Sashe 16
Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da kanta taje ta buɗe masu, Sadiq ya fara shigowa kafin Modibbo, sai faman murmushi take suka sami guri suka zauna kafin su gaidata cikin girmamawa, Nan da nan ta bayar da Umarni azo da abinda ta tanadar masu domin suci, kafin kace kwabo an cika gabansu da abinci kala kala, Sadiq ya dubi Modibbo cikin tunanin duk wannan abubuwan a wane ciki zasu zuba su, abincin kusan mutum ashirin koma fiye, Modibbo kamar baisan abinda ake ba sai danna wayarsa yake har lokacin da kilishi ta tashi tana faɗin " zan shiga ciki bari na kira maku Hamida sai ta zuba maku duk abinda kuke son ci ku ci" Sadiq ya gyaɗa kai cikin murmushi yana godiya harta fice, ya juya yana kallon sa, " Modibbo meyasa kaƙi kace komai kabarni sai godiya nake, haba dan kai fa duk akayi wannan atleast ko sau ɗaya ne kace mata thank you zata ji daɗi". Yace " bazan ce ba saboda bani nace ayimin ba, kuma babu abinda zanci saboda ni ba mayunwaci bane, na tsani matar nan idan baka sani ba saboda nasan bata son mulkin mahaifina, kuma itace dalili na biyu da ta saka aka aura min ƴarta". Sadiq yayi ajiyar zuciya kaɗan yace " kayi haƙuri ka sauke wannan abun da kake ji game da ita a yanzu, saboda mahaifiyar matar kace respect her, and....yayi shiru sakamakon taku da suka ji alamar ana shigowa, ya gyara zamansa da zaman hularsa gogan kuwa ko ajikinsa yanda yake zaune tun farko yana nan ko motsi bai yi ba har zuwa lokacin da suka shigo, har gabansu ta ajiye Hamida sai murmushi take cikin farinciki, Hamida ta gaidasu, Sadiq ya amsa, Hajiya kilishi ta fice tana faɗin " ki tabbatar sunci wani abu, nasan ki sai ki zuba masu ido". Hamida murmushi tayi a kunyace, Sadiq sai kallonta yake da yanayinta, "Masha Allah Amaryar mu ba laifi" ya faɗa cikin murmushi yana satar kallon Modibbo wanda har lokacin bai motsa daga inda yake zaune ba alamar Mulkin ya motsa, cikin sanyin murya ta gaidasu har lokacin kanta a sunkuye, Sadiq kaɗai ya amsa, ta saci kallon modibbo wanda sam har zuwa lokacin kamar baisan da zuwan ta ba, ta soma zuba masu abinci da abinsha kafin ta dube su karo na biyu cikin murmushi tana faɗin "Bismillah" Sadiq shima ya maida mata da murmushinsa yana faɗin " da wuri haka, kafin nan ai ya kamata mu san juna ko, tunda wannan shine karo na farko da muka taba haɗuwa dake duk da kina a gidannan, Da farko Sunana Abubakar amma anfi kirana da Sadeeq, nine babban aminin Modibbo wanda yafi ji dashi fiye da kowa acikin abokansa (yayi mgnr cikin tsokana yana satar kallon modibbo wanda har lokacin bai ɗago ba), tare muka yi karatu a Spain, munsan Halin juna sosai kuma mun san abinda ɗayan mu zai iya aikatawa da akasin sa, And Modibbo ba sai na gayamaki ko waye shi ba saboda a Masarauta kike a gurin mutane ma zakiji labarin sa, inace ma ke ƴar'uwar sace, bazan boye maki ba kin sami miji nagari ki godewa Allah. Ta janyo mayafi tana rufe fuskarta cikin Murmushin farinciki wai Modibbo ne a gabanta, duk da kasancewarta cousin ɗinsa basu taba tsayuwa guri ɗaya kona minti ɗaya ba, bai taba bata wannan fuskar ba, bayan gaisuwa babu abinda yake haɗasu wani lokaci ya amsa wani lokaci ko kallo bata ishe sa ba, Allah na gode maka take faɗa a zuciyarta, Modibbo banda harara babu abinda yake aikawa Sadiq sosai yaji baƙincikin da bayanin da sadiq yayi, ita wacece da zaa zauna ana gayamata ko shi waye ko menene halinsa, meyasa Sadiq ya fiye shishshigi ne a rayuwarsa, Sadiq ya katseta yana faɗin " muna so musan wacece ke" tace " Sunana Hamida, ni Cousin ɗinsa ce, Mahaifina ya rasu Shekara huɗu kenan, Nayi karatu anan gida Nigeria And.... " zan fita daga waje na jira idan ka gama sai kazo mu tafi ina da abun yi" yayi maganar yana ƙoƙarin tashi, Sadiq yayi saurin riƙe hannunsa cikin magiya ya sassauta muryarsa yace " Haba ko ruwa ne kasha mana, duk fa saboda kai akayi wannan kace baxakaci komai ba, atleast ko sau ɗaya ne