Sashe 2
Macijine Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zama tayi akan yar tabarmarta ta dukunkune jikinta tana kuka. Abubuwa dayawa ke damunta ahalin yanzu, na farko tsantsar tsoron macizan data gani dan bata taba ganin irin wadannan macizan ba, domin dayan jikinsa mai matukar shekine da kyau, sai kuma hannunta dake mata azabar ciwo uwa uba ga kuma yunwa da ta addabeta, dan rabonta da abinci tun karin safe da tayi shima nono ne kawai ta sha, har kawo yanzu da magriba tayi bata sake saka komai a bakin salatinta ba.
Sosai take tausayi rayuwarta, tabbas rashin uwa babbar gibine a rayuwa, yanzu da innarta na kusa da ita, da tuni ta rungumeta ta fada mata damuwarta, amma rashin dace ta daya shine sam batasan koda fuskar innar tata ba, sannan tana raye ko ta mutu Allah shine kadai masani.
Tana cikin wannan hali ne taji an ture karan data rufe dakinta da shi.
Azabure ta mike tsaye tana shirin sanya ihu.
"Ke fattu nutsu mana nine fa, nine baffanki" wani dattijo ne fari dami da dan tsayi yayi maganar, yana sanye da riga da wando na wani yadi mai arha sai takalmin sau ciki na roba a kafarsa, da hula irin mai malafar nan. Ya shigo cikin dakin da wani kwano riƙe a hannunsa.
Ajiyar zuciya ta sauke sakamakon ganin baffan nata, da sauri ta karasa kusa dashi tace "Baffan usee wollahi na tsorata ne" ta fada idonta akan kwanon dake hannunsa.
Murmushi yayi yace "Hoo fattu akwai tsoro, sannu maza karbi wannan tuwon ka shinye nasan kanajin yunwa, kayi sauri kar hansai ta gani" yana gama fadin haka ya mika mata kwanon yayi saurin fita daga dakin, dan kar matar tasa ta fito ta ganshi ya shiga uku.
Cikin sauri - sauri fattu ke cin tuwon nan kamar zata kware, tas kuwa ta cinye ta side kwanan, sannan ta fice da sanÉ—a har takai tsakar gidan ta wanke kwanon ta ajiye dakin girki sannan ta sha ruwa tayi alwala ta koma dakinta.
Sallar la'asar tayi da magrib dan tuni an kira magriba.
Har zuwa lokacin ruwa ake saidai bai kai ƙarfin na farko ba. Tana zaune cikin zullumin matakin da gwogwgo zata dauka akanta, na fasa mata bokitinta da tayi, a haka har akayi isshai tayi salla sannan ta kwanta tana mai karanta addu'a, nan da nan barci yayi gaba da ita, har baffanta ya shigo ya duba ta yaga tayi barci addu'a yayi mata cikin tausaya wa halin kuncin da take ciki sannan yayi saurin fita.
Gwagwgo kuwa tana daki ita da yaranta suna ta hira suna cin gyada, ba ruwansu da wane halin fattu ke ciki, shin ta dawo gidanma ko yaya taci abinci ko bata ciba? Sam ba wanda ya damu, kuma ba wanda yayi Sallah a cikinsu.
Can cikin dare Fattu na barcinta sai dai cikin damuwa da tsoro take yinsa domin kuwa mafarkin macijin nan take, saidai kuma ba na farkon bane yazo mata yanzu wannan mai kyakyakywan jikin nan ne, amman gaba daya jikinsa jini yake zubarwa, ga wani irin hayaki da tururi dake fita ajikinsa, sai burkima macijin yake yana wani irin kuka da wata murya mai amon sauti, kuma yana nufota da ƙoƙarin hawa jikinta .
Wani razanannen ihu ta kwalla tare da mikewa zaune afirgice, tana mai waige waige, ba abinda take iya gani saboda duhun dakin, hakan yasa tayi saurin komawa ta kwanta tare da karanto adduoi kala-kala, hannu ta mika dan janyo zaninta ta rufe jikinta dashi, saidai kuma hannun nata taji ya sauka akan wani abu mai dan karen sanyi da santsi.
