo da sallama a bakinta, Sadiq kaɗai ya amsa yana kallonta, tana sanye da hijab iya gwiwarta hakan ya bashi damar gane sanye take da kayan barci, fuskarta ta nuna kamar mai barci aka tayar da ita, ta sami guri ta zauna batare da ta ƙara magana ba, shiru na ɗan wani lokaci kafin Sadiq ya dube ta a karo na biyu yace " Uwargida Sarautar mata, da alama mulki ake ji haka" ta tunxuro baki kaɗan kamar bazatayi magana ba sai kuma tace " Daddy ne ya matsa min akan nazo". toh fa, Sadiq ya faɗa a ransa yana satar kallon Modibbo kafin yace " mun sanar da zamu zo ai" , tace " amma yanzu dare yayi fa". Yace " komai dare nayi tunanin zaki iya jiran mu tunda mun faɗa zamu zo,  anya kina ji da abokina kuwa? Tayi shiru bata amsa ba, kanta a ƙasa, yace " kinyi Shiru Uwargida, gashi ni bansan sunan ki ba, kuma maigidan ki yana mini rowar sunan ki, banga laifinsa ba, kin cancanta". Ta ɗago kaɗan tana kallonsa, tace " Am'baby" yace " Nice, amma sunan na gaskiya". Cikin ƙosawa tace " Jaudah and You? yayi murmushi yana faɗin Sadiq, babban aminin Mijinki". Tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta, tun zuwansu ta kasa kallon ko inda yake, bata san dalili ba, "Uwargida kamar bakya farinciki da zuwan mu" ta girgiza kai a hankali, yace " Naga ko ruwa baki bamu ba" ta dube shi kaɗan " kayi haƙuri" ta tashi da nufin fita yace " a'a ki barshi a ƙoshe muke, zo ki zauna". Tace " ina zuwa bara na kawo wani abu" bata saurare shi ba ta fice ya juya yana kallon Modibbo yace " sai ka barni da tsula tsulan matan ka ina magana dasu, ya kamata kana magana atleast ko sau ɗaya ne". Cikin bacin rai Modibbo yace " ka gama zubar min da mutunci da ƙimata har kake tunani nace wani abu, baka ga abinda kake aikatawa ba? Cikin rashin fahimta sadiq yace " menene nake yi ba dai dai ba, idan kuskurene nake yi meyasa kai bakayi mgn da kanka ba, ina ji dama munzo saboda ku fahimci juna kuma kasan bukatunsu saboda biki, amma meyasa kake shiru duk inda muka je idan kana tunanin ba dai dai bane". Modibbo yace " then meyasa kake Magana tamkar kana rarrashin su? Dukkansu yara ne Under 20, Muyi magana akan abinda yazo damu, menene damuwar ka da baa kawo mana abin sha ba, just imagine matsayinka har ya kai kayi roƙo? Tabe baki Sadiq yayi dai dai lokacin da ta shigo falon, ta ajiye abinda tazo dashi a gabansu kafin ta sunkuya ta ɗauki Tropical punch mocktail ta miƙawa sadiq tana faɗin " kayi haƙuri Yaya dama nayi ne saboda ku, tunani na bazaku zo ba saboda dare" ya karba yana faɗin " babu komai ƙanwata tunda an bani matsayin brother, saura Angon ki bashi". Ran Modibbo ya ƙara baci, sai an roƙeta tukunna kafin ta bashi, tayi jim kaɗan kafin ta ɗauka ta miƙa masa cikin girmamawa, bai karba ba, bai kuma ɗago daga kan wayarsa ba, Sadiq yayi murmushin takaici yana faɗin " Uwargida tana magana hankalin ka yana kan waya" ya ɗago a hankali idanunsa akan jan lallen dake hannunta, taja ƙaramin tsakin da take da tabbacin tabbas yaji kafin ta maida ta ajiye ta zauna cikin bacin rai, shi me ya ɗauki kansa ne? Sadiq ya dube ta " kiyi haƙuri kinsan jinin sarauta, a ko ina nuna izza suke, amma nasan one day zaki mana maganin shi" tabe bakinta kawai tayi, yace " dan Allah Am'baby kina son Modibbo da gaske? Karo na farko daya ɗago yana kallonta don jin amsarta, baisan dalilinsa na son jin me zatace game dashi ba, kuma baisan dalilin dayasa baiji haushin tambayar da Sadeeq yayi ba sabanin ɗazu da yayiwa Hamida, " Gaskiya bana son shi" ta bayar da amsar kai tsaye, Mamaki ya cika Modibbo, tun da yake a rayuwa babu macen da ta taba ganinsa tace bata so sai wannan? Menene a tattare da ita har take jin kanta wata, ya soma kallonta ƙasa da sama, to ko dan ta taimake sa ne ya saka ta raina shi tana ganin kamar bashi da karfi ko makamancinsa? Sadeeq kansa yayi mamakin furucinta, gsky kam bai taba jin mace tace batason Modibbo ba sai wannan karon, yace " Meyasa", tayi shiru, yace " bakya sonsa kika amince ki aure sa? Tace " Biyayya zan yiwa mahaifina dan bani da zabi, kuma friends ɗina ma sun amince na aure sa shine dalili". Cikin mamaki Sadeeq yace " Friends, dama abokai suna zabawa mutum abokin rayuwa ne? Tace " uhmm tam ni dai zabinsu shine nawa, naje gun Mama Amarya ta tura min picture ɗinshi na nuna masu, and suna son shi shine dalili" Sadeeq yace " kice kin yiwa abokina terere, yanxu idan basu amince ki aure sa ba kenan bazaki aure sa ba" tace " No zan aure sa saboda Daddy, amma ni gsky bana son sa ina son namiji mai ƙarfi". Kafin sadeeq yayi magana tuni Modibbo ya tashi ya fice, duk suka bisa da ido.

End of free pages.

Ku shigo cikin daular mu domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku,

MASARAUTA tare da alƙalamin FATYMA XARAH

FATY ~ISLAM daga alƙalamin UMMI A'ISHA

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu ɗaya kacal, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.
Chapter 17 · 0% Book details