← Book details Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 27

Sashe 13

Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Runtse idanun Adeeb. Yayi da mugun ƙarfi yana ambaton sunan Allah ,ya ɗauki kusan minti biyu cikin halin ruɗewa da rawar jiki.gaba ɗaya jikinsa yayi wani iri,kafin yayi ƙarfin halin sanya hannunsa dake rawa ya fizgota daga bayansa tare da tureta can gefe guda,yana mai sauƙe numfashi cikin sauri ,kawar da kansa yayi daga gareta yana mai cewa"kisa zani ki rufe jikinki Please.
Fattu kuwa cikin rawar jiki ta ƙara matsowa gareshi sam tama manta da batun wasu kaya,"dan Allah ka fitar dani daga ,Ni gurin baffana zani "ta faɗa cikin kuka.

"Kisa zani nace miki"ya daka mata tsawar data ƙara hargitsata.tsugunnawa tayi tare da ƙanƙame jikinta tana kuka.
"Ni ka kaink gurin baffana dan Allah ka maidani gurin baffa "abinda take daÉ—i kenan cikin kuka da rawar jiki ,gaba É—aya ta gama tsorata .

Zanin nata Adeeb yaje ya yayumo cikin lalube,dan ko gani batayi sosai .yana zuwa ya lulluɓa mata sannan,ya fice daga bayin, da gyar ya iya ƙarasawa kan gadon yana zuwa ya faɗa kan gadon tare da duƙunƙune jikinsa yana rawar sanyi ......

Masu karatu mutara next oage.

Ina ganin comments ɗinku masoya ta ko ina ,ina matukar jin daɗi da ƙaunarku ga wannan novel ɗin .

Na gode sosai Allah ya bar ƙauna ,

And I love you guys where ever you are🥰🥰🥰🥰

Anty mammy ce

Mrs babi💘💘
[7/17, 7:11 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄

MACIJI NE 🪱🪱🪱

Na mammy kabeer
(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book

Page 23/24

_________________Kwanci Adeeb yayi akan gadon ,tare da duƙunƙunewa guri ɗaya ,jikinsa kuwa banda rawa ba abinda yake ,idanunsa arufe ruf!
Ba abinda yake gani cikin idanunsa face hoton surar fattu.
"Ya Salam ! Ya Allah save"Adeeb ya faɗa ahankali yana mai riƙe matarsa data ke masa wani ciwo na lokaci guda.

Fattu kuwa tana jin fitarsa da sauri itama ta fito tana kuka.jikin madubi taje ta tsaya tana kallon yadda ya faɗa kan gadon tare da dunƙulewa yana rawar sanyi,cikin ranta take rayawa kodai baida lafiya ne ?ko shima zazzaɓin yake ?
Ganin idan ta tsaya zancen zuci saita shekarar agurin,gashi batayi sallaba.
Dan haka cikin tsoro da fargaba ta fara takawa zuwa jikin gadon ,tana zuwa taka ta tsaya ,tare da sanya bayan hannunta ta share hawayen daya silalo daga cikin idanunta.

Cikin sanyin murya tace "hamma zanyi sallah" ta faɗa kanta a ƙasa.
Yana jinta yayi shiru abinsa, yana ci gaba da jin yadda matarsa ke masa ciwo tana ƙullewa,ahankali yake karanta addu'oi cikin ransa ,fatansa kawai ya daina jin wannan azabar da kuma yanayin dake bibiyar ilahirin jikinsa.

Kusan minti biyar fattu na tsaye kanta aƙasa ,jifa jifa tana share hawayen dake zubowa daga idanunta.aranta kuwa cewa take "wannan hamma wllh baida kirki ,san ba bakinsu ɗaya da macijina ba,dubi yadda nayi masa magana ya wani shareni.

Shikuwa Adeeb yana kwancene yana ci gaba da ambaton sunan Allah,harya samu marar ta kafa masa ,sai wani uban gini dake karo masa agishinsa ,duk da sanyin a.c dake É—akin hotel É—in.
Ahankali yake sauƙe ajiyar zuciya yana ɗan kumshe idanunsa.kafin ya tashi zaune yana mai dafe da kansa.

Ganin ya tashi zaune yasa Fattu É—an ja da baya,dan ita tsoronsa ma takeji yanzu ,dan wllh da gani masifaffene.

