← Book details Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 17

Sashe 12

Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Umma wacece Jaudah?, Jaudah? ta maimaita sunan tana kallonsa, yanda idanunsa suka yi jawur alamar yana cikin bacin rai sosai, tace bansan ta ba, lafia na ganka a wannan yanayi? Yayi shiru saboda bacin rai ji yake kamar ya hargitsa ɗakin ko zai sami sauƙin raɗaɗi a zuciyarsa, hannunsa ta riƙa ta zaunar dashi kusa da ita tana kallon sa, tace " na rasa gane kanka Modibbo, dan Allah me mutanen da suka ɗauke ka suka yi ma, basu baka wata ƙwaya ko suka maka allura ba, yanayin ka kamar ba Modibbona ba, cikin kwana ɗaya ka canza inaji tunda muka dawo asibiti ko wanka kaƙi kayi, kaƙi kaci abinci, kaƙi ka kwanta ka sami hutu, me yake damun ka, baka taba haka ba." tayi mgnr cikin sanyin murya idanunta sun kawo ƙwallah alamar tsantsar damuwa ga Auta kuma tilon ɗanta. Yanayin ta kaɗai ya saka zuciyarsa karaya daga zafin da take, yaji babu daɗi ga halin da ta shiga kawai saboda damuwa da halin da yake ciki, ya sassauta riƙon da yayi mata a lokacin da ta riƙo hannunsa, kamar bazai yi magana ba ya jiyo kamar zaiyi kuka yana kallonta " Umma damuwata ɗaya ce kinsani jinin wannan yarinyar dake jikina, kuma yanzu naji da kunnuwana Abba yana nema min auren wata Jaudah, Umma wacece ita? Cikin rashin sani tace " bansan wata Jaudah ba, Yaushe kaji yana maganar kuma tare da waye, yaushe Sarki zaiyi hukunci irin wannan batare da neman shawarata ba? Da ƙyar yace " tare da Galadima yake maganar .....ta dube sa da sauri tana faɗin " Na tuna, na tuna yanxu yarinyar Galadima itace Jaudah saboda sunan Mahaifiyar sa ne aka saka mata." zumbur ya tashi daga zaune da yake, yace " wacce aka sakamin jininta ita ake nema min auren ta? ta qara zaunar dashi tare da faɗin "to menene aciki, ni ina son yarinyar tun ranar farko dana fara ganinta, tana da kyau, tana da son mutane bata da girman kai, ga ƙuruciya a tare da ita, ga shagwaba irin wacce kace kana so, babban abinda ya ƙara sakamin son ta a zuciya ta ceci rayuwar ka Muhammad, meyasa bazan so yarinyar ba? Yace "Umma ni bana son ta, ba irin macen da nake so bace, ko a mafarki ba irin ta nake hangowa ba, taya zaki fahimtar da sarki haka? Ta kai hannunta bayansa tana bugawa a hankali alamar rarrashi tace " believe me cikin lokaci ƙanƙani zakaji yarinyar a zuciyarka muddin ka zauna da ita ko na tsawon minti talatin ne, kayi haƙuri.....bai bari ta gama zancen ba ya tashi da sauri yana faɗin " bana son ta, babu abinda zai saka nazauna da ita har tsawon minti talatin, koda zan bar ƙasar nan zanje na bincika asibiti da yawa a online naje a fitar da jinin ta dake jikina".
*
"Wai Alhaji da gaske mai martaba da kansa ya nemi mu bashi Am'baby ya aurawa Modibbo" ta tambaya cikin tsantsar farinciki da mamaki, shima cikin murmushi yace " ƙwarai kuwa, kema kinsan bazan tallata mashi ita ba saboda bamu taba tunanin hakan zata faru ba, abu ne daga Allah kuma mu gode masa, ƴarmu zata je gidan mutunci da karama bugu da ƙari gidan sarauta kuma a tare damu cikin MASARAUTA" ta jinjina kanta cikin farinciki tace " tunani nake taya akayi yayi wannan tunanin, ashe taimakon Am'baby ga modibbo alheri ne, yaron da kowacce mace take kwaɗayin samu amma Jaudah ta samu batare da wahala ba, Allah yana son mu da alheri, Allah ya nuna mana wannan auren lafia" yace "amin" yana kallon Am'baby dake kwance tana latsa wayar ta kamar baa kanta ake maganar ba, yace "baki ce komai ba cwthrt kina son sa? Kallonsa tayi kamar bazatayi magana ba tace " waye Daddy? Yace " Modibbo wanda kika taimaka" ta yatsina fuska kaɗan tace " a'ah ni bana son sa, ina son namiji mai ƙarfi ba irin sa ba" yace " haba kin taba ganin namiji bashi da karfi Am'baby, sai idan anci karfinsa a yaƙi ne amma Modibbo ai ya kai namiji yana da ƙarfi sosai". Ta ajiye wayarta gefe tana faɗin " Allah Daddy bashi da ƙarfi, kaga yanda suke dukanshi amma ya kasa ramawa ko sau ɗaya, ni gsky bana son sa bazai iya tare min faɗa ba" "fiye da faɗa duk zai iya maki dan baki san waye shi ba, kuma ai kin faɗa su da yawa ne suka tarar masa ai bazai iya ba, ki amince da wannan auren zakiji daɗi sosai muma iyayen ki zamuyi farinciki". "Daddy ni bana son shi, ina so na auri best friend ɗina, wanda muke wasa da dariya a koda yaushe, ya san halaye na nasan nashi sosai, a friend that a kowane situation muna tare bazai barni ba, And i have alot of friends idan aure kake son yi min zan iya zaba acikin su cos kowanne yana sona