← Book details Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 27

Sashe 17

Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kayan data cire É—in ta dauka tare da rikews ahannunta tana tsaye ,tana waige waige kallo É—aya zaka mata kasan afirgice take.

Bude É—akin Adeeb yayi bayan yayi noking yaji shiru,
"Masha Allah " shine abinda Adeeb ya iya faÉ—i lokacin da yayi arba da fattu cikin kayan nan.

Shima yana sanye da wata farar jallabiya ajikinsa da hirami akansa.yayi kyau sosai cikin shigar tasu ta larabawa.

Cikin ɗakin ya nufa yana mai jure fattu da idanu,ita kuwa kanta na ƙasa,riƙe da jiƙaƙkun kayanta.

Cikin wata irin murya mai kama da mutum na jin barci Adeeb yace "Hulwa"
Ahankali fattu ta daga kanta tana kallon bayan Adeeb É—in dan gani ta ina hulwar zata fito.....

DOMIN SAMUN LITTAFIN COMPLETE SAI KU TAƁA BULUN RUBUTUN DAKE KASA 👇🏻👇🏻👇🏻

https://www.aihausanovels.com.ng/2022/07/macijine-shi-page-21-22-hausa-novel.html

Muje zuwa masu karatu,

Mrs babi ce💘💘💘
[7/21, 11:20 AM] Abue Saleh AlQuyraemey: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄

MACIJI NE🪱🪱🪱

Na mammy kabeer
(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book

Page 29/30

_________________Cikin wani irin salo da murya mai maka da yana jin barci,Adeeb yace "Hulwa"
Ahankali fattu ta dago kanta tana mai kallon bayan Adeeb É—an ganin ta ina hulwar zata fito.

Rarraba idanu take ,amma bataga kowa ba,ikon Allah ko ina hulwar take ?bisani Banga kowa abayansa ba ,kuma ba kowa cikin É—akin nan, fattu ta faÉ—a tana mai waige bayanta ,dan ita dai bataga hulwa anan ba.
Duk abinda take Adeeb na kallonta,kuma ya gane me take nufi,wato suna daya faÉ—a shine bata ganeba,take neman mai sunan.
Juyowa fattu tayi ta kalli Adeeb É—in cikin rashin fahimta tace "Hamma Ina hulwar take ?naga ba kowa cikin É—akin nan ?
Kallonta yayi tare da É—an zafi ido yace "yanzu ke bakuga hulwar tawa ba anan?" Ya faÉ—a yana mata kallon tuhuma.
Waigawa fattu ta sakeyi bayanta,amma wllh ita kam bataga kowa ba,juyowa tayi tace "alƙur'ani banga kowa ba" ta faɗa tana ɗan buɗe hannayenta dan tabbatar masa da cewar ba kowa aɗakin.

Yaɓe baki yayi yace "matata ce hulwa kuma gata nan akusa dani idan ke bakya ganinta toni ina ganin abata,ya faɗa yana ɗan kallon kusa da gadon da fattu ke tsaye.

Ai fattu najin haka wani irin tsoro ya kamata,da gudu ta watsar da kayan hannunta ta taho gareshi ,tana zuwa ta biye abayansa tana tsuma, ahankali take masa faɗa cikin kunnensa,"aradu Hamma aljanna kake gani ba matar ka ba,dan ba kowa acikin ɗakin nan,Ni dama tun dazu nakewa dakin kallon na aljanu,dan wannan ɗakin baiyi kama dana mutane ba ,kyanshi yayi yawa aradun Allah" fattu ta ƙare magannarta cikin kunne Adeeb da sunan tana masa raɗa dan kar Hulwa tajisu.
Tunda ta fara masa magana akunne ya wani lumshe idanunsa,har cikin ƙwaƙwalwar sa yake jin sautin maganarta, yayi da yake jin tana zaga dukkan ilahirin jikinsa, wani yuuuuum yakeji ajikinsa har kamar zai faɗi.ahankali ya buɗe idanunsa,jin ta kai aya akan maganar tata. Wacce shidai yaji farkon,amma sam bai fahimci me take fadi ba daga ƙarshen.
Yana shirin yin magana ne yajiyo ƙarar na'urar sanarda mutum yayi bako tana faɗin tareek na jikansa afalo.

