← Book details Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 27

Sashe 23

Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

" Wllh Ni haushi ma kake bani ,akan wannan kucakar zaka wani tsaya bata lokacinka,me zaka samu jikin wannan banzar?"cewar Zulaihat cikin haushi.

" Ke wllh ƙarya kike kinsan wannan yarinyar tafiki komai na mata ,kalleta mana da kyau ki gani ,aikinsa ba karya ,malam komai yaji yadda ake bukata" cewar Rashad cikin wani irin shegen voice .
Tsabar haushi daya kama Zulaihat tashi tayi afusace ta bar falon tana ƙunƙuni.

Adeeb yana can ƙasar farin yana gudanar da binciken kasuwanci sa ,gefe guda kuma ya dage sosai wajen neman iyayen fattu,yasa hoton sarkar nan Tata da rigarta tare da nuna yana neman wanda yasan waɗan nan kayan,saidai bai yarda ya nuna wata alama da zata nuna shike neman wanda yasan wani abu game da kayan ba,dan nunawa yayi shidin talaka ne sosai .

Kullum suna waya da ammi yana tambayarta fattu ,sannan yace ta rinƙa koya mata Yaren larabci ,kuma ammi tana kokarin koyawa fattun ,dan yau take son kawo tsohuwa salima ,ta zauna tare da Fattun dan ta koya mata Yaren sosai,tunda ita ta iya hausa sosai.kuma kusan ahannunta Adeeb ya girma ,ita tayi renonshi.

Wai ina batun baffa ne?
Allah Sarki baffa lokacin da aka kaishi dakin hukunci ,saida yayi kwana biyu basu wai-waiceshiba,yana can yana fama da zazzabi sakamakon dukan da sukayi masa.sau daya ake kawo masa abinci.

Ranar kwana na biyun ne da yamma aka fito dashi dan zartar da hukunci,lokacin mai gari ya danji dama -dama an gyara masa karayar daya samu har uku .jauro kuma yana nan cikin halin bakin ciki,dan kuwa jauronsa ta lalace ,bazata ƙara amfanuwa ba,ta motse ta zama ƴar ririya kamar sillen kara.
Shiruwa abokin ta'asar tashi,yanan ido daya ya tsiyaye ,rabin fuska ya zagwanye ,ya zama kamar horo,arÉ—o ma hannu ya shanye ya zama kamar lauje.

Cikin fushi da bacin rai tare da bakin ciki mai gari yace , sakamakon ta'adda cin da baffa da yar shegen daya kawo musu cikin gari sukayi,an karbe duk wasu shanayensa da tumakai harda gidansa ,matsayin diyyar abinda mayyar daya kawo gidansa tayi,sannan ankoreshi daga garin ,saboda ƙarya da cin amanar yan garin da yayi ,na cewa fattu yarsace.

Baffa yayi kuka sosai,akan wannan rashin adalcin da akayi masa.amma haka ya haƙura ya miƙawa Allah lamarinsa.

Koda ya dawo gida tuni labari ya isa kunne gwogwgo hansai,dan haka yana shigo taci kwalarsa tace ya bata takardar ta bazata iya zama da faƙiri ba.
Nan take kuwa baffa yayi mata saki daya .kuma sam ta hana Æ´aÆ´an ta subi baffa. Shi kadai ya bar garin cikin mawuyacin hali.
Allah Sarki baffa ,Allah ya saka maka wannan zalumcin da akayi maka.

Acan misra kuwa ,amma na hango zaune akan wata ƙayatacciyar kujera , da waya ahanunta ,magana take cike da nuna yanayi na jimami, masu mata hidima na can gefenta azaune.
" Zanyi duk iya ƙoƙarin na,ɗan ganin naja yarinyar ajikina, in Sha Allah muke da nasara" amma ta faɗa tana mai ajiye wayar.

