← Book details Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 17

Sashe 1

Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

[10/18, 9:15 PM] Fertymerh: ﺑِﺴْـــــــﻢِﷲِﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦِﺍلرَّﺣِﻴﻢ

(TWE)

©️Fertymerh Xarah💞

🛕 *MASARAUTA*🏤

~2024~

1

Tun da ya fito shago yake ta zuba ido yana kallon ta inda zata bullo, ya san a daidai irin wannan lokacin take zuwa karban bread wurin sa, bashi da kuɗi masu yawa a hannu kasancewar yanzu ba wani ciniki yake samu a shagon ɗinkin nasa ba, kayan maza yake ɗinkawa dasu yake samu yana rufawa kansa asiri dana mahaifiyarsa da yake kula da ita, da kuɗin yake biyan hayar shago idan lokaci yayi bashi da wata sana'a daya dogara da ita da zai nemi kuɗi bayan wannan, ana haka kwatsam sai ga wata mahaukaciya da ciki ta bayyana a layin nasu a galabaice da alamun yunwa sosai a tare da ita, duk inda taje babu mai kulata sai ma hantarar ta da ake yi, very young girl da lalurar hauka ga kuma ciki dole a tausaya mata, sanda tazo shagonsa xuciyarsa ta kwaɗaita masa da son taimakawa qaramar yarinya, abincinsa shinkafa da mai da yaji ya ɗauko ya bata ta yatsina fuska tare da girgiza kai bata so, abin ya bashi mamaki kuma sai hannu take kai baki alamar yunwa, meyasa bazata ci ba ya tambayi kansa cikin mamaki, xuciyarsa ta raya masa kenan suma mahaukata idan suna da juna biyu yana saka su ƙyanƙyamin abinci, ya jinjina kansa ya rasa abinda zai bata wanda take so, cikin sa'a sai ga mai bread yazo wucewa ya gwada siya mata aikuwa da sauri ta ƙarba ta soma ci, ya siya mata pure water ya bata, nan ta zauna tana ci da ruwa duk wanda zai bi yana kallonsu, tana gama ci ta tashi ta bar gurin bata ƙara waiwayarsa ba, tun daga ranar kullum a irin wannan lokacin take xuwa ya siya mata bread taci tayi tafiyarta, bai santa ba bai san daga inda ta fito ba kuma baisan a ina take zama ba. Haka yau yake ta zuba idanuwa yana jiran zuwan ta shiru, duk sai ya shiga damuwa, ga bread a gefe da ya siya mata tun ɗazu bata zo ta karba ba, ya tashi daga inda yake ɗinkin sa ya fito shago yana dube dube ko Allah zai sa ya tsinkayo ta, babu alamar ta, baisan dalilinsa na damuwa ba, ko dai ta haihu a wani guri ne ya tambayi kansa, sai kuma ya girgiza kansa nooo wannan cikin bai isa a haifesa ba, ya dubi abokan aikinsa dake cikin shagon yana faɗin " Salisu zan ɗan zagaya kaɗan koda an zo nemana pls" salisu ya jinjina kai babu bata lokaci ya zira slippers ɗinsa ya fito da hanzari cikin shagon ya soma tafiya yana waiwaye waiwaye batare da yasan ta inda zai soma ganin ta ba, meyasa ma ya damu da ita haka ya tambayi kansa, wata zuciyar tace tsananin tausayin tane, sati ɗaya kacal daya soma ganinta, har ya gama zagaye unguwar babu alamar ta a sanyaye ya juyo ya dawo, ga mamakinsa tsinkayota yayi zaune a bakin shago cikin rana, wata ajiyar zuciya yayi ya nufe ta da sauri yana kallonta cikin mamaki, tana ganinsa ta nufe sa bazata manta fuskarsa ba a duk inda ta shiga, shi kaɗai ne wanda ke taimakamata yake bata abinci a duk sanda ta buƙata, shi kaɗai ne wanda baya hantarar ta ko ƙyamarta a duk sanda ta doso inda yake, shi kaɗai take gani taji sanyi a ranta kamar ƴa da uba, ƙaton bread ta miƙa masa tana kallonsa, ya dubi bread ɗin kafin ya dube ta cikin mamakin inda ta samo bread ɗin yace " ina kika shiga nake ta neman ki, kuma a ina kika samu wannan bread ɗin? tayi shiru batare da tayi magana ba, shi har yau bai taba jin muryarta ba bai sani ba ma ko tana ji tana magana, duk hanyar daya bi na son sanin inda ta sami bread ɗin ya kasa samun amsa sai ya ƙarba kamar yanda ta dage da bashi, yace " nagode, amma ni ina da abinci idan na karba me zaki ci" nan ma tayi shiru tana shafa cikinta, ya dubi cikin ya girgiza kansa cikin takaicin da baisan dalilinsa ba, ya shiga shago ya ɗauko bread daya ajiye mata da lemu ya kawo mata ta karba tana ƙoƙarin juyawa yace " ko sunan kine ki gayamin mana" ta juyo tana kallonsa shima ita yake kallo, dattin dake jikinta da fuskarta idan mai ƙyanƙyamine kai bazaka jure kallonta ko tsayuwa kusa da itaba har lokacin batayi