Sashe 1
Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[7/14, 1:00 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJINE SHI🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 1
Bismillahir rahmanir rahim, Ina godiya ga Allah daya bani damar fara wannan littafi, bayan kammala littafin soyayyata. kasa yadda na fara lafiya naga bayansa lafiya ameen.
Gargadi banyarda wani ko wata ya juyamin wannnan littafi ta kowace sigar ba.
_______________Wata kyakkyawar yarinya na hango sanye da kaya irin na Fulani, wato rigar saki da kuma zaninta, duka duka rigar da kadan ta wuce cibiyar ta, saidai kuma ta daura zanin da ya rufe mata cikin nata ta yadda ba wanda zai ga jikinta awaje.
Farace irin mai sirkin yallow -yellow din nan, tana da doguwar fuska mai kyan tsari dauke da dogon siririn hanci har baka, bakinta dan karami kamar gidan tsutsa, tana da irin manyan idanunnan masu kamar tana jin barci, ga gashin ido zara -zara.
Girarta kuwa, kamar wacce aka dora Mata ita dan saiti, gaban goshinta wasu yan kananan gashine kwance lub lub kamar na jarirai.
Masha Allah yarinyar ta ko ina ta hadu, dan doguwace marar jiki saidai fa Allah ya hore mata hips Kai kace wata babbar macece Sannan akwai alamun girma akirjinta, ma'ana dai akwai dukiyar Fulani da suka fara tasawa akirjin nata.
Duka duka wannan yarinyar bata wuce shekara 15/16 ba, amma kallo daya zaka yi mata kasan Allah yayi halitta agurin.
Sandace irin ta Fulani ahannunta tana dagawa sama, da alama tana son hada kan wasu tarin shanu ne dake kiwo cikin wani kayataccen jeji, dan kuwa ciyawace agurin Kore sharr da ita, shanun suke ci abinsu .
Tafiya ta farayi gurin shanun dake dan nesa da ita, dan ita tana daga jikin wata bishiya ne tana kallon yadda suke kiwo abinsu.
Kanta ta daga ta kalli yadda garin ke hada wani irin hadari baki kirin dashi, kuma da alama koda yaushe ruwa na iya saukowa.
"Kuzo mu tai gida abokaina kada ruwan nan ya sauko ya taba mu, don aradu banin son nai mura"
Cikin Yaren fulatanci take musu magana, tana daga sandarta. Aikuwa kamar wanda suke jin me take fadi suka fara yin hanyar gida .
Murmushi tayi tana mai binsu tana kara daga sandarta sama sabo da suyi saurin karasawa gida.
Tafiya suke cikin jajen ita kadai daga ita sai wadannan garken shanun, sam ba alamun tsoro tattare da ita, sai yar wakar tama take tana cigaba da É—aga sandarta sama.
Kusan tafiyar minti biyar sukayi, sannan na fara hango bukkokinsu dake can gaba kadan .
AHankali annurin dake kan fuskar yarinyar ya fara dusashewa tamkar yadda hasken rana kan dauke a lokacin a ta zo faÉ—uwa. Nan da nan damuwa ta maye gurbin nishadi da take, sosai naga jikinta yayi sanyi har suka karasa wata bukka dake farkon rigar da alama nan ne gidansu.
Garken shanun ta fara zuwa ta daure su tsaf sannan ta nufi cikin gidan dauke da sallama.
Lokacin har anfara yayyafi .
Ba kowa a tsakar gidan nasu, hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da nufar wata bukka cikin sauri.
Saidai kafin ta karasa kofar bukkar aka daka mata wata uwar tsakar da saida sandar hannunta ta fadi kasa.
Afirgice ta juyi jikinta na rawa sosai kamar dan mazari, da sauri ta karaso gurin matar data daka mata tsawar
"Gani gwagwgo" ta fada cikin rawar murya. Ni kuwa sai na kalli matar duk da cewar farace amman kuma kazanta da rashin kulawa yasa tayi wani irin baki baki fari fari, sannan tana da jiki sosai sam fuskar ta ba alamun rahama a cikinta.
Tana tsaye a kofar bukkar ta tana hararar yarinyar dake durkushe gabanta.
Cikin masifa da bala'i matar ta fara magana da hausarta marar kyau.
"Da kake kokarin shigewa dakin, ubankane zai debi ruwan? Ko kin ajiye bawanki ne a gidan? matar ta fada cikin zaro ido.
Kan yarinyar akasa jikinta na rawa ta fara magana
"Allah hukkumu hakuri gwagwgo naga ruwa na dan sauka ne shiyasa ban deboba" ta fada cikin rawar murya gami da tsoro.
Wani wawan mari matar ta kai mata cikin rashin imani da tausayi cewar yanzu ta dawo daga kiwo kuma ko abinci bata ci amma take kokarin sake turata rafi.
"Shegen yaro mai bakin hali wllh yanzu dole ki dobo min ruwan nan dan ubanki karuwa kawai" matar ta fada tana mai hankade yarinyar cike da rashin imani.
Faduwa tayi sosai hannunta ya bugu da wani dutse dake ajiye tsakar gidan da alama na zama ne.
Kara ta saka cikin azaba tana mai dafe hannunta dake mata wani irin azabar raÉ—aÉ—i.
"Wayyo handi ɗin boni lalashewa gwagwgo hannu na ta ɓalle" ya rinyar ta faɗa cikin azaba.
"Shege wllh dama zai karye danafi kowa jin dadi yarinya kamar aljana, ace kinfi kowa kyau arugarnan? Na tsaneka fattu saina bata wannan shegen fuskan naki, ni maza ki tashi kona shakeki agurin ki mutu kowa ya huta" cewar matar cikin bala'i da tsantsar nuna tsana ga Fattun.
