← Book details Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 57

Sashe 18

Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamshin omar da suka ji shi ya basu tabbacin fitowarsa wani danyen yadi ne sanye jikinsa light blue,har kasa ya gaida ummi,umaru wannan kwalliya haka kamar me zuwa zance?amshe zancen iklas tayi haba ummi ke ba dama mutum yayi kwalliya sai kice zance zai je to shi ya omar wa yake da ita,ina yake fita Da har zaiyi wata budurwa, to uwar shishigi ki bari umaru ya bani amsata mana,

Murmushi omar ya saki ummi bikon matata zanje,tayi yaji sabo da rashin ganina da batayi.sallallami ummi ta fara yanzu umaru kana da mata amma baka fada min ba,ayi hakuri ummi,yanzu ma so nake iklas ta rakani can.dole kaje ai baka kyauta ba umaru.

Da karfi iklas tace bazanje ba kaje kai kadai ina ruwana da wata matarka,ni nasa ka aureta,zamana takeyi,kai ta shafa can kaje da wata badai ni ba.cike da masifa ta mike zata shige daki,omar kuwa daria kawai yakeyi kadan kadan wannan masifa ta iklas da takeyi,riko hannunta yayi tunda bazaki ba suhaila jeki shirya ki rakani,

Tana zaune suhaila ta fito sanye cikin English wears Riga da wando masu kyau,ummi ta gyara mata gashinta,wuce iklas tazo yi iklas kuwa kafa tasa wa suhaila ta shatile kafarta ta fadi kasa,kuka ta fashe dashi me karfin gaske,rufe iklas da masifa ummi tayi.

Omar da ummi ne suka lallasheta da kyar,gani tayi da gaske tafiya zasuyi,fuuuu tazo ta wuce su tare da bangaje omar,mota ta gani rantsatsiya a waje, omar na danna remote ya bude iklas ta balle murfin gaban motar ta shige,

Shi kuwa omar murna yayi a ransa dama haka yakeso,a baya ya zaunar da suhaila shima ya shiga.yasan idan ba iklas tafiyar baza ta yiwu ba saboda definitely ciwonsa zai tashi,amma idan iklas na kusa ya riketa sai ya warke

Tafiya sukeyi sun fara shiga abuja city iklas kawai kumburi takeyi kamar zata ce wayyo na shiga uku na lalace

Tunda suka fara tafiya omar ciwonsa ya fara tashi kawai zufa yakeyi ya rasa inda zai sa kansa, ba shiri ya sadada hannunsa ya riko hannun iklas,da karfi cike da masifa ta fisge hannunta,naga Wanda zaka rike ai yau.

Omar ta kansa yakeyi kawai shi yasan me yake ji,suhaila ce dake bayan mota ta mikowa omar hannu gashi ya omar ni ka rike nawa hannun ka kyale na anty.iklas juyawa tayi a fusace ta zubawa suhaila rankwashi ta make hannun wai ni sa'arki ce,ina ruwanki da shi,ba a son hannun naki to.

Omar na nishi da kyar yake tukin motar kallon iklas yayi idonsa yayi jajir,ki daina dukanta ke iskancin da kikeyi a garin nan wa ke dukanki,kunya iklas taji tace to a kyale maganar kana fama da kanka,hannunta ta miko masa ungo gashi ka rike na taimakamaka.yatsunsu ya sarkafe wuri daya yaci gaba da driving,5mnt omar ya dawo garau dashi,yayinda iklas da shi suka shiga wani hali na shauki kowannensu ji yake jininsa na masa wani yammmm.....yammmm.

Wani katafaren barbing saloon Wanda yake hade maza da mata omar ya parker,mata maza birjik ciki ana gyaran gashi,matan manya da yaran manya,da manyan masu kudi sune a cikinsa,turawa ne masu aiki a ciki.gurin ya hadu kamar a turai,

Fitowa yayi sakale da hannun iklas kamar chewgum,tafiya sukeyi cike da izza,iklas ta raina kanta kyaune kadai ya ceceta,dan duk tafi matan ciki kyau nesa ba kusa ba,sai kallonsu akeyi,suhaila na kusa da ya omar.bangaren mata ya fara kaisu yana zaune,iklas ta karbe daya hannun ta mika masa daya hannun gashi rike wannan dayan ya samu ya huta.

Kujera aka ba omar yana zaune gaban iklas hannunsa rike da nata haka akayi mata gyaran gashi aka gama,suhaila ma an mata,sunyi matukar yin kyau,su Kansu masu saloon din sunyi jinjina.

Wurin maza suka koma wannan karan iklas aka bawa kujera ta zauna gaban omar rike da hannunsa,masifu kawai take ji a jikinta na kamar sha'awa amma ta rasa gane mene take ji.

Omar kuwa a cikin jininsa yake jin bala'in sha'awar iklas wacce bai taba ji ba,amma haka ya daure ya cije.tunda aka fara gyarawa Omar suma iklas ta fara turbine fuska,idan ta kalli Omar sai ta tabe baki,wlh ka cuci kanka ko kyau bakayi ba,minti daya ko biyu zata kalleshi tace ko kyau,wai dole za a je bikon mata.

Gajia Omar yayi yace tunda sahar na son kalarsa ai alhmdlh dama dan ita nayi.mutumin da ba a sonsa anyi yaji an barshi wooooooo....cewar iklas,duk rashin fara'ar Omar iklas daria take sashi.

