← Book details Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 17

Sashe 10

Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanyin safiya da hasken rana ya saka shi buɗe idanuwansa a hankali, ya kai hannu ya taba inda yake kwance, wannan baiyi kama da gadon sa ba, haka iskar da yake shaƙa a ɗakin ba irin ƙamshin ɗakinsa bane, to ina ne nan, ya tambayi kansa cikin tunani kafin ya kai hannunsa goshin sa, nan da nan komai na soma dawo masa baya, a asibiti yake kenan, zumbur ya tashi tuna cewa bai yi sallah ba, ba bata lokaci ya nufi ƙofar da yake tunanin toilet ce, bai jima aciki ba ya fito, bayan iddar da sallah idanunsa ya sauka akanta can rakube gefe, ya kasa tantance a zaune take ko a kwance, me take yi anan? ya ƙara tambayar kansa, shiru yayi daya tuna yaji Doctor jiya na faɗin itace ta cece shi, knocking da akayi tare da buɗe ƙofar ya saka shi waiwayawa da sauri yana kallon bakin ƙofa, Doctor ne tare da wata nurse suka shigo, sai dai ba Doctor ɗin jiya bane idan idanunsa ba gizau suke masa ba, bayan sun gaisa ya nuna Am'baby dake can gefe yace " meyasa take zaune acan? Batare daya kalli gun da take ba, yace " Doctor nima haka na ganta, bansan wacece ita ba? Doctor ya dubi Nurses ɗin da sauri yana faɗin " ya zaku bar wani ya shigo wanda ba relative ɗin patient ba, wacece ita? "Sir, itace ta taimakesa jiya tazo dashi asibiti, Inaji kamar ma itace ta bayar da jinin da aka sawa patient ɗin ko Humairah" ɗaya ta tambayi ɗaya, Humairah ɗin ta jinjina kanta alamar haka zancen yake, Modibbo ya dube ta kafin ya juya yana kallon sa, "Ni aka sawa jinin waccan? Wait, kuna so ku gayamin jinin mace ne a jikina, macen ma wacce ban sani ba bani da alaƙa da ita, wannan wace irin asibiti ce? Doctor yace " Calm down, wannan ba abin ɗaga hankali bane ka godewa Allah ka kuma gode mata ta ceci rayuwar ka, inshort abinda ke rubuce a wannan file din ya nuna Pcv ɗinka yayi qasa sosai wanda dole ana neman jini da gaggawa a saka maka, har suma kayi saboda rashin jini, duk wannan comment ɗin likita ne daya duba ka a jiya". Ransa in ya kai dubu ya baci har ya kasa buɗe baki yayi magana, idanunsa sukayi jawur alamar bacin rai, meyasa baa saka masa jinin namiji ɗan uwansa ba sai mace, macen ma wannan ƙaramar yarinya, yace "Doctor bani aron wayar ka, zan kira Mahaifiyata" babu musu, Doctor ya miƙa masa wayar yana faɗin Nurse, a duba yarinyar can wane irin kwanciya ne tayi haka, Suka je suna duba ta babu alamar numfashi a tare da ita, da alama ma kamar ta daɗe da suma a gurin, "Sir bata Motsi fa.." da sauri Doctor din yaje gareta yana miƙa masu file dake hannunsa, ya soma duba ta kamar bata numfashi, da sauri ya bada Umarni aka ɗauke ta zuwa wani ɗaki domin bata taimakon gaggawa, Modibbo ko a jikinsa, Hassalima kallo basu ishe sa ba, sai kiran wayar mahaifiyarsa yake bata ɗaga ba, ta barta ɗaki tana gurin Sarki, ya kira Number sarki duk da baya tunanin ya ɗaga saboda bai san number ba, yayi kiran wayar bata shiga ya tuna duk baƙuwar number bata shiga wayar Sarki, iska ya furzar kaɗan daga bakinsa gashi bai san Number Hajiya Maryam ba, kuma duk cikin abokansa babu number daya riqe akai,...kai ya tuna ya riƙe Number yayar sa Laylah, da sauri ya saka number yana kira, bata jima tana ringing ba aka ɗaga, da sallama ta amsa kiran, yayi ajiyar zuciya yana faɗin " Na kira Wayar Umma bata ɗaga ba, Kira Abba ki Sanar dashi ina Hospital." tace " akace anyi kidnapping ɗinka....ya katseta " Ni ki kirashi yanzu ki gayamasa ina asibiti." tace "wace asibiti ce? Yayi jim kaɗan cikin rashin sani yana dube dube saboda tuni sun fice daga ɗakin bayan sun ɗauki Am'baby idanunsa na sauka akan file ɗinsa da aka jiye a saman bed yace " kamar Jos university teaching Hospital nake gani akan file ɗin" tace " oh na gane asibitin, Amma Muhammad ( bata kiran sa da modibbo) Menene ya same.....ya katseta da sauri, " ki kira shi yanxu" ya katse kiran batare daya saurare taba, sanda ta kira ta sanar da Sarki tuni aka cika mota uku zuwa asibitin banda shi, amma duka matansa kowa yana so yaje yaga a wane hali yake ciki indai basu cutar dashi ba suka kai shi asibiti, shi kansa sarki dake gida hankalinsa baa kwance yake ba yana jiran feed back, galadima da matar shi suka bi bayan su