← Book details Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 17

Sashe 7

Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shiru ya biyo na ɗan wani lokaci kafin Hajiya kilishi ta dubi sarki cikin girmamawa saboda kasancewar sa sarki ba dan ya girmeta a shekaru ba, tace " nazo da magana ne mai karfi wacce nake so ka saurare ni da kyau, bani da wani buri a rayuwa yanxu wanda ya wuce naga auren Hamida da Modibbo". Kallonta sarki yayi batare da yayi magana ba, ta cigaba da faɗin " abin farinciki ne a gare ni da kai idan hakan ta kasance saboda su ɗin ƴan uwan jini ne kuma jinin sarauta, zasu so juna su kuma yi haquri da juna sa'annan zumuncin mu zai ninku". Yace " sun faɗa suna son junan su ne? Tace " ko suna so ko basa so, dole ne wannan zumunci ranka shi daɗe" ya girgiza kansa a hankali kafin yace " babu auren dole tsakanin ƴaƴana haka kuma bazan ma ƴaƴanki auren dole ga kowa ba, duk wanda suke so shi zaa aura masu" tace " koda nace dole sai anyi wannan haɗin? Ya dube ta ganin yanda ta ɗaure fuska kamar ba itace ke mgn cikin lallami ba, ya sani sarai kilishi bata da haquri akan duk abinda ta sakawa gaba, yasan halinta da kafiya da naci koda rayukka bazasuyi daɗi ba, yace " amma Hajiya fisabilillah haka kawai ki tsiro da wannan mgn ana zaune qalau, bakya tunanin shiga haqqin yaran da abinda zai biyo baya idan basa ra'ayi? Tace " zaka iya tursasawa yaronka kamar yanda zan turasasawa tawa ƴar, ballantana Hamida tana son sa da bakinta ta gayamin hakan." yace " Idan kuma modibbo yana da wacce yake so fa? dai dai lokacin daya shigo da sallama a bakinsa, ya sami guri kusa da sarki ya zauna kafin ya dube ta cikin girmamawa yace " barka da fitowa Hajiya" fuska a ɗaure ta amsa kafin ta dubi sarki tana qoqarin tashi " ina son wannan haɗin koda bada amincewar su ba, ina son auren Hamida da Modibbo" ya dubeta cikin rashin fahimta " wane Modibbo" tace " inaji duk masarautar nan Modibbo ɗaya muke dashi, kada ka raina min hankali, Alheri nake son ƙullawa a tsakanin kai da ƙanwar ka, Hamida tana son ka da gaske koda kai baka son ta ina so ka koyawa xuciyarka son ta daga yau." cikin tsananin mamaki yace " ko da ina da wacce nake so take sona? Sarki ya dube shi, itama kallon mamaki take masa ta nuna sa da qaramin yatsa tace " kai kake da wacce kake so? Ya gyaɗa kai batare da ya san ko wacece ba, sanin kowa ne babu wacce yake so ko yake kulawa dole zasu yi mamaki. Ta numfasa tana faɗin " wannan zancen banza ne Modibbo, babu wanda bai sanka akan ƙin mace ba, idan da gaske ne wacece ita, ƴar gidan waye? Yayi shiru cikin tunani tare da lumshe idanuwansa, ƴan matan da suke kururuwa akansa yake tunawa wacce zai zaba, duka acikinsu babu wacce ta cika irin quality da yake so agun mace, ya buɗe su a hankali akan kyakyawar fuskar sarki, ya shagwabe fuska kamar zaiyi kuka yace " ranka shi daɗe bana son Hamida, Hamida is not my type, babu wani abu da nake so a tattare da ita ta fannin halitta ko halayya, zan kawo wacce nake so bada jimawa ba abani lokaci" cikin gamsuwa sarki ya jinjina kansa ya riqo hannunsa yace " abinda kake so shi nake so modibbo, babu dole, kaje ka kawo min wacce kake so" cikin tsananin farin ciki ya sumbaci sarki a goshi ya tashi ya fice batare da ya qara kallon fuskar kilishi ba tamkar babu ita a wurin haka yazo ya wuce ta gabanta da ƙasaita, ta dubi sarki rai a bace tace " ni zaka wulaqanta a gaban yaron ka? Yace " babu wulaqanci Hajiya, amma bazan iyawa modibbo dole akan wacce baya so ba....ta katse sa cikin bacin rai " wallahi ko baya so sai ya auri Hamida, baka isa ka hana zumuncin da Allah yake son haɗawa ba, ta fice a fusace, ya bita da kallo cikin tsananin mamakinta. Yana fita falon sarki kai tsaye sashen mahaifiyar sa ya nufa yanayinsa kaɗai ya tabbatar da ba lfy ba, tace " akwai damuwa ne? Ya tabe bakinsa kamar bazai yi mgn ba sai kuma ya shiga bata lbr abibda ya faru yanxu, cikin mamaki tace " wane irin tunani ne haka yazo zuciyar Hajiya har take qoqarin haɗa auren ka da Hamida? Yace " koma menene bazan aure taba Umma, ina da ƴan mata masu kyau da aji babu wacce na kula ballantana wannan ƙwailar saboda ana son raina min da wayo". Cikin kwantar da murya tace " Modibbo lokaci yayi da zaka tsayar da wacce kake so ayi maku aure, idan ba haka ba kasan halin Hajiya kilishi zata iya kome saboda burinta ya cika, ka nemi mata hakan kawai zai saka ta daina mgnr Hamida" yayi shiru cikin tunani tare da lumshe idanuwan sa, ta tsurawa kyakkyawar fuskarsa idanu tana kallonsa, ɗaya bayan ɗaya suke zo masa a zuciya tun daga kan ƴaƴan abokan Sarki da mahaifiyarsa, xuwa waɗanda suka yi karatu tare ƴa'ƴan manyan ƴan kasuwa da siyasa ya kasa hango mace ɗaya wacce ta kwanta a xuciyarsa da zai tsayar a matsayin wacce zai aura, ya buɗe idanunsa a hankali sai acikin na mahaifiyarsa, ya shagwabe fuska a hankali kamar zaiyi kuka yace " Umma na kasa hango...." ta katse shi " kada ka wahalar da zuciyarka wurin tunani Modibbo, ina ji a jikina zaka sami mace mai tarbiya wacce tazo dai dai da ra'ayin ka, kaje ka kwanta ka huta cikin kwana biyu ka barwa Allah zabin sa."

