← Book details Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 27

Sashe 11

Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dawo da kallonsa yayi kan baffa wanda yake kallon duk abinda ke faruwa,zuciyarsa tana masa wani irin ƙuna da ciwo.
Saida ya ɗauki kusan minti biyar kafin yace "Abba nayi maka alƙawarin zan taimaka wajen neman asalin iyayen yarinyarka,zamuiyi amfani da wannan sarƙa in Sha Allah everything is gonna be ok"ya faɗa cikin muryar sa mai daɗin amo .

Hannunsa baffa ya kama cikin farin ciki yace "na gode Allah yayi maka albarka,ka kulamin da fattu karka bari ta cutu "

Jinjina kai yayi shima yana mai riƙe hannun baffan, akaro na farko ya ɗanyi murmushi.masha Allah masu karatu bakuga yadda yayi wani sihirtaccen kyau ba,Dan murmushin ba ƙaramin kyau ya ƙara masaba.

Kwanciya fattu tayi akan sallaya ta juya bayanta tana ta kuka da rawar zazzaɓi,shikenan yanzu haka zata bi wannan bawan Allah da batasan koshi waye ba,meyasa iyayenta suka yarda ita?me tayi musu haka da zafi?dama baffa ya fasa ƙidurinsa na cewar saitabi wannan bawan Allah mana.

Baffa ne ya miƙe tsaye da sauri tare da leƙawa ƙofar ɗakinsa, dan tabbas yaga gilmawar mutum,aikuwa yana leƙawa ya hango zanin gwogwgo hansai tana shigewa ɗakinta. Ya Salam kenan taji duk abinda suke tattaunawa ?lallai dole su bar gidan nan kafin gari ya gama wayewa.dan yanzu kam asuba ta kawo kai,

Da sauri ya koma É—akin yace "Adeeb akwai matsala,yanzu yanzu zaku tashi ku dau hanya,dan kuwa hansai taji duk abinda muke tattauna,kuma na tabbata ko bari bazata yi gari ya gama wayewaba zata je ta sanar da mai gari"

Baffa ya faÉ—a cikin tashin hankali da damuwa.

Shikuwa Adeeb ko ajikinsa ƙara gyara zama yayi ,dan bazai iya kwanciya anan gurin ba ,kafin ya kalli baffa ya ɗan taɓe baki yace "and so what idan ta faɗa masa"?
Ya faÉ—a cikin ko in kula.

"Bazaka gane zalumcin lamiɗo ba Adeeb zai iya sawa kashe fattu ,dan Allah ku tashi muje In fitar daku hanya ku tafi, ka taimaka min ka ceci rayuwar yata"baffa ya faɗa cikin kuka yana durƙusa akan gwuiwoyinsa.

Da sauri Adeeb ya tashi ya kama baffa ya miƙar dashi yace "is ok Abba zamu tafi yanzu.ya faɗa yana mai kamo hannun fattu ya miƙar da ita tsaye.

Ita kuwa fattu yadda yake jin zuciyarta bayani ace mai gari yasa a kasheta Bama,koba komai zata huta da ƙuncin zuciya da damuwa.tana mikewa tayi baya zata faɗi,dan gaba ɗaya ba ƙarfi ajikinta.da sauri Adeeb ya tallafi ga zuwa jikinsa,kallon fuskarta yayi wacce ta kumbura ,sai rufe idanu take tana buɗe wa,da gani tana shan jiki sosai.

"Muje bawan Allah ,fattu daure kinji"baffa ya faɗa cikin ruɗu ,ba abinda yake ɓukata irin yaga sun bar rugar nan.

Ganin fattu zata ɓata musu lokacine yasa Adeeb ya ɗagata sama tsak!kamar ƴar tsana ya saba akafaɗarsa yacewa baffa" muke Abba"

Wata leda Baffa ya dauko,tare da rigar nan ta fattu ya cusa ciki,sannan yayi waje suka rufa masa baya......

Masu karatu me zakuce game da rabuwar baffa da fattu?

Mrs babi ce💘💘
[7/17, 6:48 AM] +234 906 568 0805: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄

MACIJI NE🪱🪱🪱

Na mammy kabeer
(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book

Page 21/22

_______________Wata leda Baffa ya É—auko ,ledar da É—an nauyi ,alamun wani abune acikin ta .sannan ya É—auki wannan rigar ta fattu ya cusa acikin ledar,safin yayi waje ,Abeed ya rufa masa baya.

