← Book details Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 27

Sashe 24

Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Hamma zanyi fitsari" fattu ta faÉ—a ahankali.
Dan kallonta yayi kafin yace " zaki iya zuwa toilet É—in?"
Kai ta daga masa tana mai yunkurawa ,tashi tayi tsaye tana ɗan yamutse fuska. Sai taji kamar lema ajikinta,juyawa tayi tare da kallon inda ta tashi,zato idanu tayi lokacin data jini agurin,da sauri ta kai hannunta ta shafo bayanta ,tana mai kallon hannun,aikuwa jini ne kuma daga jikinta ya fito,ƙara zato idanu tayi cikin tsoro tana mai faɗin" na shiga ukuna Hamma jini ,jine yana zuba ajikina,wayyo Allah Hamma jini"fattu ta faɗa tana mai nuna masa hannunta ,jikinta na rawa sosai kamar ana kada mata gangi,
Kallonta Adeeb yayi da sauri ,yana mai kallon hannun nata ,lumshe idanu tayi yana mai jin wani iri ajikinsa,tausayi fattu ke bashi,ita bata san komai ba ,yanzu meye abin damuwa akan wannan ga yadda jikinta ke rawa kamar ana yankata.?
Ahankali ya mike tsaye tare da dafa kafadun fattun yace " ki nutsu mana ,wannan ba wani abun damuwa bane kinji dama hakan na faruwa ga ko wace mace data kai shekaru irin naki" yayi shiru yana É—an sauke nunfashi ahankali.

Fattu kuwa kuka take tana cikin tashin hankali,sam Bama tajin me Adeeb ke faÉ—i,sai cewa take " Hamma jini ajikina, dan Allah kace ya daina zuba ,na shiga uku jinina zai kare wayyo baffana" abinda take fadi kenan jikinta na rawa .

Gaba daya Adeeb yana rasa me zaicewa fattu,dan haka kallonta kawai yake cikin damuwa,suna cikin haka saiga nanny ta shigo, ajiyar zuciya Adeeb yayi tare da kallon nanny amarairaice.

" Aa meke faruwa ne haka magajin faÉ—a?(da yake haka take kiransa) taci gaba ,naga fateema na kuka ,kaikuma ka tasata gaba da kallo kaima kamar salati kukan?nanny ta fada tana mai karasowa cikin dakin.

Ahankali Adeeb yace "nanny kiyi mata bayani kuka take, wai bata so" ya faÉ—a kamar zaiyi kuka.
"Yau naga ikon Allah fateema meye baki so?ko maganin ne baki don sha?kiyi haƙuri ai lafiya ake nema miki kinji ?kuma da kinsha jinin zai....sai kuma tayi shiru tare da bin gadon da fattu ta tashi da kallo,to kace jinin ne yazo ,wato shi tagani take cewa bata so,Allah Sarki ai zaki saba dayake wannan ɗin na farko ne ,zo muje In gyara miki jiki yi shiru" nanny ta faɗa tana mai kamo hannun fattun suka nufi toilet.

Kallonsu Adeeb yayi tare da sauke ajiyar zuciya ,sannan ya fice daga É—akin,bayan ya janye zanin gadon daga kan gadon,ya ajiye gefe guda,tare da shimfida wani.

Kai tsaye gurin mai martaba ya nufa,yana shiga ya tadda mai martaba tare da amma, zama yayi kusa da mahaifin nashi,bayan ya jefa wa amma wani kallon na tsana .
Kawar da kai amma tayi tare da sakin murmushin gefen baki tace yaro yarone ,cikin zuciyarta.

" Habeebee Barka da dawo ,yanzu nake ƙoƙarin sake kiranka,ai najika shiru,kasan yanzu bana son koda da minti ɗaya ka ƙara nisa dani"abie ya faɗa yana mai shafa kan Adeeb.

Murmushi Adeeb yayi tare da sumbatar hannun mahaifinsa kafin yace " abie wancan karon ma ,kaddarace ta sameni,har Allah ya ba maƙiya nasara akaina,saidai ahalin yanzu kar nake kallon,kowa sannan ba abinda mutum ya isa yayimin na cutarwa in Sha Allah" Adeeb ya faɗa yana mai kallon ammi cike da tsana .

Itama ammi kallon Adeeb take ,tana mai suna maganganunsa ,kafin ta sauke ajiyar zuciya tayi sallama da mai martaba tare da ficewa daga É—akin.

