← Book details Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 57

Sashe 9

Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaka ummi zabura tayi Allah maka albarka Umar yarinyar nan bata da kunya wlh wani halin banza ta dakko na son girma,gashi bata jin maganata na rasa inda zanyi da iklas wlh ka ganta duk wannan haukan da takeyi sauri takeyi zata je party na makwafta.dan ta taba taimakamana shine wai dole sai taje partynta na murnar zagayowar haihuwa,

Giya fa suke sha a wurin umaru rawa maza da mata a cure ana badala nayi nayi akan Kar taje amma takiji,bata jin maganata sai abinda ta tsarawa rayuwarta kaka ummi ta fashe da kuka wiwi.

Asmahbaffa
[17/03, 21:45] Hadiza Sani Fbk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

10

By
Asmahbaffa

Wannan shafin nakine MAMAN WALEEDA ina godiya sweet sis.

Kiyi shurunki ummi yanzu zan kula da ita duk wani iskanci da take ji dashi zan gyara ta,cuno baki iklas tayi ta bar palon,wanka ta samu tayi ta palon ta wuce sanye da hijab,kwalliya ta tsantsara ta sa daya daga cikin rigunan da ta siyo rannan a kasuwa wata yar gaunt me dogon hannu ta haura gwiwa da kadan,daga sama ta matse kasa ta bude,orange and black color tayi kyau ba laifi harda yafa siririn gyale orange wai ita a dole zata birge,tayi shiga me kyau,don kaya manya su atamfa nauyi suke mata,bata saba ba sam,batan me yasa take so yau tayi kyau ba.wuce su omar tayi a Palo ta koma kitchen hade da kiran suhaila,abinci suka Jere a gaban omar,kallonta omar yayi tayi kyau amma wai ita bata sa kayan kirki ne?ga bako ai kamata yayi ta suturta jikinta,wato kowa haka yake kalleta tab,ummi ce tayi magana umaru bari inje makwafta zanyi ta'aziyya anjima kadan zan dawo ba dadewa zanyi ba ka jirani,ba matsala ummi sai kin dawo,kallon iklas ummi tayi tace sai ki zauna wajensa na dawo uwar giggiwa kullum aikinki kenan yawo da watsatsun kaya,zigidir kullum da kayanki ba babu.

Umaru kaci abincin dan Allah kaji,ko albarka kasa mana,kar ka bari na dawo na tarar baka ci komai ba,bazan ji dadi ba.ok ummi cewar omar.
Fitar ummi keda wuya dakin yayi dif ba Wanda yayi magana ga suhaila tayi bacci,sadda kai kasa iklas tayi bata son kallon omar wani faduwar gaba take ji,

Kallonta yayi fuskar sa daure,ke a tsawace yayi maganar wato bakyajin magana ko,tun baki tafasa ba za ki kone kamarki har kin isa zuwa wani party kuma partyn na wasu tambadaddun yare,tsohuwa na zaune daku kina bata mata rai,ki kiyayeni wlh,da na kowa ne bar ganin bamu hada dangantaka ba duk lokacin Dana kamaki,ko na ji kin yi abu rubbish sai na hukuntaki.itafa iklas mamaki ya gama kasheta irin karfin halin omar,ina ruwansa da rayuwarsu wai,sai kace ubansu,ko wani sabawa dajuna basuyi ba amma yake wani fada haka,lallai ma,Nima asmah naga shishigin omar anan.

Turo baki tayi to birthday din maman ola ne fa sir,kuma....shut up ba inda zaki .to ai dama na hakura sir cewar iklas a sanyaye,karma ki hakura.shuru dakin ya kara dauka can tace sir?Ina jinki,kaci abincin mana to,jagwalgwalonki zanci an fada miki ina cin girkin irinki,dama ummi ce tayi sai na ci.shuru ta masa dan taji haushin kalamansa,ta rasa why take daga masa kafa,ita da take masifaffiya bata kyalewa amma akan omar ta kasa daukan mataki.ba komai ko dan taimakon da yayi mana zan dinga kyaleshi.bani ruwan nasha kawai s ok ma maganar omar ta katsewa iklas tunani,da sauri ta mike ta fara tsiyaya ruwa a wani glass cup me kyau da tsafta,cikin izza ya karba yasha hade da mikewa tsaye idan ummi ta dawo na wuce ni ki sanar mata

