← Book details Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 27

Sashe 3

Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wayyo Allah na gwogwgo kiyi haƙuri wllh bazan ƙara ba, tsautsayine yasa na fashe miki bokati, dan Allah kiyi haƙuri gwogwgo" abinda fattu ke daɗi kenan cikin azaba dan ko ina na jikinta ciwo yake mata barin ma hannunta daya kumbura sosai, alamun tayi targaɗe a hannun kenan.
"Wllh yau saina kasheni Shegiyar yarinya muguwa kafin baƙin cikinki ya kasheni, na Tsaneki fattu bana ƙaunar ganinki arayuwata, kinsan nawa nasai bokatin nawa? kika je kika fashemin shi? Murtala huɗu da naira goma fa na siya, wllh saina dakeki, kuma ki sani duk inda zaki je ki samo min kuɗin bokatina sai dai kije dan bazan ɗauki asarar ba" gwogwgo ta faɗa tana haki, kuma bata daina jibgar fattu ba, kamar ta sami jaka.
"Wayyo gwogwgo dan Allah kimin rai hannuna zai karye, wllh bada gangan na fashe miki bokati ba, macizaine suka biyo ni zasu cinyeni shine na gudu amma bada gangan nayi ba wllh" ta faɗa cikin azaba dan tuni ƙarfinta ya kare ko iya ɗaga hannunta bata yi.

"Allah ya tsine muku keda mashizan shegen yaro karuwa, ina ruwana da macizai? dama sun cinyeki kowa ya huta mai baƙin hali marar farin jinin da kika kasa auruwa, dama shegun macizan sun.......kasa ƙarasa magannarta tayi sakamakon wani ƙaton abu dataji ya faɗo kanta jifff !!! kamar buhun hatsi.

"Wayyo ni Hansai menene wannan ɗin yake zagayemin jiki? ta faɗa cikin firgici da tashin hankali tana mai jefar da iccen hannunta. Aikuwa carab idanunta suka sauka akan wani ƙaton macijin daya nannaɗeta ko motsi bata iya yi, kuma ya fasa kai a saitin fuskarta sai huci yake yana fito da harshe.

"Wayyo Allah na ni hansai yau me zan gani ? na shiga ukuna malam kazo fattu ta min ture maciji zai kasheni ka taimakeni, handi ɗin bonu lalashewa ni yar nan wayyo malam" ta faɗa cike da tsananin tsoro gami da razani da ƙyar take magana dan ba ƙaramin shaƙar mata jiki macijin yayi ba har wuyanta.

Tsoro, fargaba da tashin hankali sune suka daɗa kashewa Fattu jiki, dan faɗuwa tayi ƙasa warwas ko motsin kirki bata iya yi, shikenan Tata ta ƙare yana gamawa da gwogwgo tasan kanta zaiyo, Allah Sarki innarta, yanzu shikenan haka zata mutu bataga innarta ba, batasan ya fuskarta take ba? bare tasan dangin innarta? Amman Gara ta mutumma ta huta da wannan baƙar azabar da take sha agurin gwogwgo.

Shikuwa macijin nan ƙara matse gwogwgo yake sosai, gaba ɗaya ta fice daga hayyacinta, dan ko magana ma ta kasa, sai idanunta da suka kada suka yi jajur da su, sai faman nishi take numfashinta na ƙoƙarin ɗauke wa.
Saida macijin nan yaga gwogwgo bata motsi alamun ta suma, sannan ya sake ta ta hanyar janye jikinsa daga gareta.

Da gudu kuma yayi kan fattu wacce ke kwance cikin tashin hankali ganin yadda macijin nan ya kashe gwogwgo. Runtse ido tayi da mugun ƙarfi tana salati da sallama da duniya, ko motsin kirki batayi, dan da kyar take iya jan numfashi ma.

...Shikuwa macijin nan ganin bata ko motsine yasa ya sauƙo daga ruwan cikinta ya tsaya saitin fuskar ta tare da fasa kansa yana huci, matsowa yayi sosai jikin fuskar tata yana hura mata iska daga bakinsa, sannan ya ɗan ja da baya ya tsaya yana kallon ta.

