← Book details Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 17

Sashe 4

Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Kansa a sunkuye yake sauraren maganganun mahaifinsa cikin mamakin yanda yake roƙarsa da ya riƙe masa amanar company nasa da zai fara aiki yau, kallon sa yayi a raunane yace " Abba dukiyar ka kake roƙona na riƙe amana, ko kana tunanin zan cutar da kai" yace " ko ɗaya yarima, amanar mutanen dake ciki nake baka ba amanar dukiya ta ba, abinda na mallaka dani kaina duka naka ne, idan company ka siyar bazan tambaye ka saboda me ba nasan akwai dalili amma mutum ɗaya aka zalunta dake aiki a ƙarƙashin company zan tambayi dalili saboda su ɗin amana ne a wurin mu basu cancanci wulaƙanci ko tazarci saboda suna aiki a ƙarƙashin mu ba" modibbo yaja numfashi cikin takaici a ransa sai cewa yake dama saboda ma'aikatan ne kake tamin wa'azi haka tun ɗazu yaja guntun tsaki a ransa, a fili sai yamutsa fuska yayi yana ɗauke kansa gefe yace " ni bani da niyar cutar da kowa a wurin" sarki yace " madallah, sai magana ta gaba ka fito da mata ayi maka aure" a shagwabe yace " ni bana son aure, am not ready for it" sarki yayi jim kaɗan kamar bazai yi magana ba yace " yarima aure shine mutuncinka a yanzu a matsayin ka na mai jiran kujera, ka tuna bani da wata isasshiyar lfy a yanzu kuma kasani ko bayan raina kaine mai wannan kujerar da nake kai a yanzu, idan baka da iyali zasu iya aura maka kowacce irin mace suke so is better ka auri zabin ranka" yace " Abba ciwo da mutuwa duka na Allah ne, ni da nake da cikakkiyar lfy sai na mutu na barka, bana son kana zancen mutuwar nan saboda baka da lfy, dan Allah ka daina" ya faɗa yana riƙa hannu sarki cikin tsoro kamar zai rasa shi a lokacin, ya ɗora kansa a kafaɗad sarki sai ga hawaye, dogarai dake tsatsaye a gurin duk suka sunkuyar da kansu ƙasa cikin girmamawa, akwai so da shaƙuwa sosai a tsakanin su suna matuƙar son juna da girmama juna, basa nuna mulki ko izza wa junan su, sarki ya kai hannunsa bayansa yana shafawa a hankali cikin rarrashi yace " kayi haƙuri" modibbo ya ɗago yana kallonsa, " promise bazaka ƙara irin wannan mgnr ba" sarki ya gyaɗa kai cikin murmushi, yarima ya tashi da murmushi a fuskarsa yana kallonsa " insha Allah zaka sami sauƙi kafi kowa lafiya a MASARAUTAR nan, kafi kowa ƙarfi da jarumta, kuma ka cigaba da mulki cikin izza da gaskiya, kamin addu'a zan tafi" cikin murmushi sarki yace " Allah ya dawo da kai lfy" yace " Amin" ya juya, dukaa fadawa suka durƙusa ƙasa cikin girmamawa suna faɗin " a dawo lafiya yarima, Allah ya tsare ka ya kuma kare ka ɗan sarki" ko kallon su baiyi ba ya fice cikin izza, fitowar sa fada duka guards ɗinsa dake jiran sa suka taso da dogarai, ya nuna dogarai da hannun sa yana faɗin " ku jira ni a gida ba sai kun biyo ni ba" ya nuna guards ɗin yana faɗin " mutum biyu is ok sauran su jirani har na dawo, and ku shiga waccan motar, i will drive myself" ya faɗa yana tunkarar motarsa a hankali kamar baya son taka ƙasa. Yana shiga motar aka wangale ƙaton gate ɗin da sauri, yana ƙoƙarin fita motarta na kunno kai duk suka ja suka tsaya, tunanin shi ko waye a motar tunda yaga motar sa da sunan sa a jikin number zai yi ƙoƙarin ja baya ya bashi hanya ya fice, taja dogon tsaki cikin takaici tare da danna horn ɗin motar da ƙarfi idan baya ganin