Pls ka bari ta dawo mana ko ka tsaya na kira ta yanzu pls,sallamar ummi sukaji ta shigo palon,yawwa ummi zai tafi wai cewar iklas kuma baici komai ba wlh,hangame baki ummi tayi haba umaru ya zaka Mana haka,mu ka taimakamana mun yarda mun karba duk da bamu sanka ba,ba dangin iya ba na baba amma mun yarda da kai,yanzu dan mun baka abinci shine baza ka ci ba,kamar mun baka guba ko wata cuta.

In dai kana so mu shirya gaskia kaci ko kadan ne idan kuma kyankyami kakeyi bazan ma dole ba.da sauri omar ya koma ya zauna haba ummi ba wani abu kiyi hakuri bari naci.baki ummi ta washe haba ko da kaifa amma ai sai ka sa muji ba dadi ai,iklas zuba masa bari naje na karasa gyara wasu kaya.omar ji yakeyi tsohuwar na birgeshi,kallonta yakeyi kamar mama.

Tana bude flask wani kamshi ya daki hancinsa me dadi,fried rice lafiyayya tasha hadi da su hanta etc,zuba masa tayi ta kara bude wani bowl me kyau na glass kaji ne soyayyu zuba masa tayi a gefe ga hadadden salat,mika masa tayi ta zuba masa lemon kwakwa.

Yatsina fuska ya dauki spoon da kyar ya fara ci,wani arnen dadi yaji kamar kunnensa zai fita,sai santi yakeyi a ransa a fili kuwa yatsina fuska kawai yakeyi,iklas na kallonsa kafafunta sunyi sanyi tun a fuskarsa ta gane baiji dadin abincin ba,kamar zatayi kuka bata San ace girkinta baiyi dadi ba.

Musamman a wajen Omar bata San me yasa take so ya yaba girkinta ba.idonta har ya Tara kwalla kadan,omar yana kallonta ya gama ganota tsab,a ransa sai daria yakeyi,ganin kaka ummi bata kusa yasa yake ta wannan yatsina fuska,tunda yaga yanayin iklas ya kara yatsine fuska dan yanzu har yi yakeyi kamar zaiyi amai,abin mamaki yaci abincin yafi Rabin plate,lemon ma yasha yaji dadi amma harda rike ciki wai a dole yaci guba.can yace kai ummi ta takura naci jagwalgwalo,babu dadi haka akeyin girki,wannan ai sai ki kashe mutane.

Hawaye ne ya digo dis daga idon iklas da sauri ta goge kar sir omar ya gani Wanda ta Riga ta makaro a idonsa tayi komai.kitchen ta shiga sai gata ta fito da wata Leda me kyau a hannunta,mikawa Omar tayi ga wannan ka kaiwa mom dinka,

Tunaninsa ne ya tsaya cak wannan yarinyar akwai mamaki acikin alamarinta,wai tana 15yrs har tasan ta bawa mamansa kyauta yaji dadi kuma ta kara birgeshi.karba yayi hade da cewa tnx kira ummi,sai gani yayi iklas ta tsaya rubutu a jotter bai San me ta rubuta sai da ta gama ta wuce kiran ummi,ita kuwa iklas ta Riga tayi lissafi wannan week din sunyi dambun naman kaza gashi basu ci ba ta bayar kyauta,shi yasa ta canja lissafinta..sallama omar ya musu ummi ma ta bashi sakonta ya ba mama,