ka dubeta kaga irin kwalliyar da....ya janye hannunsa kaɗan bai tashi ba kuma ya kasa kallon Hamida, cikin sanyin murya tace " dan Allah kuci wani abu" Sadiq yayi murmushin ƙarfin hali yana faɗin zamu ci Hamida kada ki damu, Hannu ya kai akan kayan marmarin ya soma sha yana taba Modibbo a boye alamar yaci wani abu, ko kallonsa baiyi ba, cikin murmushin yaqe ya dubi Hamida yace " fatan babu wata Matsala? ta girgiza kanta kaɗan yace " anata shirye shiryen biki ko? tayi murmushi kadan tana gyaɗa kai yace " Masha Allah, akwai wani abu da kike da buƙata a wajen mu keda ƙawayen ki? tayi jim kaɗan kafin ta dube sa tace " akwai da yawa ma, amma bani zanyi Magana ba, da friend ɗita zakuyi Magana zata zo gobe". Yace "tam babu damuwa idan tazo sai kiyi ƙoƙarin haɗa mu" ta jinjina kanta, ya cigaba da faɗin " fatan Hamida zamu same ki ta kirki, kinsan aure ba abu bane na wasa, aure ba gurin nuna mulki ko ƙasaita bane, wurine na ibada da raya sunnah manzon Allah S.A.W, wuri ne wajen nuna jajircewa da haƙuri, ina so na maki wata tambaya, yaya kike jin Modibbo a zuciyar ki, kamar yanda aka mashi dole na tabbata kema dole aka maki, kin karbi auren da hannu biyu kuwa? ta ɗago tana kallonsa kafin ta dubi modibbo da har lokacin yana kan danna wayarsa tace " na shirya zaman aure dashi, kuma ni ba dole aka min ba na jima ina son sa zan iya zama dashi a kowane yanayi" tayi mgnr cikin sanyi, karo na farko daya dube ta tun bayan shigowar su, ta jima tana sonsa? ya ƙara tambayar kansa, yace " saboda kina sona kika saka mahaifiyarki ta matsawa mahaifina akanki? Sadiq ya dube sa da sauri baiyi tunanin zaiyi magana ba, Hamida kuwa da sauri ta girgiza kanta tana faɗin " ba haka bane....yaya ne? ya jefo mata wata tambayar, saboda kina sona kika saka aka maki dole akaina, bakya tunanin kin ruguza tawa rayuwa, bakya tunanin ko ina da wacce nake so, saboda farincikin ki ni aka ƙuntata tawa rayuwar? Idanunta suka cika da ƙwallah " tace bani na saka amaka dole ba, kayi haƙuri amma ina sonka da gaske, sone da bazan taba iya boyewa ko nayi maka ƙarya akan sa ba" Sadiq yaji tausayinta sosai yadda take mgnr daga muryarta kaɗai zaka fahimci gaskiya, Modibbo yace " babu wacce nake so acikin ku, nima bazan maki karya ba ina da wata daban da nake so, ya rage naku idan kunji zaku iya zama dani a hakan, kuma wacce nake so ɗin bazan jima ba zan aure ta". Duk da taji babu daɗi a ranta hakan bai rage son da take masa ba illah kwaɗayin son kasancewa dashi da taji tana yi, yanda yake magana cikin sanyi da kwantar da murya kamar ba faɗa yake yi ba, komai nashi burgeta yake yi, tace baka ci komai ba. Yace "kin rainani, ni mayunwaci ne? Tace " kayi haƙuri" ya tashi ya fice a fusacce, Sadiq ya dube ta yana faɗin " kiyi haƙuri zai sauko kuma zai so ki amma sai kin jajirce kin ƙara da haƙuri kamar yanda na faɗa a farko, tashi muje ki raka mu amarya" ta tashi tana murmushi duk da akwai bacin rai sosai a ranta, yana tsaye yana gyara alkyabbarsa suka ƙaraso " Kayi haƙuri idan na bata ma, fushin ka yana sakani damuwa". Kallonta yayi cikin mamaki anya wannan tana da zuciya kuwa, ko fahimtar abinda ya faɗa mata ne batayi ba? Sadiq yace " Amaryar mu muna godiya sosai, Munga karamci sosai mun gane bazaa bar abokina da yunwa ba irin wannan girki da akayi kala kala duk da bamu tsaya mun ci ba ayi haƙuri next time komai zamu cinye baxamu raga ba, and gobe ina jiran ƙawar taki naji naku shirye shiryen kinga biki ya kusa". Tace insha Allah nagode sosai, Allah ya tada mu lafia" yace Amin, ta juya tana kallon Modibbo dake kallon wata a sama yanda ya fito yayi haske abin birgewane, tace " sai da safe" shiru bai amsa ba, ta maimaita kusan sau uku bai amsa ba, ta juya batare da ta ƙara kallon su ba, tayi shigewarta cikin bacin rai.
[10/18, 9:38 PM] Fertymerh: (TWE)
©️Fertymerh Xarah💞
🛕 *MASARAUTA*🏤
17
[10/18, 9:38 PM] Fertymerh: (TWE)
©️Fertymerh Xarah💞
🛕 *MASARAUTA*🏤
17