ta ai yana jin horn, kowaye bazai matsa ya bata hanya ta fice ba. Da sauri gateman da wasu guards suka ƙaraso ga motarta, knocking suka yi taƙi sauke glass ɗin motar tana kallonsu ta baƙin glass, tace ko waye fa sai ya matsa ya bani hanya bazan ja baya ba, nima jinin sarauta ce akwai izza a kaina, a harzuƙe wani guard ya buga motar da ƙarfi sai da ta zabura a tsorace, ta cikin glass take kallon fuskarsa da ƙirar sa sanye cikin black jersey ya ɗaura wani baƙin abu a goshinsa fuskarsa murtuk babu alamar wasa, ƙutt ta haɗiye wasu yawu tana faɗin idan na tsaya wasa ya ƙara dakar min mota zata tarwatse, ba shiri ta sauke glass ɗin motar cikin tsoron da bata nuna a fuskarta ba tace " malam lfy zaka dakar min mota? Yace " kiyi reverse da motarki idan ya fita ki shigo" " waye shi? Ta tambaya a gatsale cikin takaici, suka bata amsa da " Yarima ne" yarima? ta maimaita a zuciyarta, ta dubi yanda suka zuba mata idanuwa tace " shi meyasa bazaku ce yayi reverse idan na shigo ya fita ba, ai motata ta riga tashi" cikin mamaki suka zuba mata idanuwa suna buɗe baki, ɗaya daga cikin dogari yace " hajiya yarima akace maki, ko baki ji da kyau ba, kija motar kina bata masa lokaci" tace " nima kuna bata min lokaci, kuce yaja motarsa baabu abinda zai saka naja tawa motar" ta faɗa tare da ɗaga glass ɗin motar cikin tsoron kada su kaiwa motarta duka. Modibbo dake zaune a mota yana kallonsu ya danna horn, babu bata lokaci duk suka je ga motarsa a hanzarce tana zaune tana kallonsu, ya sauke glass ɗin motar yana tambayar " lafiya? tace " bazata ja baya ka fara fita ba sai ta shigo tukunna" " wacece ita? Ya tambaya kamar baya son magana " yallabai bamu santa ba" yace " tunda kace macece kada kaci mutunci ko zarafinta, kayi mata mgn ta bani hanya" ya maida glass ɗin sama, suka nufe ta tana ganin su ta sauke glass ɗin tana taunar cingam, " lfy kuka dawo min" " madam ki matsa baya yallabai zai fita, yayi magana kada a taba mutuncin ki shiyasa muke maki magana da rarrashi" ta jinjina kanta " ohhhhh, i see, a hakan rarrashina kuke yi, ok shikenan ni babu inda zan matsa idan har bazai bani hanya ba domin motata itace gaba da tashi" " madam wai wacece ke, me kike taƙama dashi, akace maki ɗan sarkin wannan masarautar zai fita har kike jayayya? Cikin takaici tace " ni ƴar galadiman wannan masarautar ce babu inda zan matsa" da sauri ɗayan dogarin yaje ya sanarda modibbo, "And so, dan ita ƴar gidan galadima ce sai me? har kake zuwa ka sanarmin saboda ka raina ni, ko galadiman ne bazai bani hanya ba balle ita". yayi maganar cikin calm voice, ba ƙaramin abu ke saka kaga bacin rai a fuskarsa ba. Guards ɗin ya ƙara dukan motar fiye da karo na farko, ba bata lokaci ta fito daga motar cikin tsoro, ta dube sa ta soma kallon tayar motar idan babu wacce ta fashe, ta dube sa a fusacce har zatayi magana sai kuma ta nufi motar da suke xuwa, ta jima tsaye a gurin kafin ya xuge glass ɗin idanunsa akan wayarsa batare daya dube ta, a shagwabe kamar tana gaban iyayen ta tace " malam dan Allah kaja motar ka baya ina so na shigo, kada wancan ƙaton ya fasa min mota" yanda tayi mgnr cikin marairaicewa ya saka shi ɗagowa yana kallonta, wai dama wannan ƙaramar ƙwailar ce take jayayya dashi ya faɗa a ransa, kamar bazai yi magana ba sai yace " idan bakyaso ya fasa maki mota kija baya