Sashe 5
Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shikuwa macijin nan burburwa ya ci gaba dayi yana murɗewa jikinsa na turiri tare da sauya kala.can kuma ya fara wani irin ƙara mai kama da gurnanin zaki.cikin tsoro fattu ta dawo da kanta ƙasa tana kallon macijin , sakamakon wannan sautin ƙara da taji yanayi.sai lokacin hankalinta ya kai kanshi taga abinda ke faruwa.
Tsorone ya kamata ƙarara "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"shikenan ta tabbata wannan ba maciji bane tabbas aljanine ,ko kuma aljanine ya shiga jiki sa,na shiga uku ni fattu ya zanyi da rayuwata?meke shirin faruwa dani" ta faɗa cikin muryar tsoro da shiga ruɗu.
M4
Shikuwa macijin nan tana daina karatun saiya daina burburwar da wanann gurnanin,ahankali kuma jikinsa ya dawo yadda yake . Ya jima kwance lamo kafin ya fara motsi,kansa ya ɗago tare da fasa kan yana kallon fattu,gaba ɗaya idanunsa sun koma baƙiƙirin dasu sannan wasu irin ƙananan layoyi suka bayyana kusan guda uku aƙasan kanshi, sai wani irin motsi suke kamar ya'yan tsutsa.
Karkarwa jikin fattu keyi kamar an saka mata shokin, lamarin ya matukar bata tsoro ,meye wannan É—in haka suka bayyana jikin macijin nan? Me yasa daga fara karatun Alqur'ani gaba daya ya sauya kama?tabbas akwai wani boyayyen al'amari game da wannan halittar dake gabanta,kuma zata ci gaba da bibiyar macijin nan sannu kan hankali har saita gano menene tattare dashi.
Tana nan maƙale jikin katangar karan kamar ƙadangaruwa dan tsabar tsoro da shiga shock ,idanunta ƙuri akan macijin ,wanda shima ita yake kallo ,kusan minti biyar suna haka ,taga macijin ya sulale ya bar ɗakin ta wannan hanyar tashi.
Rarraba idanu ta farayi tana dafe da ƙirjinta ,yau kam tana ganin ikon Allah kala kala ,anya kuwa bata janyowa kanta masifa ba?waima meye alaƙarta da wannan halittar ne?ko dai baffanta zata sanarwa halin da ake ciki ne?kai a'a ba yanzu ba tukunna ,ya kamata ta zama jaruma tayi wanann aikin koba komai zata taimaki rayuwar macijin,dan ta fahimci akwai boyayyen al'amari atareda shi.
Haroji kuwa gaba ɗaya ya fice daga hayyacinsa sai ihu yake yana faɗuwa ƙasa ,ahaka ya nufi gidan lamiɗon garin ,wanda shine mahaifin jauro ,yana ihu yana tumami, har yaje gaban lamiɗo ya faɗi yana "wayyo idanuna ,wayyo fuskata lamiɗo ka taimaka min.
Ruɗewa lamiɗo yayi wanda yake tsaye jikin wata sanuwa yana bata ciyawa, lamiɗo bashi da imani ,azalumine sosai ,kuma mutanen garin suna matuƙar tsoronsa, dan haka yake mulki na zalumci agarina,ganin halinda haroji yake ciki ya sashi tsayawa cak da abinda ke yi ya dube shi yace "Kai haroji menene hakan ?ina jauro?me yasameka? Waɗannan sune tambayoyin da lamiɗo ya dinga jerowa haroji wata na bin wata.
Cikin azabar ciwo da fitar hankali haroji yace "jauro ya mutu maciji ya cinye masa jauronsa yana bakin rafi"
Ai dajin wannan batu hankalin lamiɗo ya tashi ,nan da nan yayi kan haroji yana faɗin wane macijin ?me kake cewa ?jauro ya mutu?ƙaryane badai agarina ba ,ba wanda ya isa ya zo garina ya kashe min ɗana."lamiɗo na gama faɗin haka ya kira mazan garin ,ya sanar dasu maza aje bakin rafi ataho da jauro.
Aikuwa cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗauko shi kamar gawa .
Nan da nan lamiÉ—o ya nemi haroji ya sanar dasu abinda ya faru .
