← Book details Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 27

Sashe 15

Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ƙila duk waɗanda aka kawo su cikin motocin can an shanye musu jininsu.yanzu itama haka za'a shanye nata jinin idan Hamma ya gudu?"wayyo ni fattu naga rayuwa "ta faɗa tana mai leave fuska da waige waige .
Shikuwa Adeeb koda suka shiga ƙofar nan,
Kusan minti talatin suka ɗauka cikin dakin kafin suka fito, ,lokacin fattu hatta fara kuka, tana ganinsa taji wani sanyi cikin ranta,da hanzarin ta ta miƙa tare da nufarsa tana kuka,tana zuwa ta kama hannunsa cikin kuka take cewa"Hamma harba fara kuka ,nayi tunanin gudawa kayi ka barni, anan ado a shanye min jinina, dan Allah Hamma karka ƙara tafiya ka barni" fattu ta faɗa tana mai ɗora kanta akan damtsen hannunsa. Wani irin yanayi na tausayinsa Adeeb yaji yana ratsa zuciyarsa,Allah Sarki,yasan ahalin yanzu bata da wani gata saina Allah saikuma shi,shi kaɗai ta sani,zaiyo iyakar ƙoƙarin sa ,wajen kula da ita har su cimma burin su. hannunta kawai Adeeb ya kama , tare da nufar cikin jirgin nan.
Noƙewa fattu ta farayi cikin rawar jiki tace"Hamma na tuba Dan Allah karka sani cikin wannan abun mai kama da kifi" fattu ta faɗa tana mai ƙoƙarin zare hannunta daga cikin nashi.

Tsayawa yayi tare da kallon wannan balaraben yace tareeÆ™ ka shiga ciki "ya faÉ—a cikin harshen larabci.
Jinjina kai tareeÆ™ yayi tare da kama É—ayan hannun Adeeb ya sunbata kafin ya shige cikin jet É—in.

Kallonta Adeeb yayi yaga yadda gaba ɗaya ta firgice,sai ƙoƙarin zame hannunta take cikin nashi.

Ahankali ya sanya hannunsa ya kawota jikinsa,yayi mata side hug,kana yace " ki nutsu kinji,ba abinda zai miki zamu tafi gidane acikinsa" ya faÉ—a yana mai shafa kanta.

Jinjina kai fattu tayi tare da cewa"Ni bazan bikaba Hamma kamaida Ni gurin baffa ,bazan shiga wannan abunba tsoro nakeji,kifine da,muna shiga haɗiyemu zaiyi Hamma"ta kai ƙarshen maganarta cikin kuka.

Murmushin Adeeb yayi akaro na farko tun tasowarsu daga Kano,wai haɗiyesu zaiyi ,kifine.kai wannan yarinyar akwai ƙauyanci.

Ganin dai da gaske fattu atsorace take, sai kawai ya juyo da ita zuwa gabansa ,bai jira komai ba ya haɗar da jikinsa ya rungumeta cikin faffaɗan ƙirjinsa,ahankali yake shafa kanta zuwa kafadunta .
Shiru fattu tayi sakamakon wani irin nutsuwa mai cike da sa annashuwa dataji tana ratsa dukkan sassan jikinta,luɓ tayi cikin jikinsa ta daina wannan rawar jikin,idanunta kawai ta kumshe tana shaƙar daddaɗan kamshi da Adeeb keyi.
Kusan minti uku Adeeb ya bata ajikinsa,yayinda shima yake jinsa cikin wani irin yanayi na samun nutsuwa da peace of mine ,ji yake kamar suyi ta zama ahakan, amma tunowa da yayi da abinda ke gabansa yasashi saurin ɗagota daga jikin nashi,ƙara komawa fattu tayi ta kwantar da kanta akan ƙirjinsa,ba tare da tasan tayi hakan ba,.cibiya ya karatu kafin yace "to dagamin jiki karki karyani"ya faɗa daidai saitin kunne ta. Wani yuuuuuuu fattu taji ,jiri na neman dibanta, lokacin da iskar bakin Adeeb ta bugi kunnenta,da sauri ta rike damtsensa tana mai runtse idanunta,saida suka sake ɗiban minti kusan biyu,kafin Adeeb ya ɗagota,wanna karon bayi musu ba,saidai kanta na ƙasa cikin jin kunya.
"Ya isheki haka ko kina don daÉ—i?"Adeeb ya faÉ—a yana kallon fuskarta.

