← Book details Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 27

Sashe 26

Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rashad kuwa banda hura hanci ba abinda yake,yana zatace wani wai baruwansa da babyn na?wannan ma ai shirmene,wllh saidai kome zai faru ya faru ,amma ya gani ya gyasa kuma saiya ɗana.ya faɗa cikin zuciyarsa,kafin ya mike cikin rashin biyayya ga mahaifiyar tasa yake magana" nufa ba wanda ya isa ya hanani yin abinda naga dama,ke dayake hanaki naki uzurin, ko kina tunanin duk irin mugun abinda kike ƙullawa Adeeb ɗin ban sani ba?wllh idan aka takuramin zan fasa kwai ba ruwana,kinji kinsawa mata ido,baiwar Allah ita kuma tana ta nunawa danki so da kulawa" Rashad ya faɗa cikin rashin kunya yana ficewa daga ɗakin.

Kallonsa kawai amma keyi,idan da sabo yaci ace ta saba da rashin kunyar rashad,sam baya ganin girmanta, amma zatayi maganinsa.
Ta faɗa cikin ranta tana mai tunanin yadda zata wulaƙanta ammi cikin ruwan sanyi.

Fattu kuwa barcine yayi nasarar É—auke ta ,har cikin barcinta mafarkin Hammana tayi tayi,yana mata wasanninsa masu nutsar da jiki da zuciya .sai kusan la'asar kafin ta farka daga barci,ba laifi marar ta daina ciwo,dan likatar nan ta dawo dan ta dubata lokacin tana barci .

Wanka nanny ta sata tayi tare da bata wata always É—in ta saka bayan ta lika mata jikin pant.abinci taci tasha magani sannan ta zauna akan gado tana kallon Film É—in da nanny ta kunna mata jikin kayan kallo.

Ta maida hankalinta sosai tana kallon Film É—in ,indian yayinda take ganin kamar itace da Hammana suke lobayya.lol

Nanny ce ta shigo É—akin ta zauna kusa da fattu tana mai faÉ—in" sannu Æ´ar nan ya jikin naki? Nanny ta faÉ—a tana ajiye wani bolw duke da kayan marmari a cikinsa.
Kallonta fattu tayi tare da sakin murmushi,dan tana ƙaunar matar har cikin zuciyarta,tana da kirki ga kulawa da mutum,dan zaman da sukayi sosai fattu ke cintar wasu kalmomin na larabci,saidai baya iya maidawa ba.
Jinjina kai tayi alamun da sauƙi, kafin ta fara cin apple.sosai take jin dadin wannan abun mai kama da dankali aradu idan tanacinsa har wani lumshe ido take.

Ammi ce ta shigo ɗakin cikin shigar ta ta koda yaushe wato doguwar riga mai shegen kyau da ɗaukar ido,gaba daya jikinsa sarkokin gwal ne ,sai ƙamshi take bugawa,cikin murmushi take shafa fuskar fattu tare da mata ya jiki,sunkuyar da kai fattu tayi cikin kunya,bata e komai ba.
Kallon wuyan fattu ammi tayi, tare da kafe sarƙar wuyan nata da ido,tabbas tasan wannan sarƙar da masu alaƙa da ita,amma ta yaya sarƙar zata kasance a wuyan wannan yarinyar,lallai dole ta raba ta da sarƙar nan dan kawar da zargi.zama tayi abakin gadon,cikin murmushi tana shafa lalausan bakin gashin fattu,kafin ta kalli nanny cikin murmushi tace " nanny ƴar taki fa akwai kunya sosai,ban sani ba kodai sirikata ce ita?da alama ko suna soyayya da dana ne " ta faɗa tana mai shafa sarƙar da hannunta.

Murmushi nanny tayi wacce ke tsaye can gefe tun shigowar ammi dakin,kafin tace " ranki ya dade gimbiyar uwar magajin faɗa,ba wannan alamun atare dasu,yana mata kallon ƙanwa itama tana masa kallon yaya ne,wannan shine abinda na fuskanta atsakaninsu" nanny ta faɗa cikin murmushi tana kallon fattu.

Murmushi itama ammin tayi,tana mai jin wani sanyi cikin ranta,yanzu ta sami nutsuwa ,akan ba wata alaƙa atsakaninsu,saura biye duk wata alama da zata sa agane iyayen fattu.

" Nanny kawo mata lemo mana ,naga ba wani drinks agabanta " ammi ta faÉ—a dan son fitar da nanny É—aga É—akin.