Nan ya sanar dasu iya abinda idanunsa suka gani,dan shima yana cikin mugun halin mutuwa ko rayuwa dan tuni gurin da jinin nan na macijin ya taɓa ajikinsa yayi wani irin kore shar yana zubar da wani yallow ɗin ruwa .
"LamiÉ—o fattu ce ta Turo mana macijin nan ,shine ya kashe jauro"abinda haroji ya faÉ—a kenan ya sume.
Nan da nan mutanen gurin suka fara maganganu Suna faÉ—in da "Dama hansai ta faÉ—a tace mayyace yarinyar ,tunda har ta fara kashe mutane ba zasu yarda ba sai an hukunta itama.
Ran lamiɗo ya ɓaci sosai ,dan dama yana jin haushi yarinyar da ubanta,ya shirya neman aurenta amma sam taƙi yarda wai karatu take,yanzu kuwa dama tasameshi da zai hukunta su ita da tsohon nata.dan haka cikin bada umarni yace lallai lallai aje ataho da fattu da ubanta .
_____Nan da nan fusatattun rugar suka nufi gidan malam bukar ,dan aiwatar da ƙudirin lamiɗo.
Allah Sarki fattu kuwa a wanann lokacin tana ɗakinta cikin jimami da tunanin abinda ta gani yau ɗin nan,haka nan ta tsinci kanta da son sanin menene wannan abubuwan dake motsi aƙasan wuyan maciji? wanda tun daɗewa bata taɓa ganinsu ba sai yau,waya sani ma ko wani akayiwa asiri ajikin macijin ?tabbas zatayi iya ƙoƙarin ta dan ganin ta raba macijin nan da wannan abubuwan ,ta yadda koda wani aka yiwa asiri ta hanyar macijin, to asirin zai karye .sannan tana fargabar gwogwgo ta gano cewar tana gidan kuma bata ɗebo ruwan ba.kuma ahalin da ake ciki yanzu bazata iya komawa rafin nan ba ,.dan ta tsorata dasu jauro .
Hayaniyar mutane ce ta cika gidan nasu fattu ,wanda haka yasa gwogwgo hansai fitowa dole badan ta soba, Dan har lokacin nan ita da yaranta ba wanda yayi sallar asuba.
"Kai su waye haka suka zo suka cika mana gida da ihu kamar ana yaƙi?"cewar gwogwgo hansai tana gyara daurin ƙirjinta dake ƙoƙarin kuncewa bayan ta fito daga ɗakin.
"Aa meye hakan arÉ—o ?lafiya na Ganku da yawanku kun shigo?ta tambaya lokacin da idanunta ya sauka akan mutanen da suka cika gidan,kusan duk mazan garin ne.
Cikin masifa wanda aka kira da arÉ—o yace "wllh yau saimun É—auki mataki akan bukar da fattu ,haka kawai yarinya ta fara kashe mutane ,kuma ta rasa ta kan wa zata fara sai É—an gidan lamiÉ—o ?wllh yau sai mun kashe Shegiyar yarinyar nan"ya faÉ—a yana wani zazzaro idanu kamar zararre.
Eh wllh afito mana da ita kawai mukaita gurin lamiɗo ya bamu izini mu kashe mayya.gaba ɗayan matasan dake bayan Arɗo suka haɗa baki wajen faɗi haka cikin nuna fusata da ƙosawa abasu fattun .
Wani irin farin ciki da jin daɗine ya kama gwogwgo hansai ,shikenan zata rabu da alaƙaƙai cikin sauƙi Allah yasa akasheta kowa ya huta ,dama su haɗa da bukar ɗin da yake ɗaurewa fattu gindi ,koba komai shanunsa sun zama nata.gwogwgo hansai ta faɗa cikin ranta.kafin ta kalli arɗo da sauran mutanen tace "aikuwa idan aka kasheta an kyauta ,dan nima nan wllh so take ta cinyeni nida yarana, jiya da kyar mukasha data maƙuremin wuya wai saita cinyeni, ku ɗan jira kaɗan yanzu zaku ganta shegiya gantalalliya,banma san inda ta tafiba, dama haka takeyi kullum inta fice yawon iskanci bata dawowa da wuri,tana can gurin maza"gwogwgo hansai ta ƙarasa maganarta tana mai buga hannu acinyarta.