Haj rahina ce gaban baffan su omar,pls baffan yara 1million nake rokonka ka bani zan canja motata.hajia rigimarki ta isheni duk motocin gidan nan,omar fa baya bari motoci su shekara yake kawo sabbi,jin baffa ya ambaci omar yasa ummansu sadiya daure fuska,kaga alhaji ni ba zancen tambadadde nazo kamin ba,dan iskan yaro Wanda tsabar bin matane yasa ya bar gida.wa ya sani ma ko a waje tayo cikinsa....bata rufe baki ba taji saukar lafiyayyun mari har uku...kunci ta dafe tare da tsagewa da kuka tana kururuwa ta cukume baffa da kokawa tare da danna masa ashar,ai kuwa baffa ya sa kafa ya harbata gefensa,ta bigi center table,

Takadda ya dauko ya rubuta mata saki daya,tare da dafe kansa da kyar ya karasa dakinsa.faduwa yayi kasa yayi sharab...mama wacce abin ya faru kan idonta da kuka ta dago baffa,sannan ta kira maza masu aiki da driver suka kwashi baffa zuwa hospital.

Gaskia kowa ya ga yanda omar ya hadu sai ya kyasa,mata sai kallonsa sukeyi,da yawa suna so su kawo kokon bararsu na love amma yanda suka ganshi kankame da hannun iklas yasa suka ja baya, sai kallo daga nesa,

Take away ya musu na abinci kala kala sannan ya kamo hanyar gida,dadi ne ya kama iklas sosai ganin baza a je bikon sahar ba.

Sabo da murna sai labari takewa Omar,suna isa gida iklas ta hango saleem, da Sauri ta bude mota zata fita,Omar yaga saleem sarai,rigar iklas ya rike gam, kallonsa tayi yace muje gida waccen dan iskan zaki je wajensa ko?

Naji ai na fasa zuwa,to sakeni muje gida mana,kayan suka shigar gida,a cikin motar omar ya bar key din iklas na kusa dashi ta kwace hannunta taje wajen saleem da gudu ta karasa, har sun fara hira akan business da aikin gomnati yanda ake cuwa cuwa kudi na shigowa, wajensu Omar ya taka yaje cike da takama ya zubawa iklas rankwashi muje gida,cike da shagwaba tace ya omar da zafi fa,gani yayi zata bata masa lokaci kawai ya sunkuceta ya sabata a kafada. mutanen layin sai daria sukeyi GOMNATI ta hadu da dai dai ita.

Asmabaffa
[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

50-55

By
AsmaBaffa

Daukan da Omar ya mata bai direta ko ina ba sai daya kaita har Palo sannan ya jefata a kujera da karfi tare da shigewa room dinsa,
Sosai Iklas taji zafi yar kara ta saki ohhh tare da dafe hips dinta..ko juyowa baiyi ba bare ya San me take ciki.
Lokacin da su Omar sukaje saloon daya daga cikin yaran Maman Omar tare da wani abokin Omar tabbas suma sunga Omar sun fito daga saloon hannunsa rike da na wata kyakyawar budurwa.

Lallai sunyi mamakin Omar ashe tafiyarsa yayi yana sheke ayarsa da mata,amma ake ta nemansa ana cewa ya bata.
Abokin Omar wato Raj ya daukin alkawarin zuwa ya fadawa Maman Omar cewar sunga Omar a saloon da mace.

Haj.Rahina ta dauki akwati da sauran abubuwan amfaninta kadan tare da Tara yaranta tayi musu hudubar banza sannan ta bar gidan ta koma gidan babban yayansu da ke zaune a garin Abuja shima.
Tasha fada wurin yayanta saboda yayanta Alhaji Magaji mutumin kirki ne sosai ya nunawa Rahina kuskurenta amma Sam ko a jikinta sai ma kara kaimi da tayi wurin son daukan fansa,kuma ta sa a ranta dole sai ta koma gidan Alhaji Mohd.

Tunda su Maman Omar suka dauki Alhj Mohd wato Baffa suka yi hospital dashi gado aka basu bayan aune aune da bincike ya tabbatar yana dauke da ciwon hawan jini kuma ya masa babban kamu,sosai ake kula dashi a hospital Mama ta tsaya tsayin daka wajen mijinta,ita ke jinyar sa,su sadiya ma suna zuwa dubiya amma kullum idan sunje sai sunci mutuncin Mama tare da habaici da zage zage.
Mama na mamakin wai ga mahaifinka a gadon asibiti rai a hannun Allah amma su sadiya suna shirme Allah kyauta.

Sultan ma kullum yana kan hanyar dubiya,kuma shi ke kula da Baffa kasancewarsa likita babba,abokan su Omar ma kungiya kungiya suke zuwa dubiya,kamar yau ma Raj yazo yana dakin da aka kwantar da Baffa tare da wannan yaron me yiwa Maman Omar hidima duk wani aike me nisa da wasu abubuwan wannan yaron wato Nura shi ke wa Mama kusan same age suke da Omar.kuma Nura yana da dangantaka tsakaninsu da Raj.gasu frnds ne shi da Raj,shi yasa suke yawan fita tare duk da cewa Raj me kudi ne,

Raj suna zaune kusa da Mama suna hira sama sama yayin da Sultan ke gyarawa Baffa kwanciya,Raj ya kalli Mama hade da gyaran murya Mama akwai wata magana da nake son fada miki,wato yau kwana uku kenan abin na damuna,gaba daya dakin Raj aka zubawa ido har Baffa da ya samu sauki shima ba a barshi a baya ba,
Naje kusa da saloon in da Nura mun karbi sako a hannun wani Mama wlh munga Omar ido da ido ga Nura nan ki tambayeshi kiji,har kokonto mukayi sai da muka karasa har kusa dashi amma kafin mu is a wajensa sun shiga mota sunyi mana nisa,kuma Mama abin mamaki Omar da mace budurwa zankadediya muka ganshi rike da hannunta da wata yarinya zasuyi same age da suleim dinki,
Chapter 18 · 0% Book details