Murmushi tayi kafin tace" Maryam zaki san koni wacece ,zanyi abinda saiya girgizaki,saina rabaki da dan da kike takama dashi" amma ta faÉ—a tana mai gutsirar apple.
Amma dai itace kishiyar mahaifiyar Adeeb,wacce lokacin da Adeeb yazo ta bar É—akin mahaifin Adeeb cikin ruÉ—ani.

Washe gari da safe fattu ta tashi da wani irin matsanancin ciwon mara,sai kuka take tana riƙe da cikinta.
Tsohuwa salima nata rarrashinta tare da bata haƙuri,dan tana tunanin period me zai yiwa fattun.

Sosai fattu ke jin mugun ciwon mara,sai murƙususu take cike da azaba tana kiran " Wayyo Hammana zan mutu "

Wani irin amai ne ya yunkuro mata,da gudu ta mike ,da nufin zuwa toilet ,saidai taku daya biyu, jiri ya kwasheta ta tafi luuuuuuuu tayi kasa.....

Masu karatu masoya,ina godiya da addu'ar ku gareni ,kuma jiki alhamdulillah naji sauƙin sosai ,

Na gode sosai da kulawa,
Much luv sosai da sosai.

Mrs babi ce 💘💘💘

Share and comments
Fisabilillah.

More comments
More typing.
[7/27, 8:02 AM] +234 703 954 1650: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄

MACIJI NE🪱🪱🪱

Na mammy kabeer
(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book

Page 39/40

________________Wani irin amaine ya tasowa fattu,dan haka da gudu ta mike tana mai riƙe baki,sannan ta nufi toilet.saidai taku ɗaya -biyu tayi kiri ya kwasheta,baya tayi luuuuu!!!zata faɗi.da sauri ta runtse idonta tana mai saki wani ɗan siririn ihu,gaba daya ta gama saddaƙarda cewa ta fadi ,jira kawai take taji ta ina zata fara jin raɗaɗin.saidai maimakon tajita aƙasa,sai taji ta faɗa jikin mutum,wani irin ƙamshine ya ziyarci hancinta mai daɗin gaske,da sauri ta buɗe idanunta dan ganin jikinwa ta faɗa.

ido hudu sukayi da Hammanta, dan shigowarsa kenan dakin ya hangota zata faÉ—i ,shine yayi saurin tarota, dama yana sauka afadar ko gurin mai martaba baijeba yayi sashin ammi,duk kuwa da cewar maimartaban yana ta kiransa awaya akan ya dawo gida .

Dan kumshe ido fattu tayi cikin azabar ciwon da mararta keyi ,sannan ta buÉ—e idonta ,tare da saukesu akan Hammanta,so take ta gasgata shiÉ—in ne ko gizo idonta keyi.

Aikuwa shine wllh Hammanta ne ya dawo,cikin azama kuwa fattu ta rungume Adeeb tare da sakin kuka,dama kuma kukan take.
" Hamma ina katafi ka barni?inata nemanka amma banganka ba?dan Allah Hamma karka ƙara tafiya ka barni,kaga bani da lafiya cikinsu ciwo yake min sosai" fattu ta faɗa tana mai cusa kanta aƙirjin Adeeb .

Ahankali Adeeb ya lumshe idanunsa tare da rungume fattu shima tsan-tsam ajikinsa,dan kuwa tabbas ba karya yayi kewar fattu sosai ,kullum da ita yake kwana yake tashi,kwana uku da yayi baya ganinta ,jinsa yake kamar mara lafiya.

" Is ok stop crying hulwa,ai gani na dawo ko?"ya faÉ—a yana mai É—ago kanta .
Buɗe baki tayi da nufin yin magana ,amma gaba daya aman nan ya taho mata ,aiku ba ɓata lokaci ta wanke Adeeb tass!! Da aman nan ajikinsa.
Shikuwa Adeeb ko ajikinsa ,bai damu da aman da tayi masa ba ,ya riƙe ta sosai ajikinsa yana mai shafa bayanta,tausayinta yake ji har cikin ransa,bata da lafiya sosai dole ya kira likita adubata.