ko zasu ji labarin Am'baby daga gare shi. Basu sha wahalar gane ɗakin da yake ba da taimakon wata Nurse, sai kai da kawowa yake a ɗakin ya kasa zama saboda bacin rai da yake ciki, shigowar su ya saka shi tsayawa yana kallon su, Haj Amina da Haj Maryam suka nufe sa da sauri " Modibbo, menene ya same ka, su waye suka ɗauke ka? Hajiya kilishi dake gefe tana yaqe ta soma addu'a a zuciya Allah yasa bai gane fuskar ko ɗaya daga cikin su ba, Modibbo yaso ya sanar dasu halin da yake ciki sai kuma yayi gum da bakinsa ganin irin mutanen da suka cika ɗakin, abin kunya ne a gurinsa idan akaji cewa akwai jinin mace a jikinsa, ya haɗiye wani yawu da ƙyar yana faɗin " Umma ace su sallame ni, babu abinda yake damuna, bana son wannan asibitin". Tace "menene ya same ka akai, dukan ka sukayi haka? ya shafa gurin yana yatsina fuska ba dan zafi ba sai dan baƙin cikin tuna ta dalilin ciwon aka saka masa jinin mace, Hajiya Maryam tace bari naje nayi magana da likitan, ta juya da sauri ta bar ɗakin wasu suka bi bayanta, Galadima ya matsa kusa dashi yace " kowa yayi tunanin tare da Am'baby akayi garkuwa da kai, ina aka barta Modibbo". Kallonsa yayi ba dan mutunci da kasancewarsa abokin mahaifinsa ba, daya ƙunduma masa zagi, yayi ƙoƙarin rarrashin zuciyarsa da ƙyar yace " ni ban san wata Am'baby ba, bana tare da kowacce mace". Hankalin Hajiya Hauwa ya ƙara tashi hawayen da take boyewa suka soma zarya tana faɗin "shikenan ƙilama sun kashe ta".....dai dai lokacin da Hajiya Maryam ta dawo tana faɗin ashe harda Am'baby tana kwance a wannan asibitin itama" duk suka juya suna mata kallon mamaki, tace "eh naje gun Doctor neman Discharge yake gayamin yarinyar da ta ceceshi itama tana kwance, shine naje duba ta naga ashe Am'baby ce, kai gsky Alhamdulillah da Allah ya nuna mana su k....Modibbo ya katse ta ganin zata ballo masa ruwa ƙila likita ya bata lbr har jininta aka saka mashi, yaja hannun mahaifiyarsa yana faɗin " Umma zo muje bana son wannan asibitin". Galadima da matarsa suka bi bayan Hajiya maryam domin ta kaisu inda ƴarsu take. Isowar su fadar sarki keda wuya ya faɗa jikinsa tare da fashewa da kuka, abinda bai taba yi ba, sai hankalin kowa ya tashi a gurin musamman iyayen sa, kai tsaye waziri ya bayar da umarnin kowa ya fice daga fada, sarki zai gana da iyalinsa bayan fita kowa ya ɗago shi zuwa jikinsa yana kallon raunin goshinsa, yace " Su waye suka yi maka wannan aikin Modibbo? Yace " Nima ban sani ba, ban san su ba Abba, amma kaje dani wata asibiti acire min jinin wannan yarinyar da aka saka min, duk bana jin kaina a namiji yanzu Meyasa zasu saka min jininta? Cikin rashin fahimta Haj Maryam ta dafa shi tace " wai jinin wa aka sanya maka ba dai na Am'baby ba? Daga sarki har haj Amina suka dube ta cikin rashin fahimta, Modibbo kuwa gyaɗa kansa yayi tare da labarta masu komai bayan fitarsa gidan har zuwa lokacin da aka sanar dashi an saka masa jinita, hankalinsu ya kwanta da jin bayaninsa musamman mahaifiyarsa, taji yarinyar ta ƙara kwanta mata a rai bata san dalili ba, sarki kuwa kallonsa yayi yana faɗin " Am'baby ai ƴar uwarka ce kuma ƙanwarka, abinda yayi Galadima shi yayi ni banga abin ƙyanƙyami ba modibbo, tare muka yi ƙuruciya da mahaifinta, kusan gida ɗaya muka yi rayuwa dashi, tana da asali mai kyau, menene aibunta saboda ta taimake ka, banda zuwanta gurin da yanzu wani zancen ake ba wannan ba, idan da niyar kashe ka suka zo fa, ta kaika asibiti ta bayar da jininta an saka maka yanzu tana can kwance a asibiti kai kuma ka sami lafia, ta bayar da rayuwarta saboda ta ceci taka rayuwar, lallai Am'baby ta cancanci a yaba mata kuma ta cancanci Kyauta mai girma da tsada.
Duk wannan bayanan basu sanyaya zuciyarsa ba illah ƙara fushinsa ganin Mahaifinsa ma ya goyi bayan abinda yarinyar tayi, ya zai rabu da wannan jinin dake gudana a jikinsa, taya zai rabasa da jikinsa?

Ku shigo cikin daular mu domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku,

MASARAUTA tare da alƙalamin FATYMA XARAH

FATY ~ISLAM daga alƙalamin UMMI A'ISHA

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu ɗaya kacal, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.
[10/11, 7:31 PM] Fertymerh: (TWE)

©️Fertymerh Xarah💞

🛕 *MASARAUTA*🏤

11
Chapter 10 · 0% Book details