← Book details Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 17

Sashe 15

Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

©️Fertymerh Xarah💞

🛕 *MASARAUTA*🏤

15

Mahaifiyar Jaudah sosai tayi farinciki da lbrn da Jaudah ta bata akan mahaifiyar modibbo, tun daga tsaraba ta gane tana matuƙar son ƴarta, lallai Am'baby bazata wahala a gurinta ba zata sami gata, yanzu matsalar su Hajiya kilishi ce kuma insha Allah baxata taba cin nasara akan ƴarsu ba. Tun daga lokacin duk ranar da Am'baby taje gurin Amarya sai taje gurin Hajiya, basu taba haɗuwa da modibbo ba, idan Hajiya ta sanar mashi Jaudah tazo ya kanyi mamaki me take zuwa yi wurin mahaifiyarsa, kullum addu'ar sa ko sau ɗaya kada Allah ya haɗa hanyarsu, baya son ganin su ita da Hamida. Cikin lokaci ƙanƙani aka soma shirye shiryen bikinsu, ƴan uwa da abokai nesa dana kusa sun soma hallarta MASARAUTA domin bikin Modibbo, Hamida da mahaifiyarta ma baa barsu baya ba gurin nasu shirye shiryen, duk abinda uwa zatayi na gyara mace babu abinda Kilishi bata mata ba ko nace babu inda bata kai Hamida domin a gyarata ba sai idaan bata ji lbrn gurin ba, Amaren masha Allah ba laifi kowacce da nata kyawun, duk wanda ya gansu sai yace Tubarakallah, ko sau ɗaya bai taba haɗuwa da kowacce daga cikin su tun lokacin da aka sanar dashi auren su, dalailin haka Sarki yayi kiransa kuma ya bashi Umarni kafin a fara bikin dole yaje ga kowacce mace su fahimci juna idan har yana son farincikin sa, tun da sarki yayi mgnr yake durƙushe kansa a ƙasa cikin wani yanayi, ya kasa motsawa ballantana ya amsa masa kamar yanda ya bashi Umarni, Sarki ya ƙara nanata masa maganar karo na biyu da ƙyar ya ɗago yana kallon Mahaifinsa idanunsa jawur, duk zafin da yake ji a zuciyarsa sai da yaji wani iri sakamakon haɗa ido da yayi da sarki, da ƙyar ya buɗe baaki yace " kayi haƙuri zanje yau ko gobe insha Allah" Sarki yace " Allah shi maka albarka, kamar yanda kake bin Umarni na akan abinda baka so Allah ya dube ka da idon Rahma, kayi haƙuri kuma ka riƙe amana, nayi maka alƙawari duk wacce kagani kana so daga baya ko ƴar gidan waye zan aura maka ko da kwana ɗaya ne da wannan auren, nima zan faranta maka kamar yanda ka faranta min". Yaji wani sanyi a ransa, yaji wani ƙwarin gwiwa da zai saka yaje neman macen da yake so ko baƙin ciki zai saka waɗannan su kasa zama dashi su tafi su barshi da matar shi, yace "Godiya nake Abba". Sarki ya cigaba da faɗin bayan bikin zan tafi india jikin har yanzu babu sauqi, dauriya nake yi ni kaɗai nasan me nake ji a jikina" cikin damuwa modibbo ya dube shi yace " Abba tare zamu je, bazaka je ka barni ba, zan duba ƙwararren likita a india muyi mgn dashi online kafin zuwan mu tunda nan gida Nigeria sun kasa gano ciwon wataƙila acan zamu dace" Sarki yayi jim kaɗan kafin yace " kasan ciwon ajali wani lokacin baa cika gane sa ba, shiyasa nake tunanin shine ya kamani" "Abba ka daina wannan mgnr, mutum nawa ne yayi ciwo kafin kai ya warke kuma baa gano matsalar anan ba sai a wata ƙasa, ni ka daina min haka bana so" yayi mgnr cikin sanyin jiki da jin kalaman mahaifinsa, Sarki ya shafa kansa yana faɗin " Na bari Muhammad amma kasan ba dai dai bane ka bar matan ka guda biyu ka bini zuwa india, sabon aure ne da kai fa" Modibbo yaji wani bacin rai na neman lullube ahi, yace " ni kuma dai dai ne na bar mahaifina yaje wata uwa duniya neman magani ni ina kwance a gida, haba Abba, a duniyar nan bayan kai da Umma waye nake dashi da zan iya bashi lokacina fiye daku? Maza nawa suke tafiya neman ilimi wata ƙasa su bar matan su ballantana ni lafiyarka zanje nema maka, gaskiya tare zamuje akan wannan mgnr kayi haƙuri bazanyi biyayya gare ta ba, ƙafana ƙafarka". Murmushi sarki yayi yana faɗin " Shikenan Angon Jaudah da Hamida". duk da tsokana ce sarki yayi masa sai da yaji wani iri tare da faɗuwar gaba, la shakka ko sunan su baya so ana ambata a kusa dashi da sarki yasan da zafin da yake ji a zuciya game dasu da bai gwada ambatonsu a gaban saba.