Da sauri nanny ta fice tana faɗin " angama ranki ya dade" tana fita ammi ta kalli fattu tare da sakar mata wata uwar harara,ta gefe ,kafin ahankali cikin dabara ,ta yadda fattu bazata taɓa tsammanin ancire sarƙar wuyanta ba ,ammi ta zare sarƙar tare da damkewa cikin hannunta.

Lokacin da take zare sarƙar ,da sauri fattu ta kai hannunta dan jin abu yana ɗan yawo awuyanta. Cikin sauri ammi tace " ayya ƴata bari incire miki wani ɗan zarene awuyan naki" ta faɗa tana mai karasa cire sarƙar.

Nanny na shigowa ita kuma ammi ta mike tare da ficewa daga ɗakin cikin tsantsar farin ciki.da alama komai zaizo mata cikin sauƙi.

Adeeb kuwa bayan yayi wanka ya huta,sannan yaci abinci kaɗan ,kafin ya janyo computer yana ɗan wasu ayyukan da ita,har lokacin yana jin ciwon marar kaɗan,saidai ba zazzaɓin.yana aikin ne kawai amma zuciya da tunaninsa suna kan fattu,dan so yake yaga Wane hali take ciki.kasa ɗaurewa tayi ya dauko wayarsa ya kira nanny, Tana dagawa ta ce " magajin fada ɗana ɗan albarka,me kake buƙata.

Murmushi yayi yana mai ɗan kumshe idanunsa,bayan amminsa nanny itace uwar riƙonsa da bazai taba daina ƙaunarta ba.cikin sanyin murya irin ta masu jinya yace "nanny ya jikin nata" ?
"Jiki kam da sauƙi ka gantama tana kallo bari na bata wayar."
Cewar nanny Tana mai karawa fattu wayar akunne.

"Hmmmmm Indai wanna ce Allah yasa tasan me ake yi da wayar ma"Adeeb ya faÉ—a cikin zuciyarsa.
Fattu kuwa kallon nanny tayi jin ta ƙara mata waya akunne,meye kuma wannan haka ?nanny ta doramin akunne na?

Fahimtar kamar fattu bata gane me zatayi da wayar bane yasa nanny tace " yayanki ne Adeeb ya ke magana,riƙe bari naje kitchen" nanny ta faɗa tana damkewa fattu wayar ahannunta.

Kallon haÉ—aÉ—diyar wayar fattu tayi tana mai cewa acikin" Hamma kuma anan,to ta yaya yashiga cikin wannan É—an karamin abun har yake magana?wayyo Allah na ta yaya Hamma zai fito ?na shiga ukuna Hamma kana ina ?kana jina ?dan Allah ka fito" fattu ta faÉ—a cikin muryar kuka,nan da nan hawaye ya fara wanke mata fuska.

Lumshe idanu Adeeb yayi ta can bangaren dan yana jin duk abinda yake fadi,kuma yasan za'ayi hakan .ya rasa wane irin shirme ke samun fattu,yanzu inda zuwa yayi ta ganshiba shikenan zatayi ta kukane gashi bata da lafiya.
Mikewa yayi da sauri ya nufi ƙofa.

Rashad ne tare da ammi suna tsaye jikin wata ƴar ƙaramar runfa mai kama da bukka ,magana suke mai muhimmanci,dan kuwa sai murmushi Rashad keyi yana kallon ammi.
" Aikuwa ammi yanzu zanje na É—an ganta dan wllh ko barci bana iyayi,gaba daya babyn ta rikitani " rashad ya faÉ—a yana mai dage gira daya.

Dariya ammi tayi kafin tace " maza É—an jeka abinka ,ba mai hanaka abinda ranka ke so,amma karka sake kayi mata komai,kajira lokaci,kawai kaje ka ganta kasami nutsuwa ranka" ta faÉ—a tana mai shafa kan Rashad din.

Murmushin jin dadi yayi tare da sumbatar hannun ammi,yace " shiyasa nake sonki fiye da mahaifiyata ammina"ya faÉ—a yana barin gurin.

Wani shegen murmushi ammi tayi tana mai binsa da kallo kafin tace " dani kike magana hafsat, nayi alƙawarin saina kawo karshenki afadar nan, keda ɗanki.koba dani zakiyi gasa ba?muje zuwa" ammi ta faɗa cike da gadara tana kaɗan kai.
rashad na shiga dakin da fattu take ya ganta zaune tana kuka,ga apple ɗin ta ahannu wani abaki,cike da shaukin babyn ya ƙarasa inda take ya zauna kusa da ita sosai ,da sauri fattu ta matsa can gefen gadon tana kukanta.