Shiru tayi kanta a ƙasa ba tace komai ba.

Hannunta Adeeb ya kama suka fara taka matakalar. Taku ɗaya biyu kawai fattu tayi luuuuuu zata daɗi ƙasa ,da sauri cikin azama Adeeb ya ruƙota ,yana mai zato idanu waje.

Fattu kuwa ji tayi kanta yana juyawa sosai,tace "Hamma ka rikeni zan faÉ—i "ta faÉ—a tana mai kumshe idanunta.

"Ina tare dake ba abinda zai sameki"Adeeb ya faÉ—a ,yana mai É—aya fattu kamar ya É—auki jaririya ya shige cikin jet din.

Wow wato shi kansa cikin jet ɗin abin kallo e ,tsayawa fasalta yadda ya tsaru kuma bata lokacine,na barku kawai ku ƙiyasta tsaruwar jet ɗin.

Sin yanufa ya zauna tare da rungume fattu cikin jikinsa,yana shafa kanta ahankali.
Belt ya É—aura musu kafin ya É—anan wani É—an guri saiga kujerar ta mike ,yadda mutum zai iya kwanciya akai.
Wata har danja ya latsa ,nan danan mai tuƙin wato tareeƙ ya tada jirgin sukayi kula sukayi sama.

Ƙara gyarawa fattu kwanciya Adeeb yayi ajikinsa yana mai kallon fuskarta dake cike da tsoro,idanunta arufe gam, da hannunta shima ta rukunkume Adeeb dasu, idanunta kuma na tsiyayar da ruwan hawaye .

Ahankali Adeeb ya sanya hannunsa yana mai share mata hawayen bakinsa ya kai daidai goshinta kamar zaiyi mata kiss saikuma yayi saurin dauke kansa .

Ajiyar zuciya Adeeb yayi yana mai kallon sararin samaniya cike da jin wani irin shauƙi cikin zuciyarsa

Manage please my people,

Banda caji wllh nefa ya sami matsala.

Mrs babi ce💘💘💘

Share and comment fisabilillah

More comment
More typing.
[7/19, 7:01 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄

MACIJI NE 🪱🪱🪱

Na mammy kabeer
(Anty mammy

Elegant online writers📚📚

Free book

Page 27/28

https://www.facebook.com/groups/2803452939899949/?ref=share

________________Tafiya suke cikin sararin samani,yayin da Fattu ke ruƙunkume da Adeeb jikinta naci gaba da rawa,kuma har lokacin idanunta akulle suke.
ÆŠan juyowa Adeeb yayi yana mai kallonta ,shi mamakin tsoro irin na fattu yake,sam baiga abun tsoro ahawa jirgi ba,dubi yadda ta wani uzzurawa kanta,ko idanu ta kasa buÉ—e wa.
Ni kuwa nace malam Adeeb fattu fa ko ganin jirgi baya taɓa yi ba ,bare ta hau,ai dole ta shiga cikin cakwakiya,akaranta na farko.

Kallon fuskarta Adeeb keyi kamar bai taɓa ganin taba,haka kawai yake jin wani bakon al'amari tare dashi, jin yadda fattu ta ruƙunƙumeshin nan ,sai yake jin hakan yayi masa daɗi sosai,saidai yana tsoron abinda zuciya da gangar jikin sa ke ɓuƙatar aikatawa,idanu ya kirawo lips ɗinta ƙuri,cikin wani irin mugun son ya sunbacesu,gabansa sai bugawa yake,har wani lasar lips ɗin da yake ,yana hasko yadda zai sunbaci lips ɗin fattun.iyakar ƙokari Adeeb yayi dan hana kansa aikata abinda zuciyarsa ke tsananin muradi, amma ya kasa,dan jinsa yayi gaba ɗaya yanayinsa ya sauya ,ahankali cikin mugun son isar da saƙon zuciyarsa ya nufi ɗan bakin na fattu, har wani rawa bakinsa keyi,
Yana gan da kai bakin nasa cikin nata ne ,fattu tayi waral!da idanunta,ma'ana ta buɗe idanun nata ba zato ba tsammani,karaf kuwa idanunsa ya sarƙe dana juna,da sauri Adeeb ya runtse idanunsa tare da kawar da kansa can gefe,saidai bai daga daga rankwafowar da yayi ba,jikinsa gaba daya yana manne dana fattun,wani irin abu yakeji mai kama da mayen karfe ,yana fusgarsa zuwa ga aiwatar da burinsa, kiss fa only kiss Adeeb you can do it ,dan ka samawa kanka mafita daga yanayin da kake ciki.
Zuciyar Adeeb ke bashi wannan shawarar,ahankali ya ƙara bude idanunsa wanda suka fara sauya yanayi daga fari tas zuwa wani irin sirkin jaaa da wani ratsin pink.