Cikin tsoro take shafa abun dan jin ko menene, tabbatas MACIJINE dan kuwa ta tabo har kansa ....
Masu karatu badai macijin ne ya biyo fattu da gaske ba?
Wane hali fattu zata shiga ?
Muje zuwa yaki ce dai anty mammy
Mrs babi💘💘💘
Share and comment fisabilillah.
More comment
More typing.
[7/14, 1:01 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: MACIJE NE SHI
3/4
🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJINE SHI🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
https://www.facebook.com/groups/2803452939899949/?ref=share
Free book
Page 3/4
________________Cikin tsoro take shafa dogon abun dan jin ko menene, tabbas MACIJINE dan kuwa har kansa ta taɓo.
Aikuwa da hanzari ta janye hannunta cikin kidima ta fara ja baya tare da fasa wani irin gigitaccen ƙara,
"Wayyo Allah baffa maciji! maciji!! maciji!!!" Gaba É—aya ta kidime abinda take iya faÉ—i kenan jikinta na rawa kamar É—an mazari.
Allah Sarki baffa dama ba wani barci yake yi ba, dan yana kula da ɗakin fattu, kasancewar ɗakin yana gaf da ƙofane, dan haka jin ihunta da yayi, yasa shi tashi agigice ya nufi ɗakin nata.
Haskawa yayi da tocila can ya hangota jikin bangon ɗakin ta duƙunƙu ne tana ta ihu, da alama batama cikin hayyacinta.
Da sauri ya nufeta yana kiran sunanta" fadimatu! ke fadimatu menene? Ya isa haka gani akusa dake baffanki ne kinji daina ihun " Baffa ya faɗa cikin ƙasa ƙasa da murya dan kada ya ƙara tsorata ta.
Ita kuwa gaba É—aya ta rikice kawai kira take "Baffa maciji zai sareni Baffa wayyo Allah na"
Ganin halin da take ciki ne yasa Baffa ya fara tofa mata addu'a, cikin minti biyu kuwa tayi shiru sai rawa da jikinta keta famanyi, ahankali ta daga kanta ta sauƙe kyawawan idanunta akan baffan nata, kawai saita saki kuka tana mai cewa "Baffa MACIJINE yake son ya sareni aradu da idonsa na ganshi anan" ta faɗa tana nuna masa gurin dataga macijin.
Kallon gurin baffa yayi, shifa ba abinda ya gani agurin, kawai yana tunanin ko mugun mafarki tayi ne, dan haka cikin ƙokarin kwantar mata da hankali yace "shike nan fattu ya tafi maza koma ki kwonta kiyi addu'a Insha Allahu ba bu abinda zai sameka kinji" ya faɗa cikin yanayin Hausar su ta Fulani.
Cikin kuka take girgiza masa kai "Aradu baffa dawowa zaiyi tun daga rafi suke son cinyeni fa, bazan iya kwonshiya Ni kaɗai ba" ta ƙarasa tana mai matsowa kusa da baffan.
Shiru yayi yana tunanin mai ya kamata yayi, dan gaskiya yaga ta tsorata da yawa, dan haka cikin ƙarfin hali yace "Tashi muje gurin Hansai saiki kwonta shan ko" ya faɗa cikin tausaya wa.
Ai kafin ma ya rufe bakinsa ta kai ƙofa, dan ita kam babban burinta ta bar ɗakin nan, tama manta da gurin wa baffan yace taje.
Ahankali baffa cikin É—an tsoro yake tura murfin É—akin na hansai harya buÉ—e shi duka. Ya taddasu suna kwance abinsu kan gado ita da yaranta su uku, na miji É—aya sai mata biyu Dukansu basu kai fattu shekaruba, da alama na mijin zaiyi shekara sha uku, matan kuma basu fi sha daya ba.
Kuma dan rashin tsari irin na goggo Hansai da ita da yaranta duka suke kan gadon kuma na mijinta.
Ahankali baffa ya karasa yana dan bubbuga fillon da hansai ke kwance, sai uban munshari take zabgawa, banda wari ba abinda dakin keyi.
