← Book details Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 27

Sashe 18

Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ÆŠaukar tiren yayi ya nufi dakin da Fattun ke ciki,
Kwankwasawa yayi kafin ya dannan wani guri sai ga kofar tana komawa gefe guda,harya buÉ—e gaba É—aya É—aya .
Kansa ya kunna cikin dakin yana mai kallon yadda komai ya canza,wannan alamun e na lokacin barcinsa yayi ,dama haka dakunan aka shiryasu suke sauya komai da kansu,idan lokacin barcin rana ne kona dare ,kokuma safiya .
Ajiye tiren yayi yana mai kallon ta ina zai hangi fattu,can ya hangota kwance akan gado ,saidai da'alama kwanciyar bata daɗi bace, dan haka da sauri ya nufeta, kamar yadda yayi tsammani kuwa suma tayi,cike da fargaba ya ɗagota yana mai kiran sunanta ,"Hulwa !hulwa!!amma bata ko motsaba,ajiye ta yayi tare da bude fridge ya dauko ruwa mai sanyi yana yayyafa mata.amma bata ko motsaba ,wai wannan suman na menene haka?duka duka yaushema ta dawo hayyacinta ne ?gashi yanzu ta ƙara suka.
Huci kawai yake yana kallon fuskarta,zuciyarsa kamar zata fasa ƙirjinsa ta fito,sam baya ƙaunar ganin fattu cikin wani mugun yanayi,waima menene yayi silar wannan suman nata ne?kallon dakin yayi yana mai jinjina kai ,ba shakka tayi arba da yadda dakin nan ke sauyawa ne,wani irin runtse idanunsa yayi tare da dafe kansa,duk laifinane dana fita da ita da duk haka bata faru ba.bude idanunsa yayi wanda suka juye zuwa na macizai sak, ahankali jikinsa ya kama wata irin girgiza yana hayaƙi,kan kace me saiga ɗakin ya turnuƙe da hayaƙi, kusan minti biyar dakin yana wanann yanayi hayaƙi da wata irin ƙara,kafin hayaƙi ya baje, saiga wani murtukeken maciji mai girman gaske ya fasa kai yana huci.
Cikin tafiyar macizai macijin nan ya fara sauƙa daga kan gadon ,bangon dakin ya kama tare da fara lauye jikin wanan haɗaɗdun labulayen yana nannadesu tare da fesa musu wani irin ruwa daga bakinsa,da zaran ya fesa ruwan sai kaga labulen yana hayaƙi tare da murmushewa, haka yayi tayi saida ya bata gaba dayan labulayenan sannan ya fara bugun kwayayen dakin dake bada hasken nan mai ban sha'awa da jelarsa.tas saida ya gama fashesu, sannan ya nufi kan gadon,yana zuwa ya hau kan cikin fattu dake kwance ,cikin halin suma,zagayeta ya farayi tare da shigewa ciki rigarta sosai,yana goga mata sanyin dake jikinsa.

Aikuwa sanyin yana fara ratsa fattu ,ta fara bude idanunta ahankali,tana mai dafe kanta tare da yamutse fuska.
Abu taji yana fitowa sululu daga cikin rigarta,da sauri ta tashi zaune tana mai daga rigarta sama,daidai lokacin shikuwa macijin ya gama fitowa daga jikin nata.
Saƙare fattu tayi tana kallon macijin cike da tsantsar mamaki,shima macijin kallonta yake ido cikin ido.

Masu karatu meke faruwa ne?
Wannan macijin kuma waye?

Shin Adeeb dama bai daina zama macijin ba?

Muje zuwa takuce anty mammy

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Danna Bulun Rubutun Dake Kasa 👇🏻👇🏻

https://www.aihausanovels.com.ng/2022/07/macijine-shi-complete-novel.html

Mrs babi💘💘💘

Share and comment
Fisabilillah.

More comments
More typing.
[7/22, 6:06 AM] Aishat Anty: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄

MACIJI NE🪱🪱🪱

Na mammy kabeer
(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚
https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din👆🏽

Free book

Page 31/32

_________________Saƙare,fattu tayi tana kallon macijin cike da tsantsar mamaki, kamar yadda macijin ke kallon fattu shima ido cikin ido.

Ahankali fattu ta lumshe idonta,tana mai ambaton sunan Allah,abin da ya bata mamaki shine,sam bataji tsoroba, saima bin jikin macijin da tayi da kallo,tabbas wannan macijin ta ne na yar ruga, kenan hakan na nufin Hammanta ne ya ƙara zama maciji? innalillahi ,yanzu yazatayi kenan?awane matsayin take idan bai dawo mutum ba?
Ahankali ta furta "Hammana" hawaye na zubowa daga cikin idanunta.