Cikin bacin rai Hajiya Kilishi ke kallon Yaqub da Hamida, tace " a gabansa ya wulaqantani ya nuna farincikin ɗansa yafi nawa, zabin Modibbo shine nashi" cikin bacin rai yaqub yace " Hajiya koma menene kece kika ja, tun farko da kin tashi tsaye kin nuna baki yarda a bashi sarautar nan ba da yanzu a qarqashin ikon mu yake, idan har ke macece bazaa baki sarauta ba ai kina da miji a lokacin sai a bashi, idan ya mutu ai nine magajinsa sai a bani sarautar". Tace " zancen daya jima da wucewa ka daina mayar dashi, muna mgn akan haɗin auren Hamida da Modibbo anan ne zamu cika burin mu akan su, ta hanyar auren su zamu samu takardun gidan MASARAUTA da sauran ƙaddarorin da yake alfahari dasu, idan ya wayi gari bashi da ko ɗaya aciki a lokacin zamu bashi zabi tsakanin Sarauta da Dukiyar sa." yace " wannan zancen naki yana kan hanya, amma me zai hana mu sami modibbo mu ɗan dake shi ta yanda zai samu rauni a qafa ma'ana mu karyashi a qafa ta yanda babu wata mace da zata so shi idan ya nakasa, sai a haɗashi da Hamida cikin sauqi ki nuna ita jinin sace xata iya zama dashi a kowane hali". Cikin farin ciki Hamida ta rungume yayanta kafin ta rungume kilishi tana faɗin " wannan yayi yaya wlhy a raunata shi ta yanda babu wata macen da zata so shi sai ni kaɗai, ta yanda ko bayan auren mu bazai yi tunanin qara auro wata a matsayin matar sa ba." Hajiya kilishi ta girgiza kanta cikin rashin gamsuwa tace " Anya wannan shawara ce.....suka katse ta, " Shawara ce Hajiya" tayi jim kaɗan kafin tace " idan aka gane kaine fa, kasan sarki bazai barmu ba dagani har kai wata qila zai sa a korani daga masarauta." yace " babu ta yanda zasu gane, kinsan duk dare yana fita motsa jiki zamu bi bayansa ne sai ya isa dai dai inda babu mutane kuma babu haske mu aiwatar da nufin mu." tace " Allah yasa a dace ka kiyaye Yaqub bana son wani abu ya same ka zuciyata bazata iya ɗauka ba" yace " Babu abinda zai faru, anjima zamu bi bayansa." Bayan fitarsa Hamida kallon kilishi tayi cikin murmushi tana faɗin " Allah ya tabbatar naga ranar da zan auri modibbo, Hajiya bansan yanda zanyi ba saboda farinciki, ina sonsa da gaske." kilishi ta bata fuska kaɗan " kada ki sakawa zuciyarki cewa zaki zauna dashi har tsawon rayuwar ki, da zarar mun sami abinda muke so daga gare su babu mgnr aure tsakanin ku." tace Hajiya ni dai ko menene kuke so idan kun samu dan Allah ku barni dashi zan iya zama dashi cikin kowane yanayi."

Ku shigo cikin daular mu domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku,

MASARAUTA tare da alƙalamin FATYMA XARAH

FATY ~ISLAM daga alƙalamin UMMI A'ISHA

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu ɗaya kacal, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.
[10/8, 8:00 PM] Fertymerh: (TWE)

©️Fertymerh Xarah💞

🛕 *MASARAUTA*🏤

8
Chapter 7 · 0% Book details