Ahankali baffa ke takawa Abeed na biye dashi,saɓe da fattu akafaɗarsa,wacce ke cikin matsanancin hali na zazzaɓi,da damuwa.

Tafiya suke cikin sauri bayan sun bar gidan ,cikin ikon Allah basu haÉ—u da kowa ba ,har sukayi nisa da garin sosai,saida baffa ya fitar dasu kan kwalta kafin ya tsaya .

Har zuwa wannan lokacin fattu na saɓe akan kafaɗar Abeed ,duk da irin uban nisan dake tsakanin rugar da kwalta.

Ahankali Abeed ya sauƙe fattu ya ɗan jingina ta da jikinsa,dan yaga bazata iya tsayuwa ba .

"Malam Abeed karɓi wannan wasu yan kudadene da nake tarawa saboda irin wannan ranar,nasan zasu toshe muku wata kafar,dan Allah ka riƙe min alƙawari, ka kulamin da fattuna,karka bari wani ko wata ya cutar da ita,sannan kayi iyakar ƙoƙarin ka wajen sadata da magaifanta.
Kaima zaka sami lada"baffa ya faÉ—a yana kallon bayansa ,hanyar da suka baro ,dan tsoro yake kar yaje ko anbiyosu,dan yasan zuwa yanzu labari ya isa kunnen lamiÉ—o,tunda gari yayi haske an kusan shiga sallah.

"In Sha Allahu Abba zan kula da amanar ka,na gode da taimakon da kukayimin, sannan zan dawo gareka very soon"Abeed ya faÉ—a cikin nutsuwarsa da rashin son magana,akwai abubuwan da yake son faÉ—a amma tsabar rashin son maganarsa bazai iya ba dan haka yayi shiru daga wannan maganar.

Hannun fattu baffa ya kama yariƙe gam-gam cikin nashi,kallon ta yayi yayinda itama take kallonsa cikin kuka wanda muryarta ko fita batayi sosai, shima baffa tuni zuciyarsa ta karaya ,sai hawaye sharrrr!!

"Allah ya shiga lamarin ki fattu, Allah ya karemin ke ka yasa damu da alkairi,ki kula da kanki,ki kama mutuncinsu.Allah yayi miki albarka"baffa ya faÉ—a cikin kuka sosai,abin tausayi.

"Baffa bana son tafiya ,dan Allah kace na zauna ,Ni nafison zama da kai akan iyayena ma asali,baffa karka tafi ka barni "Fattu ta faÉ—a cikin kuka harda shashsheka kamar zata shiÉ—e. Kafin baffa yayi magana saiga wata mota zata wuce ,da alama daga cikin Jos take .

Da sauri baffa yayi musu hannu alamun su tsaya.tambayarsu yayi ina suka nufa ,mai motar yace Kano.

Kallon Adeeb baffa yayi yace "duk da bansan inane Kanon ba amma Gara kubi wannan motar kafin tawagar mai gari su fito nemanku.

Kai kawai Abeed ya ɗada,tare da kamo hannun fattu suka nufi motar,hannunsa ɗaya riƙe da ledar da baffa ya basu.

Kuka fattu take harda ihu tana faÉ—in"wayyo baffana ,banason tafiya,dan Allah baffa kace na dawo wayyo baffa am wayyo Allah na ,wayyo rayuwata "
Baffa kam ko magana ya kasa tsabar kuka sai daga musu hannu kawai yake yana juya kai.
Abeed ne ya sanyata cikin motar tare da riƙe ta ,ɗan sai ƙoƙarin fitowa take ,haka mai motar nan yaja motarsa yayi gaba,dan kaya zaije ɗaukowa.

Baffa yana tsaye har saida yaga ɓacewar motar ,sannan ya sauke wani kwauron numfashi yana mai share hawayen idanunsa,"Allah ga amanar ƴata nan na miƙa lamarin ta ahannunka ,ya ubangiji kazama majiɓancin al'amarinta "baffa ya faɗa yana mai juya dan koma gida ayi wacce za'ayi.

Aikuwa tun kafin ya ƙarasa cikin garin ,ya hango cincirindon mutane aƙofar gidansa,jinjina kai yayi,dan dama yayi tsammanin hakan .
Suna hangoshi sukayo kan suna wllh koya fito da Æ´ar Shegiyar daya É—auka matsayin Æ´arsa ,da kwarton ta da suka ajiye agida,ko kuma su kashe shi yanzun nan.