na fita" tace " just look, motana ya rige naka fa and menene aciki dan kayi baya na shigo" yace " kija motar ki baya na fita" taja turus haɗe da rungume hannuwan ta a ƙirjinta, tace " ashe zamu kwana anan kuwa, dan bazan ja baya ba matuƙar bazaka fara bani hanya ba" kallonta yayi irin kallon kin isa, yayi alama da hannu guards ɗin suka zo da sauri, " waye mahaifinta? " ranka shi daɗe ɗangaladima ne" suka faɗa cikin girmamawa, ya dube ta yana faɗin " duk da kasancewar mahaifinki ƙasan mahaifina bazai hana ni darajashi ba saboda shi ɗin aminin mahaifina ne tun ƙuruciya, kija motar ki baya ko na kira mahaifin ki yazo nan da kanshi ya saka kija motar baya" cikin tsananin mamaki tace " wai da gaske sai ka kira mahaifina nan, hala shi sa'anka ne, tukunna ma menene aciki idan kaja baya na shigo, zai rage kane ko ƙara ka me kake ji a kanka haka? ya dube su yana faɗin " ku kira ɗan galadima" ta buɗe baki cikin mamaki ganin da gaske suke sai ta ɗaga murya kaɗan " dawo ba sai kun kira shi ba" ta tunzuro baki tana kallonsa tare da jefa masa key ɗin motar " rantsuwa nayi bazan ja baya ba sai idan kai zaka shiga kaja motar baya' ta maida kanta gefe, ya dubi key ɗin motar ya dube ta kana ya maida kallonsa ga motarta, ya juyo yana faɗin " ni na shiga waccan motar, kinga nayi kama da wanda zai shiga waccan motar, ya miƙawa ɗaya daga cikin guards ɗin key, yace reverse na bata lokaci anan, da sauri guards ɗin ya karbi motar cikin takaici tasa ƙafa ta shuri tashi motar tana faɗin wannan banzar motar dame tafi tawa, idan kuɗi da sarauta kake ji nima gidan mu akwai, tsab Daddy zai iya siyamin irin wannan motar and i promise you daga yau bazan ƙara hawa waccan motar ba sai irin taka". Yace " daga ranar da kika yi mota irin tawa na daina hawan ta har abada". Yaja glass ɗin motar tare da barin wurin da sauri bayan an janye motarta. Ta jima tsaye gurin ta rasa me zatayi ta shigo ko ta fasa zuwa inda Hajiya maryam, yau an wulaƙantata fiye da tunanin ta. Haka ta shiga motar cikin bacin rai ta nufi masarauta, duk yinin ranar bata yishi kamar ko yaushe cikin nishaɗi ba, Hajiya Maryam tayi tambayarta sai tace ba komai, tunani take hanyar da zata bi ta rama abinda yayi mata, abincin kirki kasa ci tayi haka ta shiga bawa friends ɗinta labari ta chat abinda ya faru da ita yau. Bayan magrib tayi nufin komawa gida, ta tashi tana faɗin " Momy zan tafi" tace " yau dai ban gane kanki ba Am'baby hirar ma bamu yi ba duk na ganki wata iri, kince lfyr ki ƙalau kuma" tace " uhm, idan na shigo wani lokaci zan baki lbr" tace shikenan, ta ɗauki ƙaramin mayafinta, key ɗin motar ta da jakarta ta soma tafiya a hankali kamar wacce ƙwai ya fashewa a jiki, hannu ta saka a handle ɗin ƙofar ta buɗe tana ƙoƙarin fita dai dai lokacin da yake ƙoƙarin shigowa, babu zato kanta ya daki ƙirjinsa saboda yafita tsayi, da sauri yaja baya kaɗan, ta ɗago tana kallonsa, idanunsu suka sarƙe dana juna kowane da mamaki bayyane a fuskarsa na ganin ɗan uwansa a wannan lokacin, ɗaure fuska yayi alamar ta bashi hanya, taja turus ta tsaya tare da turo baki tana rungume hannuwanta a ƙirji, " ka kira Daddy idan zaka iya, duk wanda zai zo nan wlhy bazan matsa ba matuƙar bazaka fara bani hanya na wuce ba sai dai ka fasa shiga ɗakin nan ko mu kwana anan tsaye ban damu ba".
Chapter 4 · 0% Book details