Kallon gefen ta yayi ba tare da ya lalle ta kai tsaye ba,sannan ya ɗan ja tsaki yana mai yamutsa fuska da turo baki,kamar wani mace ,sannan ya miƙe ya shiga bayin ,ruwan wanka ya haɗa mata cikin boket dan yasan ba iya shiga kwamin wannan zata yi ba, sannan ya ɗauki sisi da sabulu ta ajiye mata .ya ratsa makilin acikin sabon burush sannan ya ɗan leƙa cikin ɗakin .tana tsaye kamar gunki ,har lokacin share hawaye take ,kumshe ido yayi yana mai cewa, wannan ta cika kuka ,cikin ransa.

Kafin ya buÉ—e baki ahankali yace "zo" ya faÉ—a kamar baya so.badan Allah yasa Fattu mai saurin ji bace da bazata ji me yace ba.
Ahankali take takowa cikin yanayi na tsoro,dan dai tana tsoron masifarsa ne da ba abinda zai sa ta koma wannan É—akin da ake ruwan jini.

Shiga tayi tare da tsayawa tana kallonsa.jikin sink ya matsa tare da miƙa mata burush ɗin yana mai cewa "oya wash your mouth"
Shiru fattu tayi tana kallonsa tare da kallon burush ɗin data karɓa daga hannunsa.

Kallon ta yayi shima fuska aɗaure yace "wanke baki" ya faɗa cikin ƙosawa ,yana jinjina ƙauyanci irin na fattu wai ko burush bata sani ba.

Ita kuwa fattu kallonsa tayi tare da kallon burush ɗin ,cikin ranta tace ikon Allah ,su nan da wannan abun suke wanke baki,mutuwa saidai hawaye da gishiri.ƙara kallonsa tayi suka haɗa ido,da sauri kowa ya kawar da kansa ,cikin shagwabar da fattu batasan tana da ita ba tace "hamma Ni ban iya wanke baki da wannan ba"ta faɗa tana miƙa masa burush ɗin.

Wani yarrrrr yaji ajikinsa, saboda salon yadda tayi maganar ,saiyaga kamar da gangan take wani abun.harara ya salla mata kafin ya karɓi burush ɗin yace "open your mouth"
Gurun fattu tayi tana kallonsa ba tare da ta buÉ—e bakin ba.
Runtse ido yayi cikin ciwon rai yace da ɗan ƙarfi"haaaaaa"ya faɗa yana bude dan madaidaicin bakinsa.

Buɗe nata bakin tayi kamar yadda taga yayi, wanda yake nan ɗan mitsitsi kamar gidan tsutsa ,haƙora ta farare tass dasu,ajere reras.

"Masha Allah "Adeeb ya faÉ—a cikin rashin sanin ya furta hakan.
Saida ya faÉ—a kafin ya ankare.kallon fattu yayi suka haÉ—a ido,harara ya watsa mata yana mai cewa"kaki cinyeni da wannan lulu eyes É—in naki"Adeeb ya faÉ—a yana mai sanya burush É—in cikin bakin fattu.

Ahankali yake wanke mata haƙoran nata masu kyau da ɗaukar hankali,yana wanke wa yana kallon fuskarta,ita kuwa ta rufe idanunta ƙam!wani irin takeji bakin nata,gashi abun da shegen zaƙi, anya kuwa ba abin sha bane ya manta yace na wanke baki ne?
Aikuwa wllh saita ɗan sha taji ya faɗinsa yake.Adeeb bai sankara ba kawai yaga ta tattara kumar bakinta ta haɗeye ƙut!

Zaro ido yayi tare da buÉ—e baki cike da mamaki yace "what!!" Kin shanye kunfar?oh my God" ya faÉ—a yana zare burush É—in daga bakinta.
Yace "oya fito dashi"ya faÉ—a yana zare mata idanu.

Shagwabar fuska fattu tayi kafin tace "ai na shanye zaƙi gareshi" ta faɗa tana mai sunkuyar da kanta.

Girgiza kai kawai Adeeb yayi,baice komai ba ya kunna fanfo yace ta tara ta kuskure bakin,

Hannu ta saka ta tari ruwan sannan ta kuskure bakinta.wani fayau taji bakin nata yayi ,sosai taji yayi mata daÉ—i ga kamshin strowberry da bakin keyi.

Nuna mata ruwan wanka yayi yace tayi wanka ,yanzu ta fito yana jiranta.
Kai ta daga masa,tana nufar gurin da boket É—in yake ajiye.
Harya kama handle É—in kofar sai kuma ya juyo yace "kiyi alwala anan"ya faÉ—a yana nuna mata jikin sink din tare da ficewa.