magana ba ta juya ta bar gurin, ya sauke numfashi a hankali kafin ya maida dubansa ga bread ɗin da ta bashi, ko a ina ta samu kuma har tasan ta kawo masa? ya tabe baki yana juya bread ɗin ya nufi shago yana faɗin kuɗina gobe sun huta domin ajiye maki kayanki zanyi gobe idan kin dawo na baki. Salisu yace " wannan mahaukaciyar me kake ji a tsayuwa da ita? Kallonsa Kamal yayi kafin yace " laifine idan musulmi ya taimaki ɗan uwansa musulmi, musamman ma irin wannan mai cikin lalura? Salisu ya girgiza kansa yana faɗin " ba laifi bane amma ka nace da yawa, mahaukaciya ce kuma kana ganin abinda ke jikinta wataƙila bata gari suka lalata mata rayuwa suka mata haka saboda rashin tausayi da imani irin na mutanen mu, kai kuma kazo kana taimakon ta wanda dalilin haka zai iya saka ka a wata matsala azo ana ganin ka da ita a soma zargin ka kasan duniyar nan taimako a yanzu matsala yake saka mutum" Kamal yaja numfashi kaɗan yana jinjina kansa yasan gaskiya salisu yake faɗa masa amma bazai iya ƙin taimakawa yarinyar ba, yace " nagode" ya zauna ya cigaba da ɗinkin sa. Da yamma ya bar shagon zuwa gida, gidansu ba wani mai kyau bane can ƙaramin gida ne mai ɗauke da ɗaki biyu kacal nashi dana mahaifiyarsa, sai toilet da kitchen, rufin asirin su gidan mallakinsu ne ba haya suke yi ba, yayi sallama ya shiga gidan dattijuwar tana zaune zaman jiran sa, ta amsa tana faɗin " lafiya yau ka jima baka dawo da wuri ba? Ya zauna daidai ƙafafunta yana faɗin " wallahi Umma yau aiki ne yayi min yawa" tace " Allah ya taimaka, dama kai nake jira ka siyo gawayi a ɗora girki babu ko sisi hannuna shiyasa ban aika yaro ya siyo ba" ya saka hannu a aljihunsa ya ciro wata ɗari biyu yana faɗin " ita kaɗai ta rage min duk aikin da nayi yau babu wanda ya biya tukunna, ina sa rai zuwa gobe idan sun zo karba na sami wani abu sai na ƙaro mana shinkafa" tace " Allah shi albarka ya ƙara rufa mana asiri, ƙoƙarta kaje ka siyo ko bani nan naje na siyo da kaina da alama a gajiye kake, kaje ka watsa ruwa ka huta" ya tashi yana faɗin " haba umma, sai na zauna ke kifita siyen abu? Tace to menene aciki, bani ce nace zanje na siya ba" ya girgiza kansa bayan ya tashi ya saka takalminsa ya fita, bai jima ba ya dawo da ledar gawayi a hannunsa ya ajiye a dai dai lokacin da tayi sallama ta shigo, duk suka amsa suna kallonta, murmushi tayi bayan sun haɗa ido kana ta juya tana gaida umma, umma tace " kece tafe da yammacin nan bakya gajiya da zirga zirga? Tace " umma nazo ne nayi maki girki naji kince idan ya dawo zaa yi girki" tace " a'a ki huta haka, kin gyara gida kinyi wanke wanke ai ya isa haka, ki bar girkin zanyi da kaina, a kunyace cikin murmushi tace " Allah umma zan yi, kibari tunda har nadawo kawai kisa min albarka" cikin farin ciki umma tace " Allah shi maku albarka ya nuna min auren ku lafiya" a kunyace taja mayafi ta rufe fuskarta, kamal kuwa murmushi kawai yayi ya shiga toilet. Jiddah ta soma ƙoƙarin ɗora girkin umma na tayata, sai hira suke cikin kulawa, bayan ya fito wankan ɗakin sa ya nufa bai jima sosai aciki ba ya fito dai dai inda umma take zaune ya zauna yana faɗin " Ummana sai kika sakar mata girkin idan girkin baiyi daɗi ba, muka kasa ci fa" wani kallo Jiddah tayi masa cikin shauqi kafin ta tunxuro baki, Umma tayi murmushi kaɗan tana faɗin " ba dai girkin Maijiddah ba kasan ko a gidan siyar da abinci bazasu nuna mata iya girki ba" ya numfasa a hankali tare da faɗin " kada kisa kanta yayi girma umma ni dai nasan bazata fi gidan abinci iyawa ba" buɗar bakin jiddah sai cewa tayi "aikuwa yau bazaka ci wannan girkin ba" murmushi kawai yayi ya tashi ya fice daga gidan ganin Magrib ta gabato.

Ku shigo cikin daular mu domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku,

MASARAUTA tare da alƙalamin FATYMA XARAH

FATY ~ISLAM daga alƙalamin UMMI A'ISHA

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu ɗaya kacal, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.
[10/18, 9:15 PM] Fertymerh: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt

(TWE)

🛕 *MASARAUTA*🏤

©️Fertymerh Xarah💞

2
Chapter 1 · 0% Book details