Tsohuwa salima ce ta karaso garesu tare da faÉ—in"ayya sannu fateema kinji,maza kawota kaje ka wanke jikinka, wllh tun jiya take fama da ciwon cikin nan,nace yaro kodai girma ne zaizo mata?tsohuwa ta faÉ—a tana mai kallon Adeeb,
Dan sunkuyar da kansa yayi ƙasa yana mai sosa kai,dan ya gani abinda tsohuwa ke nufi,ita haka take dama ba ruwanta idan zata faɗi magana,kai tsaye take faɗi.
" Ammm nanny bari na kira likita ya dubata. Ya faɗa yana nufar toilet riƙe da fattu,wanke mata jiki yayi tare da bakinta, shima ya wanke inda ta batashi,sannan ya dawo da ita cikin ɗakin, kwantar da ita yayi akan gado tare da shafa gefen fuskarta yace"sannu yanzu za'a baki magani kinji?"ya faɗa cike da tausayawa,ji yake kamar ya maida ciwon jikinsa.

Lumshe ido fattu tayi tare da kamo hannunsa ta rike gam cikin nata tace"Hamma karka tafi dan Allah" fattu ta faÉ—a tana mai lumshe idanunta .

Hannun nata ya riƙe da ɗayan hannunsa kafin yace "ba inda zani zan sake kaya in dawo yanzu" ya faɗa yana mai mikewa tare da ficewa daga dakin.
Tare suka dawo shida likita,wadda ta kasance likitar gidan ce , mai duba mata.
Sosai ta duba fattu ,kuma ta gane period ke don zuwa mata ,kuma farkon yine shiyasa take jin ciwo.
Dan haka bayani tayiwa Adeeb tare da bashi magungunan da Fattun zata sha.sannan ta lika always Jikin pant taba nanny akan idan jinin yazo saita bata tasanya.

" Yawwa Ni dama nayi tunanin ko girma ne zatayi ,dan ciwon yayi yawa,Allah Sarki ashe kuwa shine ,bari na haÉ—a mata tea mai zafi ta sha"nanny ta faÉ—a cikin tausayawa tana mai nufar kitchen.
Shidai Adeeb yana zaune bakin gado,tunda yaji abinda ke damun fattu,baice komai ba ,kawai yana kallonta dan ta É—an sami barci .

Cikin girmamawa likitar tayiwa Adeeb sallama ta fita akan zata dawo anjima .
Kai kawai ya É—aga mata ba tare da ya kalletaba.

Kusan minti biyar saiga nanny ta dawo riƙe da wani kyakykyawan kofi sai turiri yake ,mikawa Adeeb kofin tayi tana mai cewa" ungo magajin faɗa tashe ta maza ta sha zatayi daɗi,kuma jinin zai sauko da wuri" ta faɗa tana mai nufar ƙofa again tana cewa " bari i ke in kula da farfesun can dana ɗora mata,kasan shima yana taimakawa mace idan tana jini"ta faɗa tana ficewa.

Kallo Adeeb ya bita dashi,yana mai girgiza kai,yana son tsohuwar nan ,saidai tacika surutu da sanya mutum jin kunya.
Ahankali ya É—an shafe fuskar fattu da tayi wani fayau da ita ,sai kyalli take,ahankali ta buÉ—e idanunta tare da saukewa akan kyakykyawar fuskar hammata.
"Hamma" ta furta ahankali tana kallonsa.

" Tashi Kisha tea maza" ya faÉ—a yana mai taimaka mata ta zauna bayan ta sanya mata fillo abayanta.
Da kansa yake bata tea É—in abaki,saida tasha kusan rabi sannan tace ya isheta, ajiye sauran yayi yana mai kallonta kafin yace" ya kike jin jikin naki?"

" Da sauki Hamma saidai jikina ba kwari ,kuma har yanzu inajin ciwo anan dina"fattu ta faÉ—a tana mai nuna masa saitin marar ta.

Kawar da kai yayi da sauri yana mai cewa" is ok zai daina "
Chapter 23 · 0% Book details