← Book details Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 57

Sashe 5

Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Omar na hango yana tafiyarsa ta takama sanye da wani blue jean pencil da red din Riga me dogon hannu,wandon irin an dan farfasashi daga gwiwa zuwa cinya,amma ba me yaga ba dan ba a ganin jikinsa,driver ne da sauri ya bude masa wata sabuwar arniyar farar mota,yana yin ribas motar sahar ta cinno kai gidan,tsadajjen gogon hannunsa ya kalla yaga almost 5pm,kawayenta ya hango biyu a cikin motar.horn ta masa hade da daga masa hannu,haushi ne ya kamashi, wurin 2days baya ganin sahar sai yau,ko yaushe tace duty dare ne da ita,kwana takeyi a hospital,yanzu kuma da rana yawo da kawaye da shirme a gari aikinta kenan.sai shewa sukeyi da frnds,wurin babban abokinsa sultan ya wuce,sultan doctor ne babba shekarunsu daya tare sukayi schl a london,har secondary,sultan babansa ya rasu daga shi sai mamansa,sun gaji dukiya ta gaske shi da mamansa,sultan baiyi aure ba amma an kai kudin aurensa gidan wata yar beauty dinsa yasmin,a asibitinsa ya sameshi zaune a office,hannu ya mika suka tafa sultan yace shegen kaya ya kk,ka dawo amma sau daya ka nemeni,omar yace bari Frnd kasan office ba Hutu,baffa ya hadani da aiki,oh na zata amarya sahar ce ta boye min kai,kana can kana Jan kaya,tsaki omar yaja kaifa dan iskane sultan,kasan komai tsakanina da ita kana min tsiya,Allah kyauta cewar sultan,kaga malam gobe around 1pm zaka rakani wani company na baffa zan duba aikin da akeyi,kasan da nisa fa sai an bar garin abuja.

Allah kaimu cewar sultan.wai Frnd har yau baka samu wacce kake so bane,tsaki omar yaja karka dameni malam.daria sultan yayi yana ci gaba da tsokanarsa.

Washe gari kamar kullum 1pm tana titin kwalta sai bin motoci takeyi a round tana daga apple da kwanta a ledoji ,ga yayyafi anayi ruwa ya jiketa da dangalalliyar rigarta wacce taje gidan kaji da ita,duk ruwan sama ya jikata kayan sun kara dameta a jikinta,sai boobs dinta kana kana duk sunyi caro caro,hips ya fido,gashinta ya kara kwantowa a goshinta sai digar ruwa sukeyi,

Omar da sultan suna bayan mota a lafke driver na jansu,suka kawo dai dai danjar da iklas take,suna tsayawa ta karaso wurin motar tasu ga iska ta taso haka take daga musu,ido hudu sukayi da Omar wata uwar zabura yayi hade da nunata da yatsa yace you? Bata jin me yace saboda glass din motar a zuge yake,amma ta karanta lips dinsa ta gane me yace,murmushi tayi me kayatarwa ta daga masa hannu,itama tace oga da karfi,yaji abinda tace ai bai San sanda ya saki murmushi ba,yawa driver umarnin zuge glass kasa,kallonta yayi yanda iska ke daukanta,gashi ta falle mata gyalen da ke kanta gashi yaraf har kusan duwawunta,iska na kadashi sai ta kara kyau,driver yawa umarnin karbar apple da egg din hannunta,dubu biyar yawa driver umarnin mika mata,yana bata ta karba ta duba,hangame baki tayi ta dauki dubu daya,dama shine kudin apple dinta da egg da suka karba,ta mikawa driver sauran,da sauri omar ya kalleta yace karba nakine na baki,daria tayi ta glass ta girgiza kai tace tnx oga amma bazan karba ba.lips dinta ya karanta ya gane me take nufi,hannu ta daga masa ta juya cikin nutsuwa ta dauko dan gyalenta ta wuce,omar kasa dauke idonsa yayi daga kanta,sultan kuwa tuni yayi suman zaune yana kallo da mamakin abokinsa tare da jinjina kyau irin na iklas.