"Ohhh baby menene kike kuka?masu kyau ga basa kuka kiyi shiru,fadamin abinda ke saki kuka ?ko zakuɗa chocolate?ko ice cream kike so,Rashad ya faɗa yana mai ƙara matsawa kusa da fattu sosai .

Yunƙurin mikewa fattu tayi daga gurin da take ,dan ya kunaceta sosai,rashad yayi saurin janyota jikinsa ya rungume ta, ta gefe" haba babu kiyi shiru mana bana son ganin ki cikin damuwa,zo in baki chocolate kinji" ya faɗa yana ƙoƙarin hade bakinsu guri daya bayan ya riƙe fuskarta.

Cikin kuka fattu ta hankaɗe shi tare da fitowa daga kan gadon tayi kofa da gudu tana kuka.biyota yayi shima,saidai kafin ya ƙaraso ta buɗe kofar ,tana buɗewa kuwa taji ta faɗa jikin mutum,da sauri cikin tsoron ko rashad ne fattu ta dago kanta tana kallonsa. Ai tana ganin Adeeb ne tayi sauri ƙanƙameshi tana kuka.
Riketa yayi da sauri shima yana mai shafa bayanta ahankali,idanunsa alumshe" ya isa haka ba gani ba ?ki daina kukan " Adeeb ya faÉ—a yana mai dago kanta.
Cikin kuka fattu take nuna masa rashad" Hamma kace ya fita bana son ganinsa tsoro yake bani"ta faɗa tana mai ƙara kwantar da kanta aƙirjin Adeeb.

Da sauri Adeeb ya dawo kansa ,aikuwa carab idanunsa ya sauka akan na rashad,wanda yayi tsilli -tsilli dashi yana kallonsa.

Cikin wata irin zuciya da ɓaci rai Adeeb yace "what? rashad ?ubanme kakeyi anan?me yakawoka dakin Hulwa?me kayi mata" Adeeb ya faɗa cikin karaji yana ture fattu gefe guda tare da tunkarar rashad gadan-gadan kamar wani zaki.
Rashad kuwa cikin rashin kunyarsa ,duk da yana jin tsoron Adeeb ɗin,yace" kamar ya me ya kawoni ɗalibta?nazone in dubata kamar yadda ammi tace ,kuma kaima ai...bai karasaba sakamakon wani bahagon mari da Adeeb ya ɗauke shi dashi,kafin ya dawo hayyacinsa ya ƙara ma wani marin,nan da nan hancin rashad ya fara zubar da jini,kuma Adeeb ya shaƙe masa wuya tare da haɗa shi da bango.

Jikinsa banda karkarwa ba abinda yake" idan ka sake ka ƙara kallon koda inda Hulwa take ,wllh,billahi,saina illataka .wawa jaki dan iska "Adeeb ya faɗa cikin zafin rai da jin kamar ya karkarya rashad ɗin.

Rashad kuwa tsoro ya gama kamashi, gashi Adeeb ya shaƙe masa wuya yana neman kashe shi.sai dukan hannun Adeeb yake akan ya sake mai wuya,yana kakari

Kuka kawai fattu keyi tana daga tsaye jikinta na rawa ganin abinda ke faruwa,nan da nan jini ya ƙara balle mata sai zuba yake bul-bul yana bin ƙafarta.

Da gudu nanny ta shigo É—akin tana salati" magajin fada zaka kashe shi ,maza sake mai wuya " ta faÉ—a tana mai kama hannun Adeeb É—in.
Gaba daya hankalin Adeeb baya jikinsa.tsantsar kishi da tsanar rashad ke dukan zuciyarsa.sam yaki sake mai wuya.
Rashad sai kakarin mutuwa yake.

Ammi ce ta shigo É—akin arude tana zuwa ta kama fuskar Adeeb tana faÉ—in"my prince meye hakan?zaka kashe shine sakeshi mana ,nice fa na aikoshi"ammi ta faÉ—a cike da tsoron kar Adeeb ya kashe rashad.
Amma ko gezau Adeeb baiyi ba ,ba kuma alamun zai sake rashad É—in.

Rashad kuwa gaba daya jikinsa yayi kaishi dan ko hannunsa ma ya kasa dagawa bare ya kwaci kansa.
Chapter 26 · 0% Book details