Sashe 2
Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Menene cikakken sunan yarinyar da ta bata" ɗaya daga cikin ƴan sanda ya tambaya yana kallon matar, tace " Zaynab Bello Aji" yayi rubutu kaɗan yana faɗin " tun yaushe kika ce ta bata? Tace " yau kimanin sati ɗaya kenan bamu sakata a idanuwan mu ba" yace " kunyi report a police station duk tsawon kwanakin nan? Ta girgiza kanta tana share ƙwallah tace " muma bamu da labarin batan ta sai shekaranjiya da wannan ƙawarta tazo neman ta acewar kwana biyu babu labarinta a school shine tazo neman ta gida" yace " yarinyar ki ta bata sati ɗaya baki da labari kina mahaifiyarta? Ta gyaɗa kai tana kallon mijinta cikin hawaye, dattijon yayi gyaran murya kaɗan yana fuskantar ɗan sandan yace " ba laifin mu bane ba kuma sakaci muka yi ba, school muka kai yarinya karatu ashe tana fita badaƙala bamu da labari ko masaniya akan wani abu da take aikatawa makaranta, duk sanda zamu kira domin jin lafiyarta bama jin wata matsala a tare da ita illah tana nuna mana karatu yayi mata yawa bata son damuwa a waya, last call da suka yi da mahaifiyarta ta tabbatar mata da exam zata rubuta ta bata 2 days kada ta neme ta saboda ta maida hankali sosai a karatun da take, dalilin daya sa kwana biyu bamu kira muka ji lafiyarta ba kenan sai shekaranjiya wannan ƙawarta tazo neman ta acewar bata school" D.P.O ya juya yana kallon wacce aka kira da ƙawar Zaynab yace " ya sunan ki? Cikin rawar murya tace " Ruhayma Taj" yace " ya kike da wacce ake zargin batan ta" tace " she is my friend, i mean close friend ɗakin mu ɗaya a hostel amma not the same department" yace " tun yaushe rabon ki da zaynab" tace " since on wednesday, tace min zata je gida mamanta ba lafiya wai kada na neme ta just 2 days kawai zatayi ta dawo? Yace " faɗa min gaskiyar abinda kika sani game da halin zaynab, bayan ke akwai wasu ƙawaye da take zama dasu da basa jin magana? Ta gyaɗa kai a hankali tana kallon iyayen zaynab a faƙaice tace " dama dama zeebu bata jin magana, tana bin wasu a department ɗin su da suke zuwa club suna shaye shaye, several times nasha yi mata faɗa harda gargaɗin zan sanarda iyayen ta ba karatu take yi ba shashanci da friends sai take gayamin a gida ma an san tana zuwa party da friends kuma her mom knows tana shaye shaye" Hajiya Hauwa ta zare ido cikin mamaki da nuna kanta tace " ni...,sam ba gaskiya bane ƴata bata shaye shaye ban taba kamata da wani abu na maye ba ko akasin sa" cikin tsoro Ruhayma tace " Allah mom tana yi, akwai evidence a school muje a duba ɗakin mu cikin kayanta duk zaa gani, and aje a bincika school activities ɗinta duk zaa samu bata attending musamman lectures she is always absent, ni da nake tare da ita ake yawan zo min da complain akan nayi mata magana zamu zauna nayi ta mata nasiha da magiya amma bazata ji ba, kuma a ranar da ta fita ina tunanin ƙawayen ta tabi suka je wani guri amma tace kece baki da lfy zata je ta duba ki" Hajiya Hauwa tace " innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yaushe zaynab ta zama haka, dan Allah d.p.o a taimaka a nemo mana ita, itace kawai muke da a duniyar nan bamu da wasu yara bayan ita" shiru Alhaji Bello Aji yayi cikin takaici da mamakin wai