Danja taba da hannu amma omar sai waiwaye da kallon iklas yake,yanda take kai kawo a tsakiyar titi,yarinya irin wannan amma tana wannan sa'ar.take yaji ransa ya baci tausayinta ya mamaye zuciarsa, yar waye wannan aka barta tana garari a titi,tana da kuruciya haka,musulma.

Asmabaffa
[17/03, 21:45] Hadiza Sani Fbk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

6

By
Asmabaffa

Tsaki omar yaja,a ransa yana gaskia an cuci yarinyar nan.sultan Wanda mamaki ya kasheshi shi yayi karfin halin taba kafadar omar frnd ,juyowa omar yayi lfy malam karfa ka takuramin,murmushi sultan yayi yace iyye Ashe kayi sabon kamu frnd wannan zukekiyar fa gaskia tana da kyau,amma ka bani mamaki omar duk matan turai da yawon da kayi a duniya ban taba ganin ka kalli mace da idon rahma ba,amma gashi akan yar yarinya me talla a titi gaba daya ka haukace ka fita a hankalinka,harara omar ya balla masa,kaga halinka ko sultan,me zanyi da wannan yarinyar,tsaya malam nifa ka gama kasheni da mamaki omar kai da baka shiga shirgin wani bare har ka taimaka masa ba tare da ya nema wajenka ba,hasali ko mu maza sai mu Dade bamu ga murmushinka ba sai gashi karamar yarinya tatsitsiya kakewa murmushi haka har hakora su fito,ka bata kyautar kudi bata nema ba,tana kin karba kana tursasa ta kan ta karba,,harda siyan abun titi kai da baka cin abun kan hanya.

Sultan wai pls mene haka what is ur problem kasan me ya hadani da ita,za kazo kana wani talk na shirme,yarinya karama zanso,me zanyi da wannan me talla a titi,tallan ma mafi muni,tausayinta naji shi yasa.

Sultan ne ya kwashe da daria mai da wukar amma wlh wannan yarinyar ka fara sonta ko kaki ko kaso.da karfi omar yace God for bit,over my death body.daria sultan yayi ya leka fuskar omar inye anyi budurwa me kyau,gaskia ka iya zabe,dama omar ka iya murmushi haka me kyau,nima naci albarkacin new catch dinka na gani yau,tsaki omar yaja sai kayi ai.

Driver na jinsu shima ya yarda da zancen sultan,minti kadan za kaga sultan nawa omar daria sai dayaga omar yakai wuya wajen bacin rai ya ja bakinsa ya tsuke,dan yasan halin omar kwai zucia da zafin rai,sultan ne yace idi driver miko mana apple da kwan nan muci girkin amarya,omar ko kallonsu baiyi ba,ana miko kwan da apple omar ya fisge a hannun sultan,baka isa kaci abun nan ba sultan,

Daria sultan yayi au na manta hannun amarya ya taba abun kana kishi kar mu rigaka ci.shi dai omar shuru ya musu,har sukaje suka gama abinda zasuyi omar na fushi da sultan,a hanyarsu ta dawowa omar sai zare ido yakeyi ko zai hango iklas bai ganta ba.

Sultan ne ya kalleshi ya kara kwashewa da daria am sorry Frnd ban San dariar zata fito ba,amaryar ta tafi gida ka daina waige waige,tsaki omar yaja ya dauki apple daya cikin Wanda ya siya wurin iklas glass ya sauke ya zura hannunsa ta window ya wanke apple dinsa fes da ruwa ya kama cin apple dinsa ji kake baras,har wani lumshe ido yakeyi,sai daya ci guda biyu,ta karfi sultan ma yaci biyu,aka bawa driver ragowar biyun,

Can suna tafiya a mota omar ya kwance ledar kwai yaci daya ya mikawa driver duka.sultan harga Allah abin na omar ya shiga bashi tsoro kamar tsafi,omar da baya cin abun hanun yara,gashi bayacin abunda rana ta dakeshi a kan titi,yau gashi hankali kwance har dafaffen kwai na titi yaci hankali kwance lallai wannan yarinya ta masa babban kamu.