Zama yayi abakin gado bayan fito daga toilet É—in ,haka kawai yaji yana cikin farin ciki,sai murmushin yake,abinda ba al'adar shi bace yawan fara'a.

Fattu kuwa ko minti biyar batayi ba ,sai gata ta fito sanye da Kayan ta data cire .

Kallon ta Adeeb yayi yace " ina kayan dana baki?"
Miƙa masa al'adar tayi tana mai cewa"bazan iya sawa ba harɗe Ni zasu yi"

Kallon ledar yayi sannan ya lalle ta, karba yayi tare da budewa ya zazzage,doguwar rigar baƙa mai dan faɗi sai ɗan kwalin rigar shima baki,kuma yana da girma.wai amma sune bazata iya sawa ba '
"Take it ,ya faÉ—a cikin hade fuska.
Kallonsa tayi, tare da karɓar ledar,bawai dan ta ji me yace ba ,saidan taga yana miƙa mata ledar .

"Wuce kije kisa"ya faÉ—a ba alamun wasa afuskarsa.

Juyawa tayi sumi"sumi ta koma toilet ɗin ,amma bata rufe ƙofarba ,ta yadda dataji burum,zata arce.

Haka ta cire kayanta ta sanya wanna doguwar rigar ,masha Allah rigar tayi mata kyau sosai ,saita fito ras da ita.maimaiko ta lulluɓa dan kwalin ,sai kawai ta daura akanta.,sannan ta sanya kayanta wanda ta cire cikin ledar sabon kayan.
Fitowa tayi tana tattare rigar ,dan harga Allah jinta take aharharde,tafi don tsangalallen ,zaninta.

Tana fitowa Adeeb yabi ta da kallon,aransa yana mai yaba irin Khan da tayi ,amma jibi yadda yake wani dage rigar.

"Hamma a ina zanyi sallar?ta faÉ—a tana kallon gefensa.

Shiru yayi yana kallon ta kafin yace "zo nan"
Cikin tsoro take takowa har zuwa kusa dashi,tana fatan kar yayi mata faÉ—a irin na É—azu.

Mikewa yayi tare da zare ɗan kwalin kanta,ya warware shi tare da yi mata rolling irin yadda yaga amminsa da ƙannansa nayi.

Masha Allah ai nan danna fattu ta fito abalarabiya sak, tayi kyau sosai da sosai,kamar ba fattu yar fillo ba.

"Kije can kiyi sallah"ya faÉ—a yana nuna mata kan dardumar da yayi Sallah shima.

Bayan ta idar da sallar Adeeb yana kallon ta,masha Allah ba wani kuskure cikin sallar Tata,dan fattu tana da ilimin addini sosai.

Abinci ya nuna mata yace tayi sauri taci zasu tafi.bata wani ciabincin kirki ba,dan ji tayi sam abincin baiyi mata daÉ—i ba,tafi son tuwo ko madarar shanu.

Shima bai wani damu ba ,dan yaga bataci abinci ba sosai.tashi yayi yace mata suje .
Yayi gaba tana binsa abaya. Riƙe da rigarta, hannun dayan kuma tana riƙe da ledar kayanta.

Suna fita daga hotel ɗin kai tsaye gurin masu saida waya ya nufa , wata ƙaramar waya ya siya da layi,ba tare da ya tambayi kuɗi su ba ,naga ya bada duka kuɗin nan dake cikin leda,dan dama suna hannunsa,wanan rigar kawai ya cire daga ledar,sosai naga mai saida wayoyin yana ta murna da godiya har kasa ya durƙusa yana godiya.

Haɗa wayar Adeeb yayi tare da sanya layin ,kati ya karɓa gurin mai saida wayar ,aikuwa da sauri ya ɗauki mata na dari biyar ya mika masa.
Wata number naga ya daddana cikin wayar,bayan ya gama sanya katin acikin wayar.

Magana ya farayi cikin harshen larabci,bayan anÉ—aga wayar daya kira.ni dai ba dan me yake cewa a,saidai naga kamar yana kwatancen inda yake ne.
Bayan ya kammala wayar ne yana ƙoƙarin sanyata cikin Aljihu,kawai yaji mutum yana ƙwaƙwumarsa kamar za'a shige cikin jikinsa.

Da sauri ya kalli gefen hagunsa ,inda tanan yake jin alamun mutum ɗin,aikuwa fattu ya gani tsaye ta kama gefen rigarsa,jikinsa har rawa yake tana ɓoye fuskarta ajikinsa.
Chapter 13 · 0% Book details