← Book details Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 17

Sashe 6

Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A daren ranar tana kwance, bayan ta fito daga wanka ta gama shirinta, ta feshe jikinta da turare sosai ta dubi Ruhayma, " komai dare kada ki rufe ɗakin kinsan dole zan dawo bana kwanciya a waje". Ruhayma ta dube ta kaɗan tace " Zeebu kiji tsoron Allah, iyayenki karatu suka turaki kiyi amma abubuwan da kike yayi yawa, lecture ɗinma bakya zuwa suna kashe kuɗin su.....ta katse ta a harzuƙe " malama kada ki gayamin mgnr banza kuɗin iyayen ki ko nawa, kuma waye ya gayamiki bana karatu, kuma duk shashancin da kike gani inayi ai bana mu'amala da maza ki barni da shaye shayen, amma ke irin ku ne kuke nuna Allah a baki sai a wayi gari a ganku da ciki". Subhanallah, Ruhayma ta faɗa tana janye book ɗin dake gabanta, Allah ya tsare ni kuma aniyar ki ta biki, lallai ni banyi dace da abokiya ta gari ba kuma ina roƙon Allah ya shiryaki yasa ki gane abinda kike ba dai dai bane kina mace, watarana ke uwa ce". Wayarta da ta ɗauki ƙara ta hanata magana ta fice da sauri tana jan dogon tsaki zan dawo na same ki dai dai nake da kowacce amsa taki, sai naji idan kuɗin iyayen kine". A mota ta same shi ta buɗe ta shiga sai cika take tana batsewa an bata mata rai, tun daga yanayinta ya fahimci hakan, yace " lafiya Cwty" tace " ba komai", " dan Allah ki gayamin waye ya bata miki rai, ko da muka yi waya kina farinciki da zuwana, yanzu nazo naga sabanin haka", taja numfashi kaɗan tana faɗin waccan banzar ce zata tsare ni da wa'azi sai kace kuɗin ubanta ne yake zuwa a banza, ita waye yasan abinda take aikatawa a boye, saboda kawai tasan nawa sirrin" hannu ya kai ya shafa goshinta yana murmushi " na ɗauka wani babban abu ne ashe ma akan wannan kike bata ranki kike son sakani damuwa, ki barta daga baya zanyi lokacinta, idan ta matsa miki zan turo a lallatsamiki ita, kin sanni ai" tace " aa kada ayi mata komai, ƙawatace ita, ka barta kawai" yace " na barta ta cigaba da bata miki rai, gsky bazai yiwu ba ni bazan jure ba" hmmm mu tafi bana so nayi dare, ina so na dawo da wuri, kallonta yayi " beb nayi tunanin acan zaki kwana tare dani? Tayi wani far da ido tare da murmushinta mai ƙara fito da kyawun fuskarta, tace " haba sai kace wata matar ka, ai kasanni bazan iya kwana a ko ina idan ba hostel ko gidan mu ba". Ya bata rai, zuciyarsa na wani ƙuna ta dube sa" kayi haƙuri". " mgnr gsky haƙurina ya gaza, atleast ko sau ɗaya ne ki bari mu kasance tare, ki gane irin son da nake maki, wlhy ina son ki da yawa Zee, idan ina tare dake da ƙyar nake controlling kaina" " shiyasa nake cewa muyi aure, Daddy na bazai yarda ba amma zan iya convincing nashi kuma nasan mummy zata tayani rarrashinsa". Ya shafa sumar kanshi, shifa banda kwaɗayinta dake damun shi da tuni ya barta amma bazai iya auren ta ba, bazai iya auren wannan mashayar ba, ya tayar da motar batare da yayi magana ba".

Gombe

"Umma zan tafi ko akwai abinda kike buqata a yanzu? Kamal ya faɗa cikin shirin sa na tafiya shago yana kallon mahaifiyarsa cikin girmamawa. Kallon sa tayi fuska a sake tana faɗin " bana buƙatar komai Kamaludden a yanxu, idan buƙatar son wani abu ya taso akwai sauran canji a hannuna zan yi amfani dasu, Allah ya dawo da kai lfy ya yiwa rayuwar ka Albarka". "Amin" ya faɗa tare da barin gidan da sauri kada ya makara, tuni salisu ya jima a shagon sai faman ɗinkinsa yake cikin sauri saboda akwai wanda ya yiwa alqawarin yazo ya karba da safen, suka gaisa kafin ya zauna gurin tashi tela yana faɗin " wannan sauri da kake haka fa? Batare da salisu ya dube sa ba yace " mai kayan nasan yana hanyar zuwa karba, bashi da uzuri yanzu ne zai zo yana min surutun tsiya alhali ko kuɗin bai cika min ba". Kamal ya jinjina kansa yana faɗin " nima gani mutum biyu sun riqe min kuɗi k....yayi shiru sakamakon hangota da yayi tana tahowa, Salisu ya dubesa jin yayi shiru kafin ya maida dubansa zuwa inda yake kallo, murmushi yayi yana faɗin " yau gimbiyar tamu ce tafe kenan". Kamal ya fito daga shagon Idanunsa akanta, murmushi tayi lokacin da ta qaraso inda yake, yace " ina zaki je haka? Kallonsa Jiddah tayi kafin ta dubi Salisu ta gaidashi a kunyace, yace " amarya yanzu nan fitowar sa ko aiki bai fara ba, kinzo ki hana masa aikin ko? Tayi murmushi tana rufe fuska da mayafinta kafin ta girgiza kanta kaɗan tace " a'a na dai zo na tayasa aikin". Salisu yace " masha Allah, bismillah shigo ki fara" taqi shiga shagon Kamal na tsaye na kallonta cikin shauqin soyayyarta, yace " Jiddah, lafiya dai ko? ta fito da ledah dake cikin mayafinta ta bashi kanta a sunkuye tace ɗinkine zaka min na ankon auren Easha, shine na kawo ma, bai karbi kayan ba ya dube ta yana faɗin " Amma shine har sai kinzo shago da kanki, meyasa bazaki aika min a gida ko ki kirani nazo na karba ba? Tace " kayi haƙuri, kuma dama dai ina so na ganka ne, ta faɗa tana janyo mayafinta tana rufe fuskarta, shima murmushin yayi, yace " to gani ki ganni iya son ranki Jiddah". Suka ƙarasa gindin wata bishiya suka zauna, salisu ya girgiza kansa yana murmushi soyayyarsu tana burgesa matuqa yanda suke so da kula da junansu, dama Hafsat ɗinsa haka take.

Ku shigo cikin daular mu domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku,

MASARAUTA tare da alƙalamin FATYMA XARAH

FATY ~ISLAM daga alƙalamin UMMI A'ISHA

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu ɗaya kacal, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt
[10/7, 9:38 AM] Fertymerh: (TWE)

©️Fertymerh Xarah💞

🛕 *MASARAUTA*🏤

7
Chapter 6 · 0% Book details