← Book details Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 27

Sashe 6

Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasancewar baffa kowa ya sanshi arugar mutumin kirki ne sam ba ruwansa da shiga harkar wani, sannan kuma shine ke ja musu jam'i ,hakan yasa suke ɗan ganin girma da mutuncinsa, dan haka cikin Turo baki da hura hanci arɗo yasaki hannun Fattu wanda ke mata azabar ciwo da raɗaɗi, yana mai cewa" ato lamiɗo ne dai yace mu taho daku, dan haka ya zama dole ayiwa lamiɗo biyayya"ya faɗa yana hararar gefensa, dan yaji haushin sakin wannan hannun na Fattu mai shegen laushi da daɗin taɓawa da Baffa yasa yayi.

Fattu kuwa yana sakar mata hannu ,da rarrafe ta ƙara so gurin baffa ta rirriƙe shi tana kuka da faɗin" wallahi baffa ba abinda na aikata ban kashe jauro ba" ta faɗa cikin matsanancin kuka da tsoro, jikin ta sai rawa yake.

Riƙota baffa yayi cikin tausayawa yace "na sani Fattuna baki kashe jauro ba, kuma ba wanda zai kasheki, Allah na tare dake kinji" Ya faɗa cikin sigar rarashi, sannan ya kalli arɗo yace "kai arɗo ka kiyayeni, karka ƙara ƙoƙarin sake aikata irin wannan dabbacin akan ƴata, saboda baka da hankali shine zaka rinƙa janta aƙasa kamar wata dabba ? Jahilan banza jahilin hofi, muje gurin mai garin zanji idan shiyasaka wannan ɗanyen aikin" baffa ya faɗa cikin mugun bacin rai yana mai riƙe Fattu suka nufi faɗa.

_Kai tsaye su baffa suka nufi gurin lamiɗo, hannunsa riƙe da na fattu wacce ke tafiya ahankali cikin azabar raɗaɗin da hannunta keyi ga kuma ciwon jiki. Yayinda su arɗo ke mara musu baya burinsu kawai suga wane irin hukunci lamiɗo zai ɗauka akansu fattu, cikin zuciyar arɗo yake fatan inama lamiɗo ya kori su fattu daga rugar, inyaso su bisu hanya suyiwa fattun fyaɗe, dan su kashe ƙishirwarta dake cin ransu.

Shikuwa mai gari tun daga nesa ya hango su fattu, sai gaba ɗaya nutsuwarsa ta bar jikinsa, ƙuri yayi mata da ido yana haɗiyar yawu da lasar leɓe tamkar tsohon maye. Kallonta yake yana ji kamar yaje ya kamota yayi ɗaka da ita.

Haba malam yarinya tayi bul-bul da ita kamar nunannen tumatur, lallai yau zai sha shagali, lamiÉ—o ya faÉ—a cikin ransa yana mai kallon fattun.

Baffa kuwa suna ƙarasowa gaban mai gari ya nemi guri ya zauna tare da zaunar da fattu kusa dashi wacce gaba ɗaya arikice take, tsorone ƙarara shinfiɗe akan fuskarta, tayi luƙus ajikin baffanta jikinta sai rawa yake, ta kasa ɗaga kanta ta kalli kowa, sai hawaye kawai da take sharewa.

Kowa yanemi guri ya zauna, masu tsayuwa suka tsaya, da ƙyar lamiɗo ya iya saita kansa ya aro nutsuwa ya yaɓa akansa, tare da ɓata ransa ya kalli baffa yace "Malam bukar kana sane da irin abinda ƴarka take aikatawa awannan garin? lamiɗo ya faɗa cikin kakkausar murya .
Ahankali baffa ya gyara zama kafin yace, naji anata wai wai agari cewar Æ´ata tayiwa su jauro turen maciji, amma sam ban yarda da wannan magana ba, dan kuwa Æ´ata ba mai kashe mutane bace, sannan ba mayya bace kamar yadda ake faÉ—a" Baffa ya faÉ—a cikin É—aure fuska .
Cike da ɓaci rai lamiɗo ya fara magana.
"To wallahi Malam bukar bazan ɗauki wannan abun agarina ba, yanzu ace abun nata ya wuce kan kowa sai kan ɗana? sannan kuma kace wai baka yarda da zancen ba? kana nufin nayi maka ƙarya ne? to bari kaji dole ne saina ɗauki mataki mai ƙarfi akanka da ƴar taka, dan ka nuna rashin ɗa'a a gaban fada. Bayan kuma kowa yaga abinda ƴarka tayiwa yaranmu, dan haka bazan yanke hukunci yanzuba sai zuwa gobe idan yaranmu sun sami lafiya, saboda haka yanzu za'a shiga da ita cikin gida anan zata zauna cikin wancan bukkar da ake ajiye masu laifi .
Dan haka kowa ya watse sai zuwa gobe da la'asar adawo nan dan jin hukuncin da zan yanke" Mai gari yana gama faÉ—in haka ya jingina da jikin kujerar da yake zaune akai.
gaba É—ayan mutanen dake gurin sunyi na'am da wannan hukuncin nacewar fattu ta zauna a gidan mai gari, dan karta gudu.