ƴar cikinsa daya nunawa so da gata ce ke wannan aika aikar a boye basu da labari. D.p.o yayi gyaran murya kaɗan yace bani number ɗaya daga cikin abokan harƙallah ɗinta, shiru Ruhayma tayi tana nazarin kafin ta tuna number Deejah ta bada, aka kira wayar tana ringing baa ɗaga ba, kusan sau uku kafin a ɗaga yayi gyaran murya tare da sanarda ita ko waye shi, nan da nan tasha jinin jikinta duk da bata ganinsa, yace " ki gayamin gaskiyar abinda zan tambaye ki idan kika min ƙarya ko kika boye min zanzo na kama ki kuma na rufe ki a cell ba beli" ta gyaɗa kai kamar yana ganin ta yace " Ina Zaynab Bello Aji? Tayi jim cikin fargaba kafin tace " sir bansan inda take ba wallahi da gaske nake ma" yace " ranar wednesday kun fita daga school tare? Tace " eh" yace " ina kuka je" tace " dama birthday party ɗin wani friend ɗin mune muka je tun acan muka rabu da ita ban ƙara ganin ta ba har ynzu" yace " kuka rabu kamar ya, acan kika barta bayan kunje tare? Tace " aa i mean ana tsaka da bikin naga sun fita da wani ya riƙa hannunta, i try to stop her sai ta nuna min baxata jima ba yanzu zata dawo, bayan gama bikin bata dawo ba nayi ƙoƙarin kiran wayarta not reachable, sai nayi tsammanin ko ta dawo hostel ko da na dawo na tambayi one of her friend Ruhayma ko xeebu is back sai take cemin ai tace zata je gida duba mamanta ba lfy, sai ban ƙara nemanta ba" yace " kinsan yaron da suka fita tare? Tace " noo ranar na soma ganinsa" yace " amma idan kin ganshi zaki iya gane sa" tace " not sure hankalina baa kansa yake ba a lokacin kuma bana tunanin something bad will happen" yace " to zaynab ta bata yanzu sati ɗaya yau tun ranar da kuka fita ba labarin ta, gobe zaki zo nan ofishinmu zan tura maki address kizo ki amsa wasu tambayoyi" tace "innalillahi, wallahi ni bansan komai akan batanta ba dan Allah kada a rufe ni iya gaskiyar abinda na sani na faɗa" yace karki damu tambayoyi kawai zaki amsa idan baki zo da kanki ba zan tura yara gobe su zo dake" ya tsinke wayar yana kallon iyayen zaynab da nayi jugum cikin mamaki yace " kunji, sauran bayani sai zuwa gobe insha Allah and ku cigaba da trying number ɗinta ko Allah zai saka a dace, ko kuma kiran friends ɗinta duk a bincika idan bataje gurin su ba mu kuma zamuyi iya ƙoƙarin mu na dubata a gari da asibiti ko zaa dace. Alhaji Bello Aji yayi godia suka fice duk jikinsu a sanyaye jin babu shaida ta ƙwarai daga ƴarsu, ƴar da gwargwado suna bakin ƙoƙarinsu na ganin sun bata tarbiya, Ruhayma tace " nima zan bincika friends ɗinta dana sani a hostel ko da wanda yaji labarinta" Hajiya Hauwa tace " amma Ruhayma kinsan da wannan haali na zaynab kika boye bakiyi ƙoƙarin sanarda mu domin mu ɗauki mataki ba" tace " ta faɗa cewa duk kunsan abinda take aikatawa kona faɗa babu abinda zaku iya yi mata" Alhaji Bello ya girgiza kansa cikin takaici yace " bamu da masaniya akan komai da take aikatawa, Allah ya kyauta ya bayyanata tukunna" duk suka amsa da amin.
[10/3, 7:13 PM] Fertymerh: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt
🛕 *MASARAUTA*🏤
©️Fertymerh Xarah💞
3
ASALIN LABARI
Jos
[10/3, 7:13 PM] Fertymerh: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt
🛕 *MASARAUTA*🏤
©️Fertymerh Xarah💞
3
ASALIN LABARI
Jos