Cikin hanzarin ta mike ta zari wani bokitin roba ta fice tana kuka mai tsuma zuciyar ga duk wani mai tausayi.
Tafiya mai nisa tayi kafin tazo rafin, har zuwa lokacin kuka take hannunta sai zogi yake mata, ruwan ta debo cikin sauri dan kuwa ruwan da ake ya fara karfi.
Saidai me ? tana juyawa tayi arba da wani murtukeken maciji katon gaske ya fasa kai yana huci.
Wani irin mugun tsorone ya kamata nan da nan jikinta ya kama rawa har batasan lokacin da bokitin ya fadi kasa ya fashe ba.
Tashin hankali kenan wanda ba'a sa masa rana, iyakar ruÉ—ewa da tashin hankali yarinyar nan ta shiga.
Hannu ta ɗora aka tana mai kara ƙarfin kukanata.
"Wayyo ni fattun bukar na mutu na lalashe ya zanyi da rayuwata mashici zai karni wayyo baffana! wayyo Allah! A taimaka min"
Ta faÉ—a tana kallon botikin nata wanda ya tarwatse a kasa, dama kuma rana ta gama cin ubansa.
Shi kuwa macijin nan ganin yadda ta tsaya tana kallon sa kuma tana kallon fasashshen bokitin dake kasa, sai yaga kamar neman makami take dan haka afusace yayi kanta da mugun nufi.
Ihu ta kwalla mai karfin gaske tare da zubewa agurin sumammiya dan ganin yadda macijin nan yayi kanta baki bude don hakan ba ƙaramin tsorata ta yayi ba .
A Dai dai wannan lokacin ne kuma wani katon macijin ya nufo wannan macijin da gudun gaske, yana zuwa ya sarkeshi suka fara kaiwa juna sara. Hakan shi ya hana wannan katon macijin ya sami damar karasawa inda fattun ke kwance asume.
Sosai macizan nan ke kaiwa junansu sara suna murdewa cikin jikin juna, ko wanne yana iya ƙoƙarin wayen ganin ya illata dan uwansa.
Ahankali fattu ta fara bude idanunta da sukayi mata mugun nauyi tana kuma lumshesu, hannunta ta daga da nufin dafe kan nata, saidai wani azababben zafi da radadin ga wani irin zugi dataji hannun yana mata, shine ya sanyata sanya kara tare da fashewa da kuka. "Washhhh hannuna wayyo kaina" ta fada cikin kukan tana mai dafe kan nata da dayan hannun marar ciwon.
Sai kuma ta zabura cikin azama ta zauna tana mai zare idanu da rarraba su, sakamakon tunowa da katon macijin da yayo kanta dazu. Sai dai koda ta kai duba ga inda macijin yake sai ta hangi macizan sun zama biyu suna ta artabu, gaba daya sun jima kansu ciwo jini yana ta zuba akikkunansu, amma duk da haka sunki daina fadan.
Tsoro, fargaba, tashin hankali gami da rudewa suka saka fattu kurma wani uban ihu tare da yunkurawa ta falla da mugun gudu tana ihu cikin rudewa dan ganin macizan sun zama biyu wato har fada suke akan waye zai cinyeta kenan.
Duk da irin ruwan da ake zugawa mai ƙarfi ga iska, a haka tayi ta cin uban gudu ko gabanta bata gani ikon Allah ne kawai ya kawota gidansu lafiya.
Kai tsaye ta danna cikin gidan da gudu ta shige dan dakin dayake amatsayin nata, cikin rawar jiki ta janyo wasu karare dogaye guda hudu ta kara a kofar, dan sune ke a matsayin murfin kofar tata.
Dakin ba komai sai wata yar yaloluwar taburma, wacce kallo daya mutum zai yi yasan cewa taga duniya, dan gaba daya ta ciccinye kuma tayi lakwam da ita. Sai wani zani dake gefe daure, da alama kayan sawarta ne aciki.
Tana tsaye atsakar dakin, har lokacin jikin ta rawa yake, ga ruwa sai zuba yake ajikinta yararara!!!
Kallo daya zaka mata kasancewa afirgice take sai kif-kifta ido take tana kallon kofa, domin gani take kamar macizan nan zasu biyota. Tayi kusan minti biyar acikin wannan halin, kafin ta fara cire kayan jiki ta dake yararin ruwa "Masha Allah nace, sakamakon ganin wani uban dogon bakin gashi mai santsi akanta lokacin da take zame dan kwalin dake bisa kanta, an raba kan biyu an daure ko wanne bangare sai kuma aka nannade ko wanne a barinsa ya zama kamar gammo, wanda hakan da akayi shine ya hana mu ganin gashin nata tun farko.
Zanin dake É—aure a jinkinta ta kwance ta dauko wani zanin irin wanda ta cire da rigarsa, saidai kayan fa sun sha jiki sosai, sun kode sun jeme sunyi wani fari tas da su, sai wata hula baka irin ta sanyin nan ta dauko ta ajiye kusa da kayan, sannan ta mike tsaye ta cire rigarta ta ajiye ta gefen tabarmar, ahankali ta warware tsangalallen zanin shima ta ajiye gefe, ya zama daga ita sai wani kodadden pant Wanda kana gani kasan shima yaga rayuwa. Kallonta nayi tun daga sama har kasa kawai sai na kuma cewa Masha Allah a karo na biyu domin dai sura kam Allah ya halicce ta agurin fattu dan jikinta har wani sheki yake kamar yar masu kudi wacce ke rayuwa cikin jin dadi.
Haka ta dauki kayan ta saka ajikinta tanayi tana kuka abin gwanin ban tausayi.
Bayan ta kammala sanya kayan ne kuma saita dauki wanda ta cire ta matse sannan ta makalasu ajikin karan dake jingine akofar dakin nata.