"Aikuwa yanzu zamuje mu nemota ko ina ta shiga, ina mu kasu gida 3 wasu sutafi bakin rafin wasu sushiga jeji, mukuma zamu jira ana "cewar arÉ—o kenan yana kafe sandarsa akasa,sannan ya gyara tsayuwarsa.
Duk wannan abunda ke faruwa akan kunnen fattu, tana jin komai ,saidai tashin hankali,firgici tsoro da kuma ruÉ—ewa sun hanata koda yin kwakwkwaran motsine .
Numfashinta ma da ƙyar yake fita tsabar ruɗewa.
Ta shiga uku !shikenan yanzu kasheta za'ayi?laifin me tayi da za'a kasheta?me baffanta yayi ake nemansa shima? Dama jauron mutuwa yayi ? innalillahi !!!yanzu ya zatayi.
Wani kukane ya kubce mata cikin sauri ta toshe bakinta tana kuka sosai kamar ranta zai fita,ji take dama tana da ikon ɓacewa, tabbas da ba abinda zai hanata ɓacewa ta bar duniyar ma gaba ɗaya.
Ahankali ta miƙe cikin sanɗa ta leƙo da kanta ,ba ƙaramin tsoro tajiba lokacin da taga mutanen da suka zo tafiya da ita.shikena kawai ta mutu,yanzu shikenan bazata cika burinta na ganin innarta ba?wayyo "Allah ka kawomin ɗauki "ta faɗa cikin raunananiyar muryarta mai cike da tsantsar tsoro.
Ahankali ta ƙara leƙo da kanta waje ,cikin rashin Sa'a kuwa sukayi ido huɗu da dan gidan gwogwgo hansai umaru.wanda hayaniyar mutane tasa suma suka farka.
"Laaaah Ardo, gwogwgo ga fattun can cikin ɗakinta tana leƙowa"ya faɗa yana nuna ɗakin da Fattu ke ciki. Cikin hanzari fattu ta koma cikin ɗakin tana mai runtse idonta tare da dafe ƙirjinta. "Shikenan sun ganni wayyo Allah na baffa,wayyo MACIJINA kana ina kazo ka taimakeni zasu kasheni wayyo ni fattu" Fattun ta faɗa tana mai leƙa hanyar nan da macijin Kebi idan zai bar ɗakin nata inya zo, kamar zararriya haka Fattun ke bankada hanyar macijin da hannunta.
"Munafuka mayya dama kina ji ana neman ki shine kika ɓuya nan? To fito yau dubunki ta cika, mutuwa zaki yi wllh sai kin bar duniyar nan yau nima na huta da ganinki, maza arɗo zoka tafi ta ita gata nan"gwogwgo hansai ke faɗin wannan maganar tana daga bakin ƙofar dakin Fattu, dan tun lokacin nan da tasha matsa agurin maciji bata ƙara shiga ɗakin Fattun ba.
Aikuwa kafin ta rufe baki su arÉ—o sukayo kan Fattu suna janta.
"Wayyo Allah gwogwgo karki bari su tafi dani zasu kasheni ,wllh ban aikata komai ba wayyo Allah na gwogwgo ki taimaka min"abinda Fattu ke faɗi kenan tana miƙawa gwogwgo hannu cikin kuka mai tsanani.
"Ai wllh dana taimakeki gara hannuna ya karye Shegiyar yarinya ,kutafi da ita can ku kashe banza" gwogwgo ta faÉ—a tana kaÉ—a hannu irin yadda ake korar kaji ,cikin farin ciki take maganar.
Ihu Fattu keyi tana kuka,amma haka suke janta kamar akuya aƙasa, suna cikin tafiyar ne sai ga baffa aguje yazo gabansu sai kuma suka tsaya, shima Baffa tsayawar yayi yana riƙe da sanda sai haki yake, dan yana can bayan gari ya sami labarin abinda ke faruwa acikin garin da gidansa, shine ya rugo yazo .
Aikuwa Fattu na ganin baffa ta ƙara fasa ihu tana cewa" wayyo baffana ka taimakeni zasu kasheni" ta faɗa tana miƙa masa hannu, abin tausayi dukta susuce tayi buju buju da jiƙaƙkiyar ƙasa.kallonta baffa yayi
Cikin bacin rai mai tsanani ya ce.
"Sakarmin yarinya arɗo kona rotsa maka sandar nan akanka" baffa ya faɗa cikin hargowa da ƙaraji.