← Book details Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 27

Sashe 14

Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannunsa ya sanya tare da kamo hannunta ya dawo da ita zuwa gabansa.
Saida ya É—an harareta kafin yace "menene kuma"ya faÉ—a cikin salon maganarsa kamar baya so.

Ahankali fattu ta nuna masa wasu matasa kusan su goma da suka tsaya suna kallonsu.tace "waɗan can ne ke kallona "kallon gurin matasan yayi,yaga yadda suka kafesu da idanu,kuma ba akowa suke kallo ba face fattu,nan da nan yaji wani irin ɓaci rai da ciwon zuciya ya turnuƙeshi,
Cikin hanzari ya maida fattu bayansa yana mai hararar matasan nan,zuciyarsa kamar zata fito dan tsabar ɓaci rai.gaba ɗaya yaji gurin yayi masa baƙi kirin,Bama yason tsayuwa agurin, dan haka cikin zafin nama ya fizgi hannun fattu suka fara tafiya daga gurin,mai saida wayoyin yana ta masa godiya da Allah ya kiyaye amma ko sauraransa baiyi ba.

Can wani guri ya koma tare da tsayawa ,shi kaɗai dai huci yake,dan me zasu tsaya suna kallon ta ,shifa saiyaga kamar ma ɗaya ƙirjin fattu yake kallo. Cikin sauri ya juyo tare da kallon fattu tun daga sama har ƙasa.ba wani abu daya bayyana ajikinta ,wanda za'ace shigarta batayi daidai ba ,saidai fa idan ka ƙura mata ido zaka iya gane ba bra ajikinta.
Lallai ke nan bata sanya bra ajikinta?

"Ke meyasa baki saka wannan abun ba kafin kisa rigarnan"
Ya faÉ—a cikin fushi da bakin rai.

Kallonsa fattu tayi cikin rashin fahimta dan bata gane me yake nufi ba,kawai saita sunkuyar da kanta ƙasa tace "kayi haƙuri Ni banga komaiba inda rigar ba"ta faɗa Muryar har ta fara rawa,alamun zata yi kuka.
Harya buÉ—e baki zaiyi magana yaji wayarsa na ringing,tsaki yayi kafin ya É—aya call É—in.
Shiru yayi na tsawon lokaci kafin yace "Yes i sawa them"ya kashe wayar .

Dan fitowa yayi daga gurin dasuke tsayen naga ya É—aga hannunsa .

Wata tsuleliyar mota naga ta taho gareshi,suuuuuu,baka ko jin ƙagarta,kallon ɗaya zakayiwa motar kasan anɓadda Naira agurin,farking motar tayi agabansa,kafin mai riƙon ya fito cikin sauri yana mai faɗin "your highly well come back sir"mutumin ya faɗa yana mai durƙusawa har kasa gaban Abeed.

Kafadar mutumin Abeed ya dafa tare da miƙar dashi tsaye,sannan ya ɗan rungumeshi yana mai bubbuga bayansa.

"Let go hisham"Abeed ya faÉ—a yana mai nufar motar ,da sauri wanda aka kira da Hisham ya budewa Adeeb motar ,shikuma ya shiga gidan baya ya zauna.

"Hamma " fattu ta faɗa cikin sauri tana mai ƙarasowa jikin motar ganin ya shige cikin motar yana ƙoƙarin barcinta.
Adeeb kuwa da gangan yayi banza da ita ,intaga dama ta ƙara so ta shiga motar,dan haushinta ya keji sosai ,ai da gangan ta wani tsaya har wasu ba zaune ke ƙare mata kallo.

Hisham ne ya kalli fattu yace "yan mata lafiya kuwa?
Shagwabe fuska fattu tayi tana kallon Adeeb tace "gurin hamma zani gashinan acikin nan"ta faÉ—a tana nuna mai Adeeb ,wanda ya wani É—auke kai .

"Yallaɓai this ...
"Let her in"Adeeb ya faÉ—a cikin katse Hisham .

"Yes sir"Hisham ya faɗa cikin bin umarni,ya kauce daga bakin ƙofar motar yana mai cewa fattu"shiga"

Da saurinta kuwa ta shige kusa da Adeeb ta zauna ,harda sauƙe ajiyar zuciya.
Ahankali ta sanya hannunta tare da riƙe gefen rigar Adeeb ta kalle- kallen motar.banda faɗuwa ba abinda gabanta keyi.

"Yallaɓai where are we going now"
Hisham ya tambaya cikin girmamawa.

"Abuja" Adeeb ya faÉ—a tare da kwantar da kansa jikin kujera ,ac na ratsa shi ta ko ina.