Kallon fattu yayi wacce itama shi take kallo tana wani rarraba idanu,Ita dai batasan me yake nufi ba,taga ya kwanto jikinta ne ,ƙila ahaka ake tafiyar ,amma kuma me yasami idanunsa haka,idan bata mantaba ,yanayin da idanunsa ya shiga yanzu,kusan kalar da idanunsa yake ne lokacin da yake macijinsa, kodai macijin zai ƙara zama ne?na shiga uku na idan yazama maciji yanzu yazanyi?ina zamuje cikin wannan halittar mai kama da kifi?nan da nan tsoro ya kama fattu ƙara rikoshi tayi sosai cikin muryar tsoro tace "Hamma menene?dan Allah karka ƙara zama maciji kai kadai nake dashi,idan ka koma maciji ya zanyi,waye zai fitar dani daga wannan cikin kifin da muka shi?ta faɗa cikin salon shagwaɓa taba mai zubda hawaye.

Da ƙarfin gaske Adeeb ya runtse idanunsa, yana mai furta "ya Salam wannan yarinyar zata kashe ni fa"dan yanayin yadda tayi maganar ba ƙaramin tasiri yayi akan Adeeb ba,hakan saiya ƙara masa jin wani iri ajikinsa,gani yake kamar da gangan tayi hakan ma.
Kansa banda juyawa ba abinda yake,yayinda zuciyarsa ke ta bashi shawarar kawai ya sunbaci fattun .cikin rashin sanin abinyi Adeeb ya ɗora bakinsa kan na fattu,ba tare da ɓata lokaciba ya fara kissing ɗinta kamar ya sami lolli pop,zaro idanu fattu tayi cike da tsantsar tsoro da mamaki,meye hakan kuma Hamma keyi?me yasa yake shan bakina?kodai shima yana cinye mutane ne?shikenan Ni fattu naga ta kaina ,wayyo Allah na,daga cikin fiki saikuma shanye baki?nan da nan fattu ta fara rawar jiki fiye da da,cikin zuciyarta tana take ta faman haure haure da ƙoƙarin ture Adeeb,amma kuma azahiri ta kasa koda ɗaga dan yatsanta ne bare tayi yunƙurin kwacewa.

Shikuwa Adeeb É—ora bakinsa kan bakin fattu keda wuya ,gaba É—aya haddarsa ta zube,tuni ya nemi inda kansa yake ya rasa,kissing É—in bakin fattu kawai yake kamar Mayunwacin zaki.

Kusan minti shida zuwa bakwai Adeeb na abu É—aya,cikin kwancewar kai da rasa tunani,fattu kuwa tun tana jin abinda yakeyi kamar waiwayi yake mata har ta fara jin wani azababben zafi da raÉ—aÉ—i ,dan ji tayi kamar zai tsinke mata lips,tuni ta fara kuka tana É—an bubbuga damtsen hannunsa.

Hankali da tunanin Adeeb ne suka dawo jikinsa lokaci É—aya,kuma ya fahimci abinda yake aikatawa da Fattun, cikin wata irin azama da hanzari ya dago kansa tare da cire bakinsa daga cikin na fattun.
Da sauri ya zareta daga jikinsa yana mai mikewa cikin hanzari ya nufi wani daki,yana layi kamar É—an maye.
Chapter 15 · 0% Book details