Dan haka ya fasa yin maganar ,kawai saiya juyo yana kallon fattun da tunanin idanunsa,ahankali ya buɗe baki da gyara yace "wait for me here I will be back" ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe kofar,ai carab fattu ta kama hannunsa ta riƙe cikin nata gam!tana kallonsa.
Kallonta yayi shima da nuna alamun menene?
Turo baki tayi tace " Ni ma zan bila Hamma,dan naji ka kira sunan wasu mutanen da yawa,bayan waccan hulwar Ni wllh tsoro nake ji" fattu ta faÉ—a tana mai kallon fuskarsa.

Hannunsa data rike cikin nashi,yabi da kallon,kafin ya ɗago yana kallonta,waima shi yaushe ya kira sunan wasu mutane kuma?ahankali ya sanya hannu ya zare nata hannun daga nashi kafin yace"bazaki bini ba, kuma Ni nace ne ki Kijirani kawai"ya faɗa yana harararta tare da bude ƙofar,yana sanya ƙafarsa waje fattu ma ta fito jikinta sai rawa yake,juyowa yayi yana kallonta fuska ba walwala yace " koma"
Marairaicewa fattu tayi kafin tace " wllh tsoro nakeji,dan Allah kaje dani,wannan hulwar fa tana ciki" harara ya Banka mata kafin yace "get in I said ,hulwar ta cinyeki" ya faɗa yana turata ciki dakin yana ƙofar ya kulle.
Hauka yake yaje da ita gurin tareek cikin wannan shigar?ai wllh idan tareek ya ganta ahana,inaga saina kusan mutuwa dan baƙin ciki.cewar Adeeb kenan yana nufar madaidaicin falon daya gaji da hadewa,zama yayi yana kallon tareek ɗin cikin yanayinsa ya haɗe fuska.
"Yallaɓai me yake faruwa ne ?naga ka shigo cikin tashin hankali?"tareek ya faɗa cikin harshen larabci yana kallon Adeeb ɗin.
Ajiyar zuciya Adeeb yayi kafin ya jingina kansa jikin kujera ,kusan minti biyu kafin ya buÉ—e baki dagyar yace " ta tsoratane ,shine ta suma" shima cikin harshen larabci yayi maganar.

"Ya Salam, yallaɓai koka sanar da ita wanann maganar ne?"

"No ban faÉ—a mata ba" cewar Adeeb .
Shiru suka ɗanyi na wani lokaci, kafin tareek yace "yallaɓai abie baisan da dawowarsa,bansanar da kowa ba kamar yadda ka buƙata"
ÆŠagowa Adeeb yayi daga kwanciyar da yayi jikin kujera,kafin yace " Yes,bana son ya sani yanzu,sai dare yayi zamuje gurinsa, ka shirya komai da komai,yanzu zanje na rage suman nan ne" Adeeb ya faÉ—a yana mai shafa dogon lallausan gashin kansa zuwa gefen fuskarsa da gemunsa.

"Ok me kake ɓukata yanzu yallaɓai " tareek ya faɗa cikin ladabi.
"Kaje ka kawo mata kayan buƙata duka, sannan ka tahomin da wayoyi ayi duk abinda ya kamata" yana faɗin haka bai jira me Tareek zaiceba ya miƙe tare da nufar wani ɗakin da ban.

Fattu kuwa Adeeb yana kulle ƙofar taji wani mugun tsoro da fargaba, wayyo Allah,yanzu ya zanyi idan hulwar nan mai shan jini ce ? Kuma gashi bana ganinta ?
Zama tayi agurin tare da ƙanƙame jikinta tana kuka sosai harda shashsheka,Allah Sarki baffanta ,ko wane hali yake ciki yanzu?ko wane hukunci mai gari ya ɗauka akansa? Allah dai ya kare mata baffanta Aduk yanayin daya tsinci kansa.