Nan Hisham ya kunna mota suka cilla sai Abuja.

Ko daga Abuja kuma sai ina ?

Ga dai Hajiya fattu cikin mota mai a.c ana baza idanu.

Muje zuwa ku biyoni sannu kan hankali.

Anty mammy ce

Mrs babi💘💘💘
[7/18, 9:07 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄

MICIJI NE 🪱🪱🪱

Na mammy kabeer
(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book

Page 25/26

________________Tafiya suke cikin motar Ba tare da kowa ya ƙara cewa komai ba,ba abinda ke tashi cikin motar dai sanyi a.c da daddaɗan kamshi, gefe guda kuma ƙira'ar sudais ke tashi cikin suratul mulk.

Gaba daya zuciyoyinsu,sun sami nutsuwa,irin wacce mai sauraron Alƙur'ani ke samun tago mashi da ita.

Adeeb yana kwance cikin kujerar, idanunsa alumshe ,ahankali yake ɗan motsa bakinsa yana bin ƙira'ar,al'adar sa kenan dama shi,inda yana cikin mota ,to karatun alƙur'ani yake sauraro. Yayin da can ƙarƙashin zuciyarsa yake jin wani irin farin ciki da annashuwa,duk da baisan tsawon lokacin daya ɗauka cikin yanayi na wata halittar ba,amma yana ji ajikinsa cewa yayi kewar ahalinsa fiye da yadda yake tunani.ba abinda yake fata da buri irin ace yaganshi kusa da abie da ammi.ko wane yanayi zasu shiga idan suka ganshi?
Tunanin da Adeeb yayi tayi kenan cikin zuciyarsa.hakan ya hana masa fahimtar halin da fattu ke ciki.wato ta takure jikinsa sosai,sai rawar sanyi takeyi, sosai sanyin motar ke damunta, ga wani irin yanayi na kewar baffanta dake taso mata, sosai ta ƙunaci Jikin Adeeb ,aƙoƙarinta na samun gurin da dataji ɗumi.
Ahankali ta ɗan zakuɗa kadan zuwa jikinsa,ta yadda har kafaɗarta na gugar tasa.kuma har zuwa wannan lokacin tana riƙe da gefen rigarsa.

Shikuwa Adeeb jin anÉ—an bugeshi ,yasa shi buÉ—e idanunsa ahankali, É—an juyowa yayi yana kallon fattu, wacce tayi lugus ajikinsa tana karkarwa.

"Ke matsa daga jikina"ya faÉ—a cikin salon maganarsa ba tare da ya motsaba.
Da sauri fattu ta É—an matsa ,daga jikin nashi,dan ita atunaninta dama yayi barcine.
Kallonsa tayi tare da marairaicewa tace "Hamma sanyi nake ji,kodai cikin ƙanƙara muke tafiya"ta faɗa zuciyarta ɗaya,tana ɗan gwabe fuska.
Kallonta yayi tare da harararta yace "dake baki san acikin ƙanƙara muke tafiyaba?ya faɗa cikin gatse.
Zato ido fattu tayi tare da dafe ƙirji,"na shiga ukuna Ni fattu ,dan Allah Hamma kayi min rai,mu canja wata hanyar wllh mutuwa zanyi idan naci gaba da jin sanyin nan"fattu ta faɗa cikin marairaita tana rawar sanyi,gaba ɗaya ta gama tsorata,idanunsa kuwa harya fara kawo ruwa.

Bamza Adeeb yayi da ita tare da maida idonsa ya rufe,wannan gaskiya ɓaci ƙauyencima akwai shirye atattare da ita,kamar ba tare suka shiga motar ba, ko ina taga alamun ƙanƙarama bare tace akanta suke tafiya?
Fattu kuwa ganin ya maida idanunsa ya rufe sai tsoro ya ƙara makata,da sauri ta cusa kanta tsakanin hannunsa da kujera, ta kara ƙanƙame gefen rigarsa tana kuka.
"Wayyo Hamma sanyi nakeji yana shiga cikin ƙashina ,jinina daskarewa yake" fattu ta faɗa cikin kuka,tsakaninta da Allah take kukanta.

Dafe kai Adeeb yayi tare da kallon Hisham yace "switch up that a.c" ya faÉ—a kamar baya so.
"Ok sir" Hisham ya amsa tare da kashe a.cn yana mamaki,yau yallaɓai ne da kansa yace akashe a.c?