Waya ta dauko tana mai kiran wata number tace " mu hadu yanzu-yanzun nan" sannan ta kashe wayar.

Adeeb yana fitowa daga É—akin abie ya nufi bangaren da amminsa ke hutawa,
Wayace akunnenta kuma da alama wayar da take mai muhimmanci ce ,saidai tana hango Adeeb ya tunkarota tayi saurin katse wayar tana mai cewa " zan kira -zan kira" bata jira amsar dayan vangaren ba ta kashe wayar.

Zama yayi kusa da ita tare da kamo hannunta ya sumbata, kanshi ta shafa taba faÉ—in Allah yayi maka albarka.
Ya jima suna dan hira ,kuma duk akan kunyar fattun ne ,kafin ya mike yace zaije ya huta.

Ƙura mata ido naga ammi tayi ta baya ,kuma fuskarta amugun hade ,kafin kuma tayi wani murmushi tana mai jinjina kanta....

Masu karatu manage ,
Yau naje gidan suna ne.

Saida na dawo nayi wanna typing É—in.

Much luv.

Mrs babi ce💘💘

Share and comment fisabilillah.
[7/27, 8:20 PM] +234 810 779 7743: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄

MACIJI NE🪱🪱🪱

Na mammy kabeer
(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚
https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din👆🏽

Free book

Page 41/42

_______________Adeeb yana barin gurin saiga rashy ya ƙaraso,zama yayi kusa da mahaifiyar tasa tare da sumbatar hannunta,

Kansa ta shafa tana faÉ—in ",magajin faÉ—a prince Rashad Muhammad ashraf"ta faÉ—a cike da jin dadin sunan.

Turo baki Rashad yayi tare da kallon ammi yace " ammi ta yaya zan zamo magajin fadar?bayan kinƙi yin wani abu akan wannan al'amari,ki dubafa,Adeeb ya dawo gida,kuma cikin ƙoshin lafiya yake,kina tunanin abie zai bar Adeeb ne,sannan Ni ya ɗorani akan karagar?

Shiru ammi tayi tana kallon Rashad har ya kai ƙarshe azancensa,kafin tayi wani murmushi kana tace " Rashad kenan,kasan dai Adeeb yana jin maganata,sannan baya tsallake umarnina, yanzu akwai Abinda nake tunani akan yarinyar can ,daya zo da ita. Ina son tabbatar da wani abu ne game yarinyar ,wannan sarƙa ta wuyanta tabbas nasan iyalan dake da irin sarƙa,kuma sun rasa yarinyar su tsawon shekaru,
Amma idan har na tabbatar da zargina akanta,to zanyi iyakar ƙoƙarina na ganin bata haɗu da ahalin nata ba,dan haduwarsu da ahalin babban koma bayane agareni. Masanin ido kawai ,zakaga abinda zanyi akan wannan al'amarin.
Murmushi Rashad yayi tare da jin wani sanyi cikin ransa,dan yasan tabbas mahaifiyar tasu zatayi ƙoƙarin akan wannan al'amarin.

"Amma ammi Zulaihat fa?kinsan yadda take ƙaunar Adeeb ,kada ta bamu matsala"cewar Rashad kenan yana gutsirar dabino .

"Barni da zulaihat,bana jinta ko kaÉ—an ,yarinyar da ba wani hankali ta cika ba,itama bazan bari ta auri Adeeb É—in ba ,lokaci kawai nake jira in maidata can gida"ammi ta faÉ—a cike da murmushi akan fuskarta.
Sun jima suna tattauna ita da Rashad agurin ,kafin suka koma cikin gida.

Fattu kuwa suna shiga toilet nanny ta hada mata ruwan wanka mai zafi,tace tayi wanka maza.
Bayan tayi wankan ne ,nanny ta bata wannan pant din tasa ajikinta ,sannan suka fito,har zuwa lokacin kuka fattu keyi,har yanzu jinin bai daina zubowa ba,yanzu idan jinta ya kare ya zatayi?mutuwa fa zatayi kenan.

Nanny sai rarrashinta take akan taci farfesun nan tasaha magani amma taki,kuma har lokacin marar ta ciwo take mata.

Suna cikin haka saiga Adeeb ya shigo ɗakin,tana ganinsa jikinta ya ƙaru.tun kafin ya zauna ta fara magana.
" Hamma na shiga uku har yanzu jini na zuba yake ,tsoro nake karya kare In mutu,dan Allah Hamma ka taimaka min" fattu ta faɗa tana mai miƙa masa hannu cikin kuka sosai.