Shikuwa macijin yana ganin hawayen nan nata,ya taho zuwa gareta,yana zuwa ya hau kan cinyarta tare da nannaÉ—e jikinsa ya É—ora kansa akan kafaÉ—unta.

Lumshe ido fattu tayi cikin kuka tace " dan Allah HAMMA karka zauna cikin wannan yanayin,bazan iya rayuwa Ni kadai cikin wannan gidan mai aljanu ba, dazuma saida Hulwarka tazo ta tsoratani, gaba daya ta sanja duniyar wannan dakin ,ya koma wata kala,kalli kagani yanzu yadda ya koma,Hamma inajin tsoro"fattu ta faÉ—a tare da É—ora hannunta akan macijin tana shafawa.
Dagowa macijin yayi tare da zuba mata idanu,itama kallonsa take hawaye na zubowa daga idanunta. Jikinta ya fara zagayewa yana yana nannaÉ—eta,kafin kuma yayi baya da ita akan gadon,kwanciya fattu tayi tare da runtse idanunta .
Ita kam tariga ta gama sallama wa rayuwa, tasan idan har macijinta bai dawo mutum ba to mutuwa zatayi, ahalin da ake ciki yanzu tana jinsa ne har cikin ranta,kome takeyi shi take gani,ba abinda take bukata akullum kamar tajita kusa dashi,ta san duk ransa wani ya ganshi matsayin maciji ,to za'ayi ƙoƙarin kashe mata shine,wanda tayi imanin duk randa aka kashe Hamma, to tabbas da gawarsa za'a binnesu.

Shikuwa maciji bayan ya kwantar da fattu saiya zare jikinsa daga nannaɗetan da yayi,sannan ya kamo bargon dake kan gadon ya lullaba ajikin fattu,duk abinda yake kallonsa fattu keyi cike da tausayawa,ace mutum yana komawa wata da bar daban?kuma mai haɗari wacce kowa ke gudunta.saukowa yayi daga kan gadon tare da tsayawa daga can gefenta yana kallonta, itama kallonsa take ,kusan minti uku suna kallon juna,yayin da fattu ke zubda hawaye,juyawa yayi tare da nufar ƙofar dakin.
"Dan Allah Hamma ka dawo mutum,kada ka tafi ka barni,ina don kasancewa tare da kai,bani da kowa awannan sabuwar duniyar saikai"abinda fattu ta faɗa kenan lokacin da taga yana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin.

Aikuwa tsayawa yayi kamar wanda yake sauraron me take faÉ—i .saida ta kai aya azancenta,kafin ya kalleta da idanunsa masu naunuka daban daban,sannan ya fice daga É—akin.

Kuka sosai fattu ta fashe dashi,tana daga kwancen nan,shikenan komai yazo mata ƙarshe,idan Hamma ya tafi ya barta,ita ahalin yanzu ma, ta fara tunanin kodai duniyar aljanu ya kawo ta?
Haka tayi ta kukanta tana daga kwance har barcine wahala yayi gaba da ita.

Shikuwa Adeeb yana fita kai tsaye dakin daya baro ya nufa ,ahankali yake jan jikinsa , harya kai kan gadon ,hawa yayi tare da kwantawa lamo kamar baya nunfashi,rufe idanunsa yayi yana nishi da gyar, kafin kuma jikinsa ya kama girgiza sosai yana hayaƙi, sosai dakin ya turnuƙe da hayaƙi kafin ya washe.

Ikon Allah Adeeb na hanga kwance akan gadon nan,ya duƙunƙune jikinsa,sai rawa yake kamar mai jin sanyi,ahankali ya ɗaya hannunsa dake ta faman rawa ya dage kansa,yana mai yamutse fuska ,da alama kan ke masa ciwo,kusan minti goma ya ɗauka cikin wanan halin kafin naga ya miƙe jiki ba kwari,ya nufi toilet ,wanka yayi tare da sake kaya,ya fito cikin fara tass ɗin jallabiyya.
Zama yayi akan wata kujera dake gaban gadon,kujerar tsabar kyanta ,kai kace da zallar kwal akayita.sai ƙamshi yake bugawa, kallon ɗakin yake yana mai mamakin shidai yasan ya fita zuwa kitchen kuma har yayi girki,bayan nan kuma ya nufi dakin Hulwa, kuma...