Har gida suka kai sultan suna tsayawa omar yace dalla malam fitar min daga mota,zaka nemeni next time sannan zan rama kuma kasan ramuwata me zafi ce cewar sultan.gidansa ya wuce yau bazai biya ta wurin mama ba,yana shiga ya tadda sahar kwance a doguwar kujera tana chat,sallama ya mata ta amsa kuwa tace sannu ta ci gaba da chat dinta,shima ko kallo bata isheshi ba ya wuce room dinsa,wanka yayi sannan ya dauko take away da ya zo dashi ya dauko yaci a kyankyame sannan yayi sallar la'asar,karatun Quran yayi da sauran abubuwan lada har magriba tayi ya wuce masallaci,inda ya bar sahar haka ya dawo ya sameta ba sallah,har ya gaji da fadan.

Dakin haj rahina sadiya ce da naja ke hirar samari suna bawa umma labarin yanda suke cin kudinsu,Aisha tace ai ni full tank nake ja,zuka nake da yawa,jane dani,sai na cika tanki na.tana tsakiyarsu suna ta hirarsu,daga nan suka mike sukayi mangaren maman omar,su uku ne suka je kamar abin kirki, yan matan ne yau cewar mama,tsaki sadiya ta ja ta mata kallon baki isa,suma sauran haka sukayi,can naja tace an wani faffake gida matsafa kawai.wlh sai mun kawo karshen makirci cewar sadiya,abdallah ne ya mike ya cakumo naja suka fara kokawa tukuri,suna ganin ya fara naushin naja,suka hadar masa abinka da namiji yana karami amma da kyar suka sha a hannunsa.part din suka bari Aisha tace sai kayi dana sani yaro.

Mama kuwa danta ta janye tayi shigewar daki dan inda sabo ta saba,Sam bata damua.haka tasa suleim da abdallah gaba ta kira driver dinta ya tafi dasu shopping har mama,suna fita omar na zuwa gidan,yaga part din kulle dama shima yana da spare key din part din mama,room dinsa ya shige a ciki yayi sallar isha,coffee ya hada ya sha yabi lafiyar gado ya kwanta abinsa.

Tunanin iklas ya addabi zuciyarsa,to shi mene hadinsa da ita har zan na tunata cewar omar a ransa,lallai ya kamata yasan tarihin yarinyar nan,gashi ya rasa dalilin da yasa ya damu ya sake ganin kyakyawar fuskarta, sunanta ya fada a fili GOMNATI.Da kyar ya samu bacci ya daukeshi.

Mama batasan a gidan ya kwana ba gani tayi ya sauko daga part dinsa cikin shirinsa na office sanye yake da wani cufta me tsadar gaske brown sai kyalli yake da kamshi,mama ce ta bude baki tana kallonsa babana dama nan ka kwana,ina kabar iyalinka anya babana karfa ka shiga hakkin matarka,murmushi yayi hade da rungume ta,haba mama dutyn dare takeyi fa,ni sai muyi 3days ma ban sata idona ba,ta fifita aikinta kan aure,nayi fadan da nasiha amma mama a banza Bata San cina da Shana ba,bata San matsala ta ba,batasan komai nawa ba bata damu dani ba,

Zama yayi ya kwanta jikin mama yace mama kin San ba sonta nakeyi ba ko daya,baffa na yiwa biyayya,amma duk da haka nayi kokarin janta jikina ta dole dan na takurawa zuciata kan dole sai na sota,amma mama ita Sam kullum bakin ciki take tura min taya zuciata zata sota,baffa ya jona min bacin rai kullum tana bata min,bazan boye miki ba mama duk da nasan kin San komai akan abubuwan da sahar keyi wlh na tsaneta,bana sonta,bana kaunar na bude ido na ganta a matsayin matata a gidana,amma ina daurewa muna zama dan nayiwa baffa biyayya.
Chapter 5 · 0% Book details