← Book details Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 17

Sashe 13

Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu ɗaya kacal, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.
[10/15, 8:45 PM] Fertymerh: (TWE)

©️Fertymerh Xarah💞

🛕 *MASARAUTA*🏤

13

ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.

NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...
LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...

A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:

- HAIR SALOON
-HENNA
-SPA
-DUKKAN
-PEDICURE
-MANICURE
-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI DOMINSU SUMA
-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA😊
- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...

IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....

AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY 💅💯

Address 👇👇:
KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA
TEL:08133379628.

Ko da Hamida ta sami lbr rungume mahaifiyarta tayi cikin tsantsar farinciki tace " Mummy da gaske, da gaske zan auri modibbo, Mummy kada ki tasheni daga wannan barcin da nake har sai an ɗaura auren". Hajiya kilishi ta shafa fuskarta cikin murmushi da tana faɗin " an gayamaki ni ɗin ta wasa ce, babu wani abu a duniyar nan da zaku nema na kasa yi maku shi keda yayan ki yaqub, farincikin ku shine nawa, na cika maki burin ki ina so ki ɗaukar min wani alƙawari Hamida". ta sumbaci mahaifiyar tare da rungume hannayenta a qirjinta cikin rawar jiki tace " Mummy menene shi, nayi maki alqawari zan maki kamar yanda kika min a yau". Hajiya kilishi ta numfasa tare da faɗin "bazaki juyamin baya saboda son da kike masa ba, kuma duk abinda na saka ki zakiyi batare da musu ba" " Mummy wlhy koma menene zan yi indai zan zauna dashi". Hajiya kilishi tace " idan kika sabawa umarni na hanyar da nabi na ɗaura auren ita zan bi na warware, kin sanni idan kika min ganganci akan aikina zaki ga cikawa". " Allah Mummy ko menene zan maki, ko ƙafafun shi zaki cire bazan hana ba idan har zan kasance tare da shi, ina son sa da gaske, ina yawan mafarkinsa ashe zai zamo mijina, mummy wlhy ji nake yau kamar bani bace, ji nake kamar wata sarauniyar england, mummy bansan dame zan saka maki ba akan wannan ƙoƙarin da kika min, mummy yanzu ƙawayena zasu ƙara darajani saboda sun san irin mijin da nake aure shine suke so, yanzu martabata zata dawo a gidannan, zaa riƙa girmama ni kasancewata matar modibbo tilo ɗaya a gurin mai martaba, mum....ke dallah rufamin baki haka, ashe haka kike da surutu, wait wai baki da labari cewa ku biyu zai haɗa ya aura kike ta wannan zubar? tayi shiru tana kallonta baki sake ta buɗe kunnuwanta sosai, kilishi ta cigaba da faɗin " eh tabbas auren sa da Am'baby yana nan baa fasa ba, bazai fasa ba kin sani Sarki baya magana biyu, da ƙyar na shawo kansa ya yarda da auren ki, amma dole zamu bi duk wata hanya mu kau da Am'baby daga modibbo ko da kuwa bayan auren kune". Hamida tayi shiru tana tunanin yarinyar kaɗan, " Am'baby ba wata fara bace can sosai domin ta fita hasken fata sosai, sai dai akwai yalwar gashi a tare da ita wanda akan goshinta ma zaka gane hakan, yanda ƙananan gashi suka kwanta a goshi da gefen fuskarta, jagirarta cike take da gashi, tana da manya idanu nima ina dasu, bakinta dai dai fuskarta ƙarami sai ɗan neman tsiwa baya shiru ko kaɗan, bata taba haɗuwa da yarinyar bata ganta tana surutu ba, jikinta dai dai shekurunta bata da jiki sosai kamar ni, yarinyar tana da shiga rai ga duk wanda ya zauna da ita saboda komai a natse take yinsa babu girman kai kamar ba jinin sarauta ba, sabanin ni duk inda na shiga sai kowa yasan daga jinin sarauta na fito ko baa gane ba nakan faɗa da bakina idan naga ana son raina ajina, tana d.....kilishi ta katse mata tunani ta hanyar dafa kafaɗarta " me kike tunani haka tun ɗaxu ina ta magana" tayi ajiyar zuciya kaɗan tana faɗin " kishiyata nake tunani, ina so naga dame ta fini wanda zai saka ta iya kwace min miji" babu abinda ta fiki da shi, idan ma akwai duka zamu kawar dashi, kada ki ɗorawa kanki tunanin banza akan ƙanƙanuwar yarinya, shekara biyu kika bata a duniya kina 18yrs a yanxu, kinsan abubuwa da yawa fiye da ita, zamu bi duk wata hanyar da bazamu taba bari su zauna a inuwa ɗaya ba balle har yaji yana son kasancewa da ita, dole ke kaɗai zai so". Hamida ta rungumeta cikin farinciki " ina son ki mamana, you're the best👍🏻 ta jinjina mata.