Kallonsu yayi cikin kamala da dattako yace "ikon Allah me kuma mukayi dazaku kashemu?wace yarinyar kuke nema?bayan wacce mai gari ya riƙe agurinsa?baffa ya faɗa kai tsaye ba nuna alamun tsoro.
Nan wani lawwali yace masa"ai jiya yarinyar nan saida ta bari dare ya raba sannan ta sami lamiɗo tayi masa jina jina,gaba ɗaya ƙafafunsa sun ƙarye,ga hannun damanshi ma ya ɓalle baral, sannan ta gudu,kuma munsan tabbas tana gidan nan,dan kuwa hansai ta kai labari,
Kuma ta fayyace mana komai game da yarinyar ,ashe Shegiya ce ka tsinto ka kawo gidanka,sannan ka ajiye mata wani gardin suke lalata dashi,dan haka gaba ɗayanku yau sai hukunci ya hau kanku,dan lamiɗo yana nan banda ihu ba abinda yake yana kiran maciji zai kashe shi,fattu ce tayi masa ture.sannan arɗo ma yana can hannunsa guda ya shanye ya zama kamar sillan kara ,kuma duk aikin fattu ne ,dan haka yau wllh saimun kashe fattu"lawwali ya ƙare zancensa yana mai ɗaga sandarsa sama.

"Toh me yasa baku shiga kun duba fattun ba ?idan nan ta dawo,ita wacce ta kai muku rahoton saita faɗa muku inda fattun take"baffa ya faɗa yana ƙoƙarin shigewa gida.

"Ƙarya yake wllh, saidai in ya boyesu ,ko kuma sun gudu ,dama naji yana cewa su gudu dan haka karku taga masa " na tsinkayo muryar gwogwgo hansai na faɗin haka ,dan taji mugun haushi da ba'a sami su fattu cikin gidan ba.
Aikuwa baffa yana tsaye
Ba zato ba tsammani yaji sun rufeshi da duka ta ko ina.
Har saida suka kaishi ƙasa.sannan suka taitayeshi sai gurin. Mai gari.suna zuwa suka tarar ana yiwa mai gari ɗori sai ihu yake yana kuka.dan haka can ɗakin hukunci suka jefa baffa,wanda yayi kaishi sosai dan ya daku.
Allah Sarki baffa ,Allah ya saka maka.

Fattu kuwa tsabar kuka har muryarta ta dashe,can jikin ƙarshen motar ta koma tare da haɗe kai da gwuiwa tana kuka marar sauti ,jikinta sai rawa yake ,fuska ta kumbura suntum tayi jajur ,abinka da farar fata.

Abeed yana daga gefe yana kallonta ,sosai yake jin kukanta har cikin ransa,haƙiƙa yarinyar tana fuskantar ƙalubalen rayuwa and she's to Young to handle the situation.amma ya zatayi?dole ta ɗauki ƙaddara yadda yazo mata.

Kallonta yayi yadda jikinta ke ta rawa tana shashsheƙar kuka,yaso ace ya iya rarrashi, daya rarrasheta ,koba komai itaɗin yanzu amanarsace,amma Gara tayi kuka ,koba komai zata rage jin raɗaɗin da taleji cikin zuciyarta.

Tafiya suke sosai ,Dan drivern gudu yake tsulawa,kasancewar safiya ce hanyar ba motoci sosai,sai jifa-jifa suke cin karo da motocin.

Abeed yayi shiru ,tare da jingina kansa jikin kujerar da yake zaune,ba abinda ke yawo cikin zuciyarsa,sai labarin da baffa ya bashi na cewar wai shiɗin amaciji suka ganshi,to ta yaya?yaushe hakan ta faru,me yasameshi? Tabbas idan har abinda baffa ya faɗa gaskiya ne baya raba ɗayan biyu cewar sharrin Amma ne wannan ,dan ita kaɗai yake tunanin zata iya cutar dashi ,tunda afili take nuna masa ƙiyayya, amma zaibi abin ahankali harya gano mugun ƙullinta akansa kafin ya ɗauki mataki.

Ya rasa me ya tsareta Amma arayuwa sam bata ƙaunarsa ,kullum burinta ta cutar dashi,tun yana ƙarami yake fuskantar tsangwamarta,har kawo yanzu bata fasa ba ,amma akwai lokacin da ko ance tayi masa wani abun bazata iyaba.
Chapter 11 · 0% Book details