Da sauri ya mike yana mai zafi ido,tabbas asume ya ganta aÉ—akin ,amma kuma me yasa shi yaganshi ana ?me ya dawo dashi É—akinsa.
Da sauri ya nufi ƙofa yana ficewa daga dakin,saidai yana fita kafin ya kai dakin nata,yaji sanarwar zuwan tareeƙ,kallon kofar Tata yayi sannan ya nufi bakin ƙofar shigowa falon, yana ɓudewa ya ga tareeƙ da kaya riƙi-riƙi ahannunsa.
Kallonsa tareeƙ yayi yace "yallaɓai lafiya kuwa?
Ahankali Adeeb ya lumshe idanunsa kafin ya jinjinawa tareek din kai,alamu lafiya ba komai.

Shigowa tareeƙ yayi da kayan ya ajiye yana mai cewa"yallaɓai idan an duba sai afadamin abinda babu aciki." Nan ma dai kai kawai Adeeb ya daga sannan ya kalli kayan ,ledojine kusan guda goma manya-manya.
Kallon TareeÆ™ yayi na dan wani lokaci kafin yace "an shirya komai na zuwan gurin mai Abie"?
" Eh yallaɓai komai ya kammala ,lokaci kawai muke jira" cewar tareeƙ kenan cikin girmamawa .
Jinjina kai Adeeb yayi kafin yace " U can go"

"Ok yallabai"
TareeÆ™ ya faÉ—a yana mai barin falon .
Kayan da tareeƙ ya ajiye Adeeb yayi da kallo kafin ya ɗauki leda ɗaya yana ɗan leƙawa, idanunsa ne suka sauka kan inner wear masu bala'in kyau da tsada,da sauri ya rufe ledar yana ɗan kallon ƙofa, dan sosa kansa yayi kafin ya dauko bra guda ɗaya da hannunsa yana mai kallonta,shiru yayi yana tunanin lallai zatayiwa fattu daidai,dan ahalin yanzu yana kallon abubuwan ta daya taɓa gani a toilet,murmushin yay tare da dan sosa kansa kafin ya ɗauki ledojin duka ahannunsa yayi dakin fattun.

Yana tura ƙofar kuwa ya jiyo ƙinkishin kukanta,tana zaune a tsakiyar gadon ta haɗa kai da gwuiwa tana kuka.dan bata wani jima tana barcin ba ta farka kuma ita tsoro takeji taje ta taɓa kofar wannan hulwar ta kuma tsoratata.

Da sauri ya ƙarasa cikin dakin yana kallonta,tsayawa yayi akanta bayan ya ajiye ledojin dake hannunsa,sosai yake jin tausayin fattu cikin zuciyarsa,sam baya kyaunar ganinta cikin damuwa,yanzu zaiji zuciyarsa tayi masa zafi sosai.

"Hulwa " Adeeb ya furta cikin muryarsa mai sanyi da nutsuwa.
Da sauri fattu ta É—ago kanta ,sakamakon jin Muryar Adeeb da tayi,
Ai bata san lokacin data diro daga kan gadon nan ba ta wani ƙanƙame Adeeb da iya ƙarfinta tana kuka,
"Hammana dama nasan bazaka gudu ka barni ba, Hamma na shiga damuwa sosai lokacin danaga ka koma macijin nan,nayi tunanin guduwa zakayi ka barni Hammana dan Allah karka rabu dani"fattu ta faÉ—a cikin matsanancin kuka,wanda zamu iya cewa na farin cikine.

ahankali Adeeb ya lumshe idanunsa,tare da sakin ajiyar zuciya"har abada bazan taba rabuwa dake ba,ina tare dake komai rintsi komai wuya hulwatee" abinda Adeeb ya faÉ—a kenan , cikin zuciyarsa,amma azahiri kawai rungume fattu yayi shima ,yana mai shafa bayanta ahankali.
Kuka sosai fattu keyi tana kara rungume Adeeb,bazata iya faÉ—in irin farin cikin da take cikiba,
" Ya isa haka kukan " Adeeb ya faɗa yana mai ɗago kanta.komar da kan nata tayi tare da kara kwanciya akan faffaɗan ƙirjinsa.

Murmushi kawai Adeeb ya tsinci kansa dayi,yana mai shafa bayan fattu,sosai yake jin wani nishadi idan fattu ta ruƙunkume shi nan ,ji yake kamar su tabbata ahaka.
Bangaren Fattuna dai hakan ne ,ji tayi bata don rabuwa da jikin Adeeb ɗin,dan ba ƙaramin nutsuwa take samu akan wannan ƙirjin nashiba.
Kusan minti goma suna rungume da juna ,kafin Adeeb yayi karfin halin cire ta daga jikinsa yana mai cewa" waike bazai sakeni ba saikin karyani?kin fiye son jiki fa" ya faÉ—a yana É—an harararta .
Chapter 18 · 0% Book details