Dariya sosai Sadiq yake yana taba hannayensa, yace " wallahi mamaki kake bani Prince, Amma time will tell, ba lafiyayyen namiji irin ka zaa aurawa mace biyu ba yace baya so, ni Sarki ya burgeni ina tunanin ya karanceka sosai ne ya haɗa ka da mata biyu. Hmmm ya tabe baki kaɗan kafin ya ɗago da kallonsa ga waya yana kallon sa yace " nazo ina gayama damuwana ka zauna kana dariya kana min wani shirme, mafita nake nema, ko zaka je a matsayin ni gare su? Sadiq yayi caraf yace " idan an ɗaura auren nine zanje ɗakin su? Modibbo yace " idan kana ra'ayi suna raayin ka me zai hana? Wannan karon a harzuƙe sadiq yayi magana " wai meyasa kake hakane Muhammad, idan baka son su kaje ka gayawa Sarki kada ka cutar da yaran mutane Allah ya tambaye ka haqqin su, taya zaka dubeni kace idan ina raayi da matan ka naje gare su, ka kuwa san menene aure? Kai tsaye modibbo yace " na sani mana, saboda nasani aka bani auren mace biyu a lokaci ɗaya, kaine zan tambaya kasan zafin auren macen da baka so, mace ba ɗaya ba har guda biyu kuma babu zabin ka acikin su, bansan so ba saboda ban taba son kowacce mace ba amma a yau nasan zafin ƙi .....Sadiq ya katsesa " Dan Allah sanar dani halayen matan nan, gayamin dalili daya sa baka son su" kai tsaye yace " haka kawai zuciyana bata son su bata raayin su" yace " ka sanar da sarki gaskiya kada ka cuce su". Yace " sarki ya fika sanin bana son su, yasan biyayya ce kawai nake masa, kuma a hakan ya yarda na aure su, ya kake so nayi" sadiq yace " kayi hakuri kayi biyayya, watarana zaka so su, kuma koda baka so su ba zaka haɗu da wacce kake so ka aura shikenan, amma kaji tsoron Allah akan haƙƙin su kuma kaji tsoron Allah kada ka cutar dasu." kallon sa modibbo yayi wannan karon cikin mamaki " wai tun ɗaxu kake ta cewa naji tsoron Allah, ni macuci ne, ni azzalumi ne, naa taba cutar da wani ne? " Easy ba haka nake nufi ba, kada kaje baka zama dasu a gida kana debe masu kewa, baka fita dasu shaƙatawa ko yin siyayya da sauran su, ko a friends ɗin mu ai kafimu sauƙin kai, yanzu mu bar mgnr tashi ka shirya ka tafi kaga almost to 9pm kuma dukkansu ka aika masu zaka je, ina tunanin kowacce ta gama shirya zuwan ka". shiru yayi cikin tunanin yanda zaije ya dube su, bai taba zuwa zance ba kuma bai taba raka ko ɗaya daga cikin friends ɗinsa ba, bai san yanda ake zance ba ta ina ma zai fara?.
Hajiya kilishi da Hamida tun da wata Baiwa da aka aiko ta sanar da zuwan Modibbo farinciki ya lullube su, sai faman shirye shirye suke, abinci yafi kala biyar da suka girka masa, ga abubuwan sha baa magana kuma kowane babu wanda baa saka masa magani aciki ba, duk dan saboda Hamida ta mallake shi ita kaɗai, kwalliya da ado da tasha kamar ranar aka ɗaura auren su, sai ƙamshi ke tashi a lungu da saqo na gidan, turaren da aka haɗa da magani shima saboda aja raayinsa sosai akan ta, kusan ƙarfe goma babu alamar zuwan sa har sun soma gajiya da jiransa, kamar daga sama suka ji knocking a ƙofar falon su, wani tsalle Hamida tayi ta rungume mahaifiyarta, da gudu ta bar falon tayi falo yayin da Hajiya kilishi ta yiwa ɗaya daga cikin Baiwar gidan da tayi sauri ta ƙara gyara falon kafin shigowar su.
[10/18, 9:21 PM] Fertymerh: (TWE)

©️Fertymerh Xarah💞

🛕 *MASARAUTA*🏤

16

ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.

NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...
LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...

A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:

- HAIR SALOON
-HENNA
-SPA
-DUKKAN
-PEDICURE
-MANICURE
-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI DOMINSU SUMA
-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA😊
- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...

IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....

AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY 💅💯

Address 👇👇:
KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA
TEL:08133379628.
Chapter 15 · 0% Book details