Ahankali fattu ta ɗan buɗe idanunta dan ganin shin me kuma macijin nan ke shiryawa? Ta yaya yake tsara kasheta itama, saidai tana buɗe idanta suka sauka akan na macijin nan ya ƙura mata idanunsa.

Cike da tsoro da fargaba fattu ta kafe shi da nata idanun, sai kawai ta ji ta tsinci kanta da kasa daina kallonsa, abubuwan mamaki take gani tare da macijin, sam kwayar idanunsa ba irin ta macizai bace, shi wannan sak! irin ta mutane ce saidai gurin farin yayi wani irin kala kala, blue yellow pink, Amma asalin kwayar baƙiƙirin take.
Sai kuma taga hawaye na zubowa daga idanun macijin kamar mutum yana kuka.

"Innalillahi wa'inna ilahirin raji'un, Allahumma ajirni fi musibati waaklifni kairan minha, la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" Shine abinda fattu ta fara karantawa cikin zuciyarta jikinta na wani irin tsuma da karkarwa, tunda take bata taɓa ganin irin wannan macijin ba sai yau, ya maciji zai kasance da idanun mutane? sannan kuma jikinsa akwai banbanci sosai dana macizai, dan shi yana da wani irin jiki mai ban mamaki yadda kalar idanunsa ta kasance haka shima jikinsa yake, sannan kuma bai kai girma irin na macijin jiyan nan ba amma yana da girma shima sosai, kuma dogone na gaske.

Kallon kallo kawai ake tsakanin fattu da macijin nan, inda ahankali ya fara hucewa daga kumbura da fasa kan da yayi, Fattu na kallonsa harya koma normal jikinsa ya daidaita, sannan ya fara ƙoƙarin barin ɗakin ta wata yar hanya dake jikin katangar karan, wacce ita fattu sam bama tasan da ita ba sai yau, da alama dai shi yayiwa kansa hanyar.
Saida yaje gab da hanyar tasa sai kuma ya juyo da kansa yana kallon fattun, shi bai tafiya ba kuma bai dawo ciki ba.

Sosai jikin fattu ke rawa tana zubda hawaye, dan yau kam lamarin ya kulle mata kai, wai wannan wane irin MACIJINE? shin macijin ne ma kokuma wata halittar? sannan maiyasa yaƙi yi mata komai, sai dai ƙoƙarin ceto ta da yake atsammaninsa na ko bata numfashi? haƙiƙa akwai abin dubawa dan gane da wannan macijin.

"Fattu ! fattu!! ki tashi ki yi salla lokaci yana ja fa" ta tsinkayo Muryar baffa daga wajen É—akin yana mata magana .
Jin muryar baffa da fattu tayi sai hankalinta ya É—an kwanta cikin É—aga murya tace "baffa kazo ka taimaka min gwogwgo bata motsi" ta faÉ—a cikin Muryar kuka tana kallon macijin.

Cikin sauri da azama baffa ya shigo É—akin yana faÉ—in "Subhanallah me kuma ya sami Hansai din?
Cikin kuka fattu ta kalli baffa sannan ta kalli inda macijin nan yake har lokacin yana tsaye yana kallon ta,
"Baffa bansani ba kawai ta shigo tana dukana sainaga ta faɗi ƙasa" abinda fattu ta tsinci kanta kenan da faɗa murya na rawa.

Ahankali macijin nan ya juyar da kansa ya bi ta yar ƙofar nan ya fice.
Sai lokacin hankali fattu da nutsuwarta suka dawo jikinta, cikin ƙarfin hali ta yunƙura ta tashi zaune, har lokacin akwai alamun tsoro da firgici akan fuskarta, dan jikinta sai rawa yake.
"Washhhh hannuna" ta faÉ—a ahankali tana mai runtse ido, dan sosai hannun ke mata mugun ciwo.

Ruwa baffa ya É—ebo mai sanyi wanda ya tara na sama, yana zuwa ya kwarara wa gwogwgo ruwan a jikinta, aikuwa azabure ta tashi zaune tana ihu "wayyo Allah na maciji zai kasheni malam kawo É—auki, fattu tayimin turen maciji, wayyo wuyana, wayyo hannuna na shiga uku na lalace" abinda gwogwgo hansai ta farka dashi kenan, maimakon ambaton sunan Allah .