*
Alhaji ashe Modibbo har da ƴar wajen kilishi zai aura, yanzu ake sanar dani hakan. " hakane nima ɗazu sarki yake min bayani komai daga farko, amma ya tabbatar min da Am'baby itace zata kasance uwar gida a gun Modibbo kuma zai shige mata gaba akan komai.....ta katse sa " Alhaji wlhy ina tsoro, a yanzu kam ina tsoron haɗa ƴata kishi da ƴar wajen kilishi, bazan boye ma ba kasan wacece kilishi babu abinda bazata iya aikatawa ba." yace " hakane muyi masu fatan alheri, muyi addu'a Allah ya kare mana ƴar mu insha Allah babu abinda zata iya mata, Am'baby a wannan lokacin tana zaune tana sauraren su, ta turawa frnds ɗinta cewa mai mata zaa aura mata, harda yin status cos tana ɗaukar abun a wasa ita, sosai suka soma raha da qawayenta wasu suka nemi sanin mijin musamman qawayenta maza, ta soma tunanin inda zata sami hoton shi, ta tuna amarya Hajiya Maryam, tashi ta fice daga gidan dama kwana biyu da sallamarta daga asibiti.
*
Duk jawabin da sarki yake babu abinda ya zauna masa a kunne, shi tun lokacin da yaji Sarki ya sanar dashi auren Am'baby ya kuma sanar da shi auren Hamida gabaki ɗaya jinsa ya ɗauke, banda kallon sarki da yake babu abinda yake fahimta illah yaga bakin sarki yana motsi alamar magana yake har wannan lokacin.
"Muhammad kana ji kuwa? Shiru bai amsa ba hakan ya tabbatarwa da sarki baya cikin hankalinsa da ido yayiwa Mahaifiyar sa alama ta duba shi, hannu ta kai kafaɗarsa tana kiran sunan sa, firgigit ya dube ta kafin ya maida kallonsa ga mai martaba tare da sunkuyar da kansa ƙasa, yace " kayi haƙuri modibbo, na aikata maka ba dai dai ba, na ɗora maka nauyi mai girma wanda wataƙila bazaka iya ba, amma babu yanda zan iya da kilishi, kayi min biyayya". Yayi shiru har lokacin bashi da abin faɗa, shi ya kasa gane kan mahaifinsa ya daina son sa ne yake masa wannan hukuncin kome? Mata biyu a lokaci ɗaya kuma duka babu zabin sa, ya zai yi dasu idan ya sami wacce yake so? taya ma zai iya rayuwa da matan da baya so har ake tunanin ya haɗa shimfiɗa dasu? " meke damun ka modibbo? Mahaifiyar sa tayi mgnr cikin damuwa ganin tsantsar damuwar da yake ciki, ta juya ga sarki idanunta sun kawo ƙwallah tace " ranka shi daɗe kayi haƙuri zanyi magana a wannan karon, idan aura masa Am'baby dai dai ne meyasa sai an haɗa da Hamida, Meyasa dole sai mace biyu zaa aura masa a lokaci ɗaya kuma duka ba zabin sa ba, idan akwai matsala a fasa auren duka amma dube shi yanxu, tun shekaranjiya daya sami lbr aurensa da Am'baby bashi da nutsuwa yanxu kuma kana mgnr wata Hamida, dan Allah a duba masa amma bazai iya ba". tayi mgnr kamar zatayi kuka, sarki ya numfasa kaɗan shima zuciyarsa ba daɗi yace " babu yanda zanyi dole haka zaayi, bazan kunyata a idon jama'a ta ba, kowa a yanxu ya san da mgnr auren sa da Am'baby sannan kilishi kinsan wacece ita koda bana so dole na amince saboda zata iya ɗaukar duk wani mataki akan shi da Am'baby, dana rasa shi ta wata hanyar gwara a ɗaura auren da ƴarta a zauna lfy, uwa ɗaya uba ɗaya babu abinda zan iya mata a yanzu amma akwai lokaci, shiyasa na kiraki da ɗanki na nemi wannan alfarmar. Duk suka yi shiru, mata biyu? ya zai kula da mata biyu, mace ɗaya ma ya zai iya da ita balle mata biyu, wata zuciyar ta amsa da kai namiji ne, mace huɗu zaka iya kula da ita balle mace biyu, kayi biyayya ga mahaifin ka, matan kuma ka nemi wata hanyar rabuwa dasu ta yanda bazaa taba ganin laifin ka ba sai kaje ka auro wacce kake so, ya yarda da shawarar zuciyarsa ya amsawa mai martaba da cewa ya aminta, yana barin fadar kai tsaye ɗakin Amarya ya nufa ya bata lbrn abinda Sarki yake shirin yi masa, gab da zai shiga falon yaji muryarta tana faɗin "Ni bana sonsa, Ina son namiji mai ƙarfi ba irin sa ba, idan na aure sa ni zan riƙa tare masa faɗa kenan?

Ku shigo cikin daular mu domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku,

MASARAUTA tare da alƙalamin FATYMA XARAH

FATY ~ISLAM daga alƙalamin UMMI A'ISHA
Chapter 13 · 0% Book details