"Hansai! Hansai!!" Baffa ya faÉ—a cikin Muryar tsoro, dan yasan idan ta farka sai tayi masa bala'in ya tashe ta tana barci.
Juyi tayi tare da goge yawun barcin dake zuba abakinta taci gaba da barcinta abinta. A hankali ya fara kiran sunanta da É—an karfi "Hansai ! Hansai!!" Har sau biyu.
Buɗe ido tayi ahankali ta sauke su akan baffa dake tsaye, buɗe idon tayi sosai cikin bala'in ta tace "To jarabarce ta motsa haka da cikin dare zaka zo ka dameni? to wllh garama ka koma inda ka fito dan ba abinda zaka samu agurina, wannan jaraba dame tayi kama, ko sati biyu bakayi da saukemin jarabarka ba shine yanzu ka ƙara jajiɓo jiki kazo ka sake ko? To wllh banda lokacinka kaficemin daga ɗaki" ta faɗa cikin masifa tana mai juya masa baya.
Girgiza kai yayi cikin jin kunyar fattu, dan yasan taji abinda gwogwgo take faÉ—i, kuma ai ita ba yarinya bace bare ace bata san me hakan ke nufi ba, tunda tana karatun addini.
Cikin sanyin murya yace "Ashsha Hansai ba wannan ta kawoni ba, dama ina neman alfarmar fattu ta kwana anan ne daku, dan bazata iya kwana ita kadai ba, atsorace take "ya faÉ—a cikin shakkun zata amince ko yaya.
"Kan ubannan yau kuma da wannan sabon munafurcin kuka zo? Fattu ta kwana a É—akina, lallai in baka mutu ba zakaga ikon Allah, da can da ubanwa take kwana? sai yau zakace ta kwana aÉ—akina? yarinyar mayya wato cikin dare ta lashemu ko? kai baka da asara, To, ku ficemin aÉ—aki Allah yasa abinda yake tsoratatan ya cinyeta ta mutu kowa ya huta "tana gama faÉ—in haka ta juya taci gaba da barcinta.
Sosai maganganunta suka ɓatawa baffa rai, saidai bashi da damar magana, kai kawai ya girgiza yace "Muje Fattu"
Kuka sosai fattu keyi na tausayin su ita da baffanta ga wannan matsalar dake ƙoƙarin Kunno mata kai, basu da gata sai Allah kawai.
Suna fita baffa yace "shiga É—akina ki kwanta fattun, ni bari na je É—akin naki kinji" ya faÉ—a cikin sanyin murya.
Girgiza kai tayi tace "Baffa Zan koma É—akin nawa In kwanta kaima kaje É—akinka, idan gwagwgo tasan na kwana aÉ—akinka yanka ni zata yi, dan ta hanani shiga É—akin" ta faÉ—a tana mai share hawayenta tare da nufar É—akin nata gabanta naci gaba da bugawa.
"Kiyi hakuri fattu komai yana da iyaka kinji, Allah zai miki sauyi na alkairi" Baffa ya faÉ—a yana mai mika mata tocila ya ce ki haska ki kwanta kinji, sannan kada ki manta da yin addu'a" Karba tayi tare da É—aga masa kai ta koma cikin É—akin.
Daga bakin ƙofa ta tsaya tare da haska ɗakin ko ina, ba abinda tagani aɗakin, hakan yasa tayi zamanta bakin ƙofar ɗakin da tocilan ɗin ta ko yaya taji motsi saita zabura ta haska .
Sam awannan daren bata sami damar runtsawa ba, ga sanyi da garin ya ɗauka sakamakon ruwan da aka zabga jiya. Sai gabannin asuba sannan barci ɓarawo ya saceta.
Wani irin azababben sanyi daya ratsa ƙasusuwan tane sakamakon ruwan sanyin da gwagwgo ta kwara mata, shine ya sanyata zabura ta miƙe da sauri tana haki, kafin ta gama dawowa cikin hayyacinta kuma taji duka yana sauƙa ajikinta ta ko ina, ihu ta fara tana neman taimako amma ba wanda yazo dan taimakon nata, dan baffa yana masallaci kasancewar shine limamin rugar.