"Kinga hansai ki nutsu ba wani maciji anan nine bukar wannan kuma fattu ce ɗiyarki" cewar baffa kenan a ƙoƙarin sa na kwantar mata da hankali. Buɗe ido gwogwgo tayi sosai ta kallesu kafin tace "kuturin bala'i Allah ya kiyaye wannan sheɗaniyar ta zama ƴata mayyace fa, wllh ture tayimin yanzun na wani maciji ya kusan hallakani, ai komai zai faru sai dai ya faru amman sainaga bayan yarinyar nan Shegiya may.......wayyo Allah na ya dawo ya dawo Malam" gwogwgo hansai ta faɗa sakamakon hango kan macijin nan da tayi, ai da gudun gaske ta fice daga ɗakin tana ihu .

Girgiza kai baffa yayi yana mai Allah wadai da halin matar tasa, shikam yasan sam baiyi dacen mata ba. Kallon Fattu yayi wacce take riƙe da hannunta mai ciwon, hawaye a zaba na zuba a idanunta.

"Ashsha ashsha fattu kiyi haƙuri kinji, komai yayi farko zaiyo ƙarshe, Allah yana sane da halin da kike ciki in sha Allahu zakiyi dariya anan gaba" Baffa ya faɗa cikin sanyin murya da ƙoƙarin kwantar mata da hankali.

Ahankali ta sanya hannu ta share hawaye idanunta, kafin tace "Baffa hannu na ciwo yake min" ta faÉ—a tana nuna masa hannun dayake mata ciwon.

Kallon hannun yayi yanda ya kumbura yayi suntum dashi, cikin tausaya wa yace "Ayya faɗimatu sannu. Kinji maza daure kiyi sallah saina duba miki hannu kiyi haƙuri, Allah yayi miji albarka" ya faɗa yana mai taimaka mata ta mike tsaye.

"Ameen baffa "Ta faɗa tana ficewa daga ɗakin. Bayi ta shiga ta kama ruwa sannan tayi alwala cikin dabara kafin ta fito ta koma ɗakin, Sallah tayi tare da karatun alƙur'ani mai girma, da ka take karatun dan da ahaka aka koya mata, bayan ta idar ne baffa ya shigo ɗakin ɗauke da kwarya ahannunsa.

"Sannu Fattu karɓi wannan madarar Kisha kinji, saina duba miki hannun" Baffa ya faɗa yana miƙa mata kwaryar. Bata da zaɓi dan haka ta katɓi kwaryar tare da yin Bismillah ta kafa kanta, saida ta shanye kafin ta ajiye kwaryar .

Allah Sarki Fattu tasha wahala sosai lokacin da baffa ke gyara mata hannun, kasancewar yayi tsami sosai, kuka take harda su majina, haka baffa ya gyara mata yana mata sannu. Bayan ya gama gyara mata ne yace ta kwanta ta huta kafin garin ya gama wayewa. Ahaka ta kwanta tana ajiyar zuciya, inda bata jima ba barci yayi awon gaba da ita, abinka da wanda bai sami barci ba dama.
Ficewa baffa yayi daga ɗakin ya nufi nashi cike da tausayin ƴar tashi dayake matuƙar ƙauna.

Ko minti talatin batayi da fara baccin nan ba ta tsinkayo muryar gwogwgo tana kiranta "Ke gantalalliya mayya fito dan ubanki ,ko uwarki ce zata miki aikin?Shegiyar yarinya aljana wllh bakici bulusba yadda kika sa macijin nan ya lagartamin jiki to wllh saina rama ,fito ki É—ebomin ruwa yanzun nan .

Afirgice fattu ta tashi daga barcin ta fito da gudu tazo tana rawar jiki ,Dan bala'in tsoron gwogwgo take kamar ranta."gwogwgo dame zan É—ebo ruwan "ta faÉ—a kanta asunkuye.

Da ubanki zaki ɗebo ruwan kinji ?kije ki nemomin kuɗin da zaki biyani bokatina inyaso ki ɗebomin ruwan aciki"gwogwgo ta faɗa tana daga ɗaki,dan taƙi fitowa waje kartaje macijin nan ko ajikin fattun yake.
Chapter 3 · 0% Book details