Fattu kuwa ahankali taji ta daina jin sanyi da take ji,dan haka share hawayenta tayi tana mai cewa aranta."anya kuwa Hamma ba so yake ya kaini gurin yan shan jini su tsotsemin jini ba? Ahankali ta dago kanta tana kallon fuskarsa ,shagala fattu tayi da kallon kyakyakywar fuskarsa ,barin ma light pink lips ɗinsa da gashin baki yayi masa ƙawayan,ga gemunsa mai kyau sai sheƙi yake,hanci kuwa kamar wanda aka ɗora masa,gaskiya Hamma akwai kyau ,inama nike da kyansa,aikuwa danasha gayu.

"Ke meye kika ƙuramin ido haka?karki cinyeni" Adeeb ya faɗa yana mai tsare fattu da idanunsa masu tsananin haske.
Dan duk yadda ta ƙuresa da ido yana kallonta ,dan ba duka ya rufe idon nashi ba .

Ɗan zabura fattu tayi ta matsa baya tana soso kai,dan ba ƙaramin kunya taji ba,ashe yana kallonta ta ƙuresa da ido haka? wayyo Allah Ni fattu .ta faɗa cikin ranta tana mai kwantar da kanta jikin kujera cikin kunya.

Tun daga lokacin ba wanda ya ƙarayin magana a cikinsu.
Adeeb yana cikin tunaninsa yaji fattu ta langaɓo kansa,dan dubawa yayi saiyaga ashe ma barci tayi.kafeta yayi da idanuwansa yana kallon zallar kyau irin na fattu,duk da ƙarancin shekarunta ,amma Allah yayi mata baiwar kyau,irin kyanda sai kana kallon mutum kake ƙara ganin kyan nashi .
Gyara mata kwanciyar yayi agefen kafaÉ—arsa ,duk da yadda yake jinsa atakure,kasancewar kusancinsu yayi yawa ,amma haka ya daure ya barta akan kafaÉ—ar tashi taci gaba da barcinta.

Fattu na cikin barci taji ana dan taffing kumatunta, Ahankali ta buÉ—e idanunta da sukayi mata nauyi saboda barci.
"Dagani malam duk cin batani da yawun barci ko" Adeeb ya faÉ—a yana hararar fattu
Wacce ke kif-kifta idanunta tana mai daga masa kafaÉ—a,kallon kafaÉ—ar tashi tayi,amma ita bata wani ga yawu agurin ba.
Suna fita daga Motar fattu ta gansu kusa da wani ƙaton jet ,Aida sauri ta kamo hannun Adeeb ta rike ƙam cikin nata tana mai zaro ido.
Fizge hannunsa Adeeb yayi yana hararar fattu "stop touching please" ya faÉ—a yanayin gaba binsa.
Da sauri fattu ta mara masa baya,tana binsa ƙafa ƙafa.tab yaushe zata tsaya kusa da wannan abu mai kama da girman duniya?haka kawai ya fado kanta ta mutu ?

Wani farin Balarabe ne ya fito daga cikin wata ƙofa,dake ɗan nesa da inda jet ɗin ke tsaye.
Da gudu naga ya taho ya ruƙunƙume Adeeb yana sunbatarsa,kuma yana hawaye.
"Habeebi ina ka shiga ?me yasameka?kasan irin tashin hankalin da muka shiga?kowa na gida yana cikin damuwa,abie yana nan akwance ba lafiya tunda aka rasaka"Balarabe ya faÉ—a cikin harshen larabci.
Murmushi kawai Adeeb yayi yana mai shafa kan wannan balaraben ,sannan yace " where is the imam?
Cikin share hawaye mutum yace "yana ciki kai kawai muke jira.
Kallon fattu Adeeb yayi yace "jirani ana karki biyoni" ya faÉ—a cikin hade fuska.kafin yayi gaba.
Da sauri fattu ta kamo hannunsa cikin marairaita tace "tsoro nakeji Hamma dan Allah karka gudu ka barni"ta faÉ—a cikin kwabe fuska.
Zare hannunsa kawai yayi baice komai ba suka shige cikin dakin da wanann balaraben ya fito. Zama fattu tayi akan wata kujera dake gefen ta,da alama kujerar sassaƙata akayi dan zama agurin,tagumi tayi rungume da yan kayanta,tunani take yanzu idan Adeeb ya gudu ya barta anan yazatayi? Gurin wa zata?dan ita dai yadda take ganin garin nan da zungura- zunguran gidajen dake cikin garin ,zaiyo wahala idan ba shan jini akeyicikin gidajen ba.shikenan ba ita ba ƙara ganin baffanta.
Daga kanta tayi ta kalli inda aka daka motar da suka zo cikinta amma watan bataga motar ba,saidai taga wasu tarin motocin can gefe guda arufe da wani abu.
Chapter 14 · 0% Book details