amma ni bana son wannan ya fiye girman kai da izza kuma bashi da son mutane kamar ni, so kaga halaye nawa da nashi sun banbanta auren mu bazai yiwu ba". Duk wannan bayanin da take shiru sukayi suna kallonta cikin mamaki, duk yanda suke ganin ta bata da wayo ashe ba haka bane tasan zabin kanta, and abinda take cewa gsky ne mijinki ya zamo best friend ɗinka at anywhere, duk yadda suka so convincing nata akan auren fafur taqi aminta tun suna rarrashi har suka soma da faɗa, yanda taga iyayen sun haɗe kai akan sai ta aminta da auren ya ɗaga hankalinta, sam babu soyayyar modibbo ko kaɗan a zuciyarta, ita baya cikin irin mazan da take so aure, sai ta saka masu kuka sosai, ganin haka suka kyaleta akan bayan kwana biyu idan akayi discharging nasu asibiti zasu bi duk wata hanya da suke tunanin rarrashinta domin amincewa da auren.
Gabaki ɗaya hankalin Hajiya kilishi ya tashi sosai tun da labari ya riskesu cewa zaa haɗa auren Am'baby da modibbo, duk plan dinsu bai zo a yanda suka tsara ba, ga Hamida ta sanyata a gaba sai kuka take na fitar hankali akan bazata jure rashin modibbo ba " mummy meyasa sanda su yaya zasu je dukansa bamu je tare ba idan sun gama naje na bashi jini na, na taimake sa kamar yanda waccan yarinyar tayi, mummy kiyi wani abu akai mana wallahi ina son sa da gaske". Hajiya kilishi ta dube ta idanunta duk sun kumbura saboda kuka tace " insha Allah hamida sai kin auri modibbo ko ana so ko baa so, bara naje na sami shi uban nasa naji dalilinsa na wannan aikin batare da nemana shawara ba".
"Ranka shi daɗe naji wani labari a Masarauta cewa zaa haɗa auren modibbo da yarinyar galadima, ita Hamida a ina ka ajiye ta" yace "inaji mun gama wannan mgnr dake tun a farko da kika kawo zancen ta, Modibbo baya son Hamida muyi haƙuri. A fusace ta dubesa tana faɗin " ina da labarin Modibbo baya son yarinyar da kake son haɗasa aure da ita, hassalima itace yafi tsana da kowa a yanzu, jininta dake gudana a jikinsa neman hanyar fitar dashi yake yi....ya katse ta " saboda kin girmeni bazai hana ki girmama ni kamar kowa ba, a fada kika same ni baa gida ba, idan kika cigaba da ɗaga min murya tabbas zan saka ayi waje dake" "tuba nake ranka shi daɗe, tayi maganar cikin baƙinciki kamar zata haɗiye zuciya" ya cigaba da faɗin "Jaudah itace zabin da nayi masa zai sota fiye da tunanin kowa....tace idan na fahimceka kaine baka son auren sa da Hamida, amma meyasa? Hamida yar dangi ce yar asali kamar shi, uwa ɗaya uba ɗaya muke da kai, meyasa kake gudun auren su, me yarinyar tafi Hamida dashi, diri na ƴa mace ko kyawun fuska, kuɗi ko mulki? Yace " ko ɗaya kuma ina jin Hamida kamar shi Modibbo a zuciya ta kawai dai Allah bai nufa itace matar sa ba muyi haƙuri Hajiya". Sai ta fashe da kukan baƙin ciki ta soma faɗin " duk da kasancewata yayarka ashe akwai rana irin ta yau da zan nemi alfarma ka kasa yi min, shin menene aibu a tattare damu da baka son haɗa jini damu? Meyasa bazaa haɗa auren su duka su biyu a aura masa ba? Yayi jim kaɗan kafin yace "Modibbo duka duka nawa ne shi da zai iya riqa mata biyu a yanzu kuma tashin farko, mace guda bai taba zama da ita yayi rayuwa da ita ba balle mace biyu kuma rayuwa ta dindindin ta aure, bazan iya aura masa mata biyu a wannan shekarun nasa ba, kiyi hakuri hajiya ba....ta katsesa da sauri cikin kuka " wallahi baka sona baka son jinina a yau ka tabbatar min da hakan, kafison haɗa zuria da wani bare akan ni ƴar uwarka, da iyayen mu suna raye bazasu taba yarda da hakan ba, tabbas kaci mutuncina kuma tun da baka sona zan tattara komai nawa dake Masarauta ciki harda ƴaƴana mu bar maka Sarautar, zamuje muyi rayuwa can inda ake son mu amma bazan ƙara ko kwana ɗaya a Masarauta ba yau, na yafe ku har abada, ta tashi tana ƙoƙarin ficewa cikin tashin hankali ya dube ta yace " haba Hajiya ta yaya zaki nisan ta kanki da gidan mu na gado, akwai wani ɗan uwa da kike dashi bayan ni, kece kaɗai kika rage min a duniya idan kika tafi waye zan kalla a matsayin ɗan uwa" tace " tunda baka sona da ƴaƴana babu amfanin zamana dole zan tafi" yace shikenan na amince da auren Modibbo da Hamida.....kallon sa tayi fuskarta cikin tsantsar farinciki tace da gaske? Ya gyaɗa kai a hankali amma har a zuciyarsa baya farinciki da hakan kuma baisan dalili ba kawai jikinsa na bashi ba alheri bane wannan auren.

Ku shigo cikin daular mu domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku,

MASARAUTA tare da alƙalamin FATYMA XARAH

FATY ~ISLAM daga alƙalamin UMMI A'ISHA
Chapter 12 · 0% Book details