Tana nan zaune sai waige waige take ,ta gaji sosai ga yunwa ,ga barci,gashi tana sonyin salla dan rabonta da abinci tun wanann jakwalkwalon da Hamma ya bata awanann gidan.tana zaune shiru kawai taga wasu labulaye masu suna saukowa ahankali daga kowane bango na ɗakin.wata zabura da tayi cikin tsoro ta kwallah ihu tana mai komawa tsakiyar dakin ,banda rawa ba abinda jikinta keyi"wayyo Allah ma hulwa dan Allah kiyi haƙuri,karki cinyeni ,wllh ba abinda nayi miki,Hamma ne ya kawoni gidanki"abinda fattu ke fadi kenan tana rawar jiki da karkarwa,tana juye juye atsakiyar dakin,ta kalli wannan bangon ta kalli wancan..
Sukuwa labulaye ,sai sauka suke kasa,kuma basu tsayaba ,saida suka dire har aƙasa.

Sai kuma taga hasken É—akin ya sauya kala ,daga farin haske zuwa dim light,kuma daga can gefe wata bishi sai walwali take .
Kuka sosai fattu keyi cikin tsoro da rashin sanin abinyi,yaukan yasan kwananta kawai ya kare kamar wacce akace kalli can ,tana juyowa wajen da sif É—in nan take ,kawai taga abubuwa kamar malam bude mana littafi, suna ta yawonsu ajikin sif É—in.
Wata irin numfashi fattu ta jaa da ƙarfi,kafin kuma tayi ƙasa sululu ta faɗa kan gadon asume.

Shikuwa Adeeb yana shiga wannan dakin kwanciya ya ɗanyi akan lafiyayyen gadon dake ɗakin,so yake ya ɗan huta,dan gaba ɗaya yarinyar nan ta gama gajiyar dashi ,yana kwanciya sai yayi tunanin ai baiyi Sallah ba,dan haka tashi yayi tare da sake wanka sannan yayi Sallah,ya koma toilet ɗin ya gabata fuskarsa,sosai naga kyansa ya ƙara fitowa ,ashema kyanshi ya wuce yadda nake tunani,dan kallo daya idan kayi masa ,kuma kuka haɗa idanu ,bazaka iya ƙara yarda ku haɗa ido ba,dan yana da wani irin kwarjini da haiba.
Wannan karon ƙananan kaya ya sanya,riga da wando ne na jins, rigar light blue ce ,yayinda wando kuma ya kasance blue ne sosai.kansa ya taje, sannan ya fashe jikinsa da tauraruwa masu masifar ƙamshi, danaga ya buɗe wata loka guda ,duka turarukane acikin lokar tunda ga sama har ƙasanta.
Wata lokar ya buÉ—e naga agoguna ,masu azabar kyau da tsada,wani agogon kwal ya dauko ya daura ahanannunsa, sannan ,sannan ya buÉ—e bangaren takalma,nidai gefe na koma na zama yar kallo.dan abun yafi karfina, daki guda duka na kayan Amfanin mutum É—aya?wani aikin sai amasar.

Yana gama shiryawa ,dakin ya dauki wani ƙamshi mai rikitarwa da sanya nutsuwa,kanshi ya taje sannan ya shafa mayuka kusan kala biyar akan nashi,tuni kan ya dauki walwali da sheƙi,

Fitowa yayi daga É—akin ya nufi kitchen,masu karatu kuzo kuga kitchen ,aini kodaga nam aka barni ,tabbas na more,dan iya tsaruwa kitchen É—in nan ya tsaru.

Wani irin tea naga ya haÉ—a ,sannan ya siya kwai tare da imdomie,shikam arayuwarsa baida wani abinci daga tea sai imdomie saiko nama,

Yana gama haÉ—awa ya tsaya yana kallon abincin daya haÉ—a É—in cikin wani kayataccen faranti, mamakin kansa yake ,wai yau shine da haÉ—awa wata abinci,kuma shi zai kai mata da kansa.koda yake ai itaÉ—in amanar sa ce,kuma dole ya kula da ita.
Chapter 17 · 0% Book details