Kuka sosai fattu ta sanya tana riƙe hannun baffa "wayyo Allah na baffa ka taimakeni,dan Allah karka bari akulleni adakin hukunci ,wllh bani nayi musu haka ba ,kuma sunzone da nufin keta min haddi baffa ka kalli Yadda ya famamin targaɗe na wllh ba laifi na bane" fattu ta faɗa cikin matsanancin kuka kamar zata shiɗe.

Cikin tashin hankali baffa ya riƙe hannun Fattu ,ji yake kamar ya fasa ihu,aduniya ba abinda ya tsana irin yaga Fattu cikin damuwa,"kiyi haƙuri fattu ba abinda zai sameki,in Sha Allahu Allah zai saka mana dan wannan mugunta ce ake son yi mana ,kuma Allah yana bayan mai gaskiya"yana gama faɗin haka ya juya gurin mai gari yace "lamiɗo ina neman alfarmar abarmin fattu mu tafi gida ,zamu dawo da ita zuwa goben,dan bata da lafiya kuma barinta ita kaɗai akwai matsala" ya faɗa cikin damuwa da alhinin wannan rashin adalci da ake ƙoƙarin aiwatar musu.

Cike da mugunta lamiɗo yace "kai bukar ina ganin girmanka karkasa in daina gani ka iya bakinka a faɗa kake,kasan idan na riga yanke hukunci ba mai ja dani ,dan haka ka tashi ka bani guri tun kafin raina ya gama ɓaci kuma yanzu zansa aje anemomin macijin duk inda ya shiga daga nan zuwa safiya ,"lamiɗo ya faɗa yana mai kiran wasu matasa yace su shigar da fattu cikin bukkar.

Kuka fattu keyi tana faɗin"wayyo baffana wayyo Allah ka taimakamin zasu tafi dani wayyo Baffa na karka bari su nemo shi zasu kasheshi. "amma haka suka tura ƙeyarta suka tafi da ita ɗakin hukunci.baffa yana ji yana gani ,hawayene masu zafi suka silalo daga idon bawan Allah ,zuciyarsa kamar ta faso ƙirjinsa yakeji, ashe ma ƙoƙarin keta masa haddin ƴa akayi?amma saboda rashin imani da adalci aka ɗora mata sharri,ba komai Allah zai saka musu.

Juyawa yayi ya nufi gida ransa amatukar jagule,yanzu idan wani abun ya sami yarinyar fa?idan wasu suka ƙara yunƙurin cutar da rayuwarta fa?"ya Allah ka karemin yarinyar nan Allah ka duba matsalolin dake kanta da wanda suke shirin samunta.ya Allah ka sauƙaƙa mata ƙalubalen dake gabanta.haka yayi ta mata addu'a harya ƙarasa gida kwata kwata hankalinsa baya jikinsa.
Yana shiga gidan gwogwgo hansai ta sanya dariya cike da mugunta harda riƙe ciki tana nuna baffa da hannu."wllh malam Gara ka cire wannan yarinyar daga zuciyarka, inba haka ba kana tsaye zaka yanke jiki ka faɗi ka mutu.ba ruwa na bani da asara, ai wllh banso lamiɗo ya kyaleta wai har sai gobe ba,daya sani yasa anyanke mata kai yau -yau ɗin nan ,da mun huta da nauyinta akanmu" ta faɗa tana turo wani baƙin ɗan kwalinta mai shegen datti zuwa gaban goshinta.