Gidansa yaje ya duba lafiyar sahar sabo da amanar aure dake kansa,yar aikinta ya tambaya ina sahar ?ranka Dade tayi tafiya yau tace a fada ma ta tafi kasar ghana akwai wani aiki za suyi..ok kawai yace ya koma gidan mamansa,abinda Omar bai sani ba sahar ta kara lalacewa sai matan manyan alhazawa take kulawa Wanda suke da naira,wata kawarta hajiya talatu matar wani gomnace ita ta bawa sahar shawarar tunda kullum a hanya take ga mijinta ba wani shiri sukeyi ba kuma sahar akwai tsananin sha'awa kawai tunda tana da kudi a hannu ga maza nan samari yara sai ta zaba tunda yanzu matasa sun zama kwadayayyu kudi suke nema ta ko wacce hanya komai kudi,to ta mori dukiyarta ta samu wasu suna biya mata bukatarta tana biyan kudi.amma ta daina zubar da ajinta wurin omar mijinta tunda shi baya taba nemanta itama ta daina kai kanta.wa'iyazu billah mai makon muyi kokari mu gyara halinmu sai mu kara dilmiyewa mu jefa kanmu halaka wacce har ka mutu kana da na sani.Allah shiryamu gaba daya.dan yanzu wannan ya zama ruwan dare wurin wasu matayen musamman masu naira

Mama na room dinta tana shafa magani a kafafunta da suke mata ciwo omar ya shigo da sallama,da fara'a ta amsa masa babanmu ina ka shiga ne haka ban ganka ba,maganin ya karba ya karasa shafa mata,ina gida mama ga office ba sauki,omar kenan na dauka ma ko suruka ta biyu ka samo min,murmushi yayi mama aure tun yanzu zan kara aure,ina zan kai matan dayar ma da za a yagemin ita so nakeyi,daria mama tayi omar sai hakuri dan kawai ba auren so aka maka bane kuma matar taka ba ayi dace ba shi yasa ka fadi haka,

Mama kinji yanzu na dawo gida wai ta bawa yan aiki sako a fada min ta wuce Ghana,duk yawon da takeyi kasar nan bai isheta ba mama.mama ma ranta ya baci da jin abinda sahar tayi,ka bari zanwa baffanku magana a waya sai aje gidansu a sanar da iyayenta tunda ta Gagari kowa,ni ma zan kirata a waya,mama ki kyaleta pls kar tazo tana miki rashin kunya kin San bazan kyale ba.ya isa omar dole a fada mata gaskia.to mama ba matsala.ledar da iklas ta bashi ya mikawa mama,ledar kaka ummi ma ya mika mata gashi mama sunce a baki kuma suna gaisheki,murmushi tayi na gode Allah saka,amma banana wannan su waye suka bani bazan bude ba sai ka fada min,ohh mama wannan red din na kaka ummi ne wannan kuma na jikarta iklas,

Murmushi mama tayi tana jin dadi tana fatan abinda tayi tunani ya zama gaske,a fili tace ban ganesu ba ai...uhm..uhm yana Sosa kai yace aikine ya hadamu gidan gona.kyaleshi mama tayi, tace angode kaga mutanen kirki bari mu gani mene ciki.

Ledar iklas ta fara budewa wata katuwar farar roba ce mai murfi shake take tam da dambun naman kaza iklas yinsa tayi musamman sabo da suhaila na sonsa ganin omar yasa ta canja idea ta juye masa duka me uban yawa ta bawa mamansa.mama taji dadi sosai,ta bude ledar ummi kayan kamshi ne da sauran abubuwan miya busassu.mama sai murna takeyi omar har mamakin murnar mama yayii,babana ya kamata ka kawo min su na gansu ko ka kaini gidansu,ba yanzu ba mama to allah kaimu koma yaushene.kasan bana cin maiko sabo da ulcer ta,kadan zan iba ni da su abdullah.dauki wannan kaje dakinka dashi..da kyar ya karbi na robar wai a dole bayacin girkin yara,amma ya dauke ya wuce room dashi yana bata rai da muzurai.

Sadiya na hango sai masifa take zazzagawa tana dura ashar a compound din gidan,duk wani ma'aikata sunyi luf suna jinta,suleim na hango da uniform jikinta tsugune a gaban sadiya tana faman bata hakuri,anty sadiya kiyi hakuri ban San takadar tana da amfani ba shi yasa Dana gani na yaga na zuba a dustbin,
Chapter 9 · 0% Book details