Da ɗan sauri Adeeb ya ƙaraso kusa da ita ya zauna,kallonta yake cike da tausayi,kafin ya riƙe hannunta wanda take miƙa masa yana ɗan murzawa kana yace" kina so ya daina zubowa " ya faɗa cikin sanyin muryarsa.
Da sauri fattu ta jinjina kai tana hawaye.
" To kiyi shiru,ki daina kuka, sannan ki nutsu kici abinci Kisha magani,zakiga ya daina zubowa" Adeeb ya faÉ—a yana mai share mata hawaye wasu na zubowa.

"Hamma da gaske idan na daina kukan zai daina zubowa Ni tsoro nakeji kar jinina ya ƙare" ta faɗa cikin muryar kuka tana mai shagwabe fuska.
Jinjina mata kai yayi yace " sosai ma kuwa,kuma jininki bazai ƙare a idan kika daina kuka"
Ahankali fattu ta sanya bayan hannunta ta share hawayen,tana mai kallon Hammana nata.
Farfesun ya karba ahannun nanny ya fara É—iba da cokali yana bata abakin,haka take cin farfesun kamar magani,kusan lokaci shida tayi tace ta koshi.
Bai takura mata ba,ya ajiye flate ɗin ,magungunan ya bare tare da miƙa mata.yamutse fuska tayi tana mai turo baki,alamun bata so.
Kallonta Adeeb yayi kafin yace " ok baki son abun ya tsaya kenan?"

" Ina so Hamma amma Ni bana son wannan abun aradu" ta fada cike da shagwaba, kafeta yayi da idanunsa masu matuƙar haske da ɗaukar hankali,wani irin yakeji idan tana masa shagwabar nan,nan take zaiji jikinsa yayi week, kasala ta lullubeshi ,gara yayi ya bata maganin nan kar ayi abin kunya gaban nanny.
Hannunsa yaji fattu ta kama cikin nata tattausan hannu ,wani yuummmmm!! Yaji gaba É—aya jikinsa ya É—auka ,ahankali ya lumshe idanunsa yana mai sauke ajiyar zuciya.
" Hamma zansha to kabani"fattu ta faɗa tana mai ƙara damke hannun Adeeb cikin nata.
Ƙara damke idanunsa yayi tamau yana mai fidda wani sauti da ɗan sauri,kusan minti biyu idanunsa na runtse ,kafin ya budesu,har sun sauya kala daga fari tas zuwa ɗan jaa kadan.

Ahankali ya zare hannunsa daga cikin nata,jikinsa sam ba kwari,maganin ya mika mata ,buɗe baki tayi ya saka mata maganin sannan ya bata ruwa.da gyar ta hadiye maganin tana ƙoƙarin yin amai.

Janyota yayi zuwa jikinsa ya rungume ta tsam-tsam ,yana É—an shafa bayanta slowly.
Lumshe idanu fattu tayi tana mai shaƙar daddaɗan kamshi jikin Adeeb,lokaci guda kuma taji ciwon marar ta na raguwa sosai.
Shima Adeeb idanu arufe yake shafa bayan fattu,yana mai jin wani yanayi atattare dashi ,dadinsa ma nanny ta bar ɗakin tuni.dan haka gyara zama yayi ,tare da jingina bayansa jikin gado.sosai yake jin dadin yanayin da suke ciki ahalin yanzu,gaba daya yanayinsa ya sauya.sosai yake jin kansa cikin hali na buƙatuwa,wanda har wani hucin iska yake fesarwa daga bakinsa.

Ahankali ya dago kan fattu tare da ƙura mata idanu,itama kallonsa take ,dan wani iri takeji ajikinta,bata san me takeji ba,amma kawai tana so hammanta yayi ta shafa mata bayanta.

Ahankali Adeeb ya kira sunanta" Hulwa"can cikin makoshinsa,kallonsa take jin ya kira sunan Hulwa kuma yana kallonta.
Bai damu da kallon da take masa ba yaci gaba da magana " me kike buƙata yanzu?ina ne yake miki ciwo" ya faɗa kamar mai yi mata rada asaitin kunnen ta.

Da sauri ta ƙanƙame dantsen hannusa tana mai lumshe idanunta,dan wani irin abu dataji yana mata yawo cikin jikinta,lokacin da sautin muryarsa tare da iskar bakinsa suka doki kunne ta.

"Hammmma" ta furta ahankali cikin jan sunan.
Chapter 24 · 0% Book details