Kallon ta kawai baffa keyi ,cikin zuciyarsa yake kissima iri saɓawa gwogwgo da zaiyi dan yau zai nuna mata matsayin fattu azuciyarsa ,sai dai yana yunƙurowa da nufin maida mata martani,kawai yaji bakinsa yayi nauyi,wani irin shayinta da tsoro ya mamaye zuciyarsa.kai kawai ya girgiza ya wuce ɗakinsa ,wato itama gidan mai garin taje kenan?ba komai akwai Allah.

Fattu kuwa tunda aka turata cikin É—akin nan banda kuka ba abinda takeyi, ita damuwarta ma yanzu bai wuce na rashin ganin macijinta ba,duk wannan abunda ke faruwa baizo ba.anya kuwa lafiya?kodai wani abu ya sameshi ne?
"Ya Allah ka kare wannan bawan naka ,ka bashi kariya daga sharrin mugayen mutane .

Shikuwa maciji adaidai wannan lokacin yana gidansu fattu yaje nemanta bai ganta ba yayi ta zagaye aɗakinta amma bata nan,tun lokacin datayi masa karatun nan daya fita yaje can jeji ya kwanta ,sam bayajin daɗin jikinsa sosai yake jin ciwo ta ko'ina ajikinsa,sai da lokaci yaja sannan ya nufi gidansu fattu ,ahankali yake tafiya cikin ciyawa da jikin katanga, harya ƙarasa gidansu fattu.
Koda yaje yaga bata nan saiya yi ta zagaye É—akin yana nemanta ,amma bata nan. Kwanciya yayi akan É—aurin kayanta yayi lamo kamar ya mutu.saidai hawayene ke zuba cikin idanunsa .

Can kuwa gidan mai gari ,da misalin ƙarfe bakwai na dare sosai hadari ya haɗu agarin, dan haka kowa ya shige cikin gida dan gudun zubowar ruwan da akowane lokaci yana iya sauƙa.

Daidai wannan lokacin kuma fattu na duƙunƙune cikin ɗakin hukunci sai kuka take zuciyarta tayi mata ƙunci ga yunwa dake addabar ta rabo ta da abinci tun madarar da baffa ya bata da safe ga kuma hannunta sai zagi yake mata.
Ahankali taji ana turo kofar É—akin hukuncin,da alama shigowa za'ayi,ga duhu aÉ—akin.
Zabura tayi cikin sauri ta miƙe tsaye jikinta na karkarwa,kar dai ace su jaurone suka dawo ?wayyo Allah na " ta faɗa tana dafe ƙirjinta ,zuciyarta kamar zata fito dan tsoro da firgici.
Cikin rawar murya tace "wa...w....ayee."
Ahankali cikin murya mai kama da raÉ—a,yace "ke kwantar da hankalinki,nine nan lamiÉ—o"
Ya faÉ—a yana mai haska tocilan É—insa .

Cikin zubar da hawaye tace "dan Allah lamiÉ—o ka fitar dani daga gurin nan ,wllh ban aikata komai ba,bani na kashe jauro ba"ta faÉ—a cikin kuka.

"Kinga ki nutsu jauro bai mutu ba yana raye ,kuma idan kika bani haÉ—in kai muka yi komai cikin sirri ,to zan kyale ki ki tafi gida abinki"lamiÉ—o ya faÉ—a yana matsowa gareta.

Ja tayi da baya cikin sauri tace "me kake so nayi maka ?dan Allah ka gyaleni na tafi gida an fara ruwa"ta faÉ—a cikin kuka,dan ta gano manufarsa ,irin tasu jauro ce ,wato fyaÉ—e yake son yi mata.

Matsowa lamiɗo yayi tare da ruƙo hannunta yana mai cewa"Ayya fattu yarinya mai kyau da kyan jiki ki yarda dani mana duka -duka minti nawa ne ba dayawa zanyi ba kinji ki taimaka min"ya faɗa yana mai janyota jikinsa sosai .

"Wayyo Allah na baffa kazo ka taimakeni,dan Allah lamiɗo kayi haƙuri wllh ba kyau kaji tsoron Allah ka tausaya min na roƙeka"fattu ta faɗa cikin rawar jiki da matsanancin kuka,tana mai tureshi daga jikinta,banda warin tsufa ba abinda yake yi.
Chapter 6 · 0% Book details