← Book details Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 57

Sashe 51

Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khairat tunda Allah yasa tazo gidan tayi tozali da Omar mijin Gomnati taji duk duniya ba Wanda take so da muradi sai shi,dan haka ta like masa ta manne masa,shi kuma ganin yan uwar abin kaunarsa ce Gomnati Iklas sai yake kulata yana karramata,itama Iklas data ga haka bata damu ba tayi tunanin kawai saboda mijinta ne shi yasa take matukar ji da ya Omar,Wanda ita Khairat balarabiyar kasar libiya Sam ba haka bane a ranta tsabar son Omar ne yayi mata yawa,Wanda tana jin baza ta iya rayuwa ba sai da shi,dole sai dai itama ya aureta tunda musulunci ya bada damar auren mata har hudu,
Shi yasa take Neman hanyar da Omar zai fada tarkon sonta, ita tasan Iklas din Omar ta fita kyau amma dole ne ta sameshi ya aureta.

Shi yasa khairat Sam bata zama a bangaren da Baffa ya basu kullum tana wajen Iklas saboda taga Omar kullum yana manne da matarsa,shi yasa take nacewa kusa da Iklas,Khairat taga Iklas yarinya ce shi yasa take so tayi mata wayo ta kwace mijin,dan burinta ta dauke Omar su koma kasarsu da zama,Khairat shekarunta 28 dan haka ta girmewa Iklas wacce kwanan nan ta cika 17yrs kwata kwata.

Shi fa Omar Khairat ta fara damunsa tana shiga rayuwarsa shi da Iklas, ba dama su kebe waje daya sai tazo ta takura musu,dan dai kawai dangin Gomnati ne da tuni yaci uwarta an wuce wajen,
Amma dannewa kawai yakeyi yana biye mata ganin Iklas bata Nuna damuwarta ba,

Idan sauran bakin sunce time yayi ya kamata su koma kasarsu fafur Khairat ke hanasu wai a bari suga yar uwarsu ta sauka lafiya wato Iklas,Ummi da Mama sun gano take taken Khairat.
Omar yaje gidan Sadiya da Aisha ba tare da ya Sanar da kowa ba,ya musu Sulhu sosai da nasiha sosai sun samu yanci mazan nasu sun fara canjawa inda suma su Sadiya suka kara jajircewa wajen kula da miji,har makaranta ta koyon girki da dabarun zaman aure suka shiga. Har sauran kannansu sun biya musu sun shiga kuma suna ta kula da tarbiyar sauran kannensu tare da yiwa Ummansu Nasiha kuma ta dauka.
Har wajen Baffa suka je gaba dayansu har Umma Rahina suka bashi hakuri kan abubuwan da suka shuka.

Haka Maman Omar ma sun bata hakuri Aisha ta haifi yarta mace me suna Mufida, Sadiya kuwa anayin Hutu tazo ta dauki Suleim da Suhaila Suna gidanta suna jin dadinsu dan Alhaji balarabe kashe musu kudi yakeyi yana shagwaba su.

Mijin Aisha ma Nasihar iyaye data Omar sun jawo ya nutsu ya canja hali,sai kiba da kyau da su Sadiya suka karayi. Kullum sai sun Sawa Omar albarka, har Baffa da Umma Rahina suka fadawa abinda Omar yayi musu,haka Mama har Godiya suka Mata.

Iklas ta shiga damuwa akan Khairat tana shigewa mijinta tayi hakuri tayi kawaici ta gaji haka.musamman da taga Omar na biye mata,shima Omar Haushin Iklas yakeji yaga kamar ta daina sonsa bata kishinsa,tana ganin yanda Khairat ke manne masa amma bata nuna komai,shi kuma kara yake mata kawai,baya ga haka da tuni ya kwadawa Khairat maruka yanda take zama tana goga masa kafardarta a tasa, tana taba jikinsa ko ta rike hannunsa in tana masa magana.ga shi kullum shigar banza takeyi a gidan ko kunyar su Baffa bata ji.
Kamar kullum yau Omar da Iklas suna zaune a palon Mama sun baje suna cin abinci Khairat ta fito taci kwalliya ta matse cikin Riga yar fingila da wando sai kamshi takeyi, wajen Omar ta nufa tare da zama kusa dashi tana gugan jikinsa, ran Gomnati yayi mummunan baci

Kishi ya tashi dama ta gaji da halin Khairat,Iklas wani azababben kishine ke azalzalarta kwakwalwarta ta dau zafi, zuciyarta tafasa kawai takeyi,Omar ya ga halin da Iklas ta shiga amma yace me yasa tun farko bata dakatar da abinba.
Iklas tana so taga Omar ya matsa amma taga cin abincinsa ma kawai yakeyi. Iklas a ranta tace kut inama ina da lafiya da billahillazi sai nayiwa matar nan abinda ko a mafarki baza tayi sha'awar zuwa Nigeria ba,amma zanyi maganinta, maganin shege sai dan banza.
Gani tayi Khairat ta zuba lemo a glass cup za ta kai bakin Omar,cikin Zafin Nama Iklas tasa hannu ta fisge cup din tare da watsawa Khairat lemon a fuska, ta mike tsaye tare da nunata da yatsa a tsawace tace get out before I scatter your skull into peaces, dama ga su da tsoro Da Sauri Khairat ta fice,Omar zaiyi magana Iklas ta daga masa hannu ya Isheka ya Ishe.....bata karasa ba mararta ta mirde,ta kulle tare da zamgewa da cakudewa. Rawa jikinta ya fara Kar kar kar....... Gumi ne kawai yake keto mata,wani azababben ciwo taji Wanda ko a labari,,films,da mafarki bata taba sani ba,mararta ta dafe ta daddage iya karfinta cikin siriyar Muryarta ta tsandara Ihun daya fito dasu Mama da Ummi daga kitchen a guje.
Sulalewa kasa tayi tana kuka wayyo Allah na Ku taimaka min,a kaini asibiti na mutu acan,tuni Omar yana kanta shima hawaye yazo masa yana tunanin idan ya rasa Iklas tasa ta kare.

Iklas ta rike Omar kam yana kiyi addua pls yanzu za a tafi asibiti,tana kuka ta fara La'ila ha illalla la'ilaha ilallah taana rerawa ita kadai yanda zakuru sukeyi kawai kirjinne da bata duka,tuni su Ummi sunyi waje kiran driver,Mama na hada kayan haihuwa,
Suna cikin mota tana cinyar Omar kwance su Mama a gefe,Ummi tace dan Allah Iklas ki rufemana baki haka akanki aka fara haihuwa,Omar shafawa Gomnati marar yakeyi yana lallashi tare da tofa mata addua.

Ciwon ne ya lafa mata suna mota driver na tsala gudu, mikewa zaune Iklas tayi tana goge gumi tana wash naji salama,suna shiga asibitin ciwon ya dawo yafi na da,cije baki Iklas tayi tana Bala'i.....Bala'i....gashi......nan.....Omar sai hawaye yakeyi yanda Iklas ta haukace gaba daya gashin kanta kamar daga bakin kura ya fito,yanzu bata ma San me take cewa ba,kuka takeyi tana nishi tana Ku miko min danwake na kwandala,abani ko dan malelene,haka aka turata a gadon asibiti har dakin da aka kwantar da ita,patients da malaman asibitin kowa dariya sukeyi da tausayin Iklas yanda take fadan abu barkatai.

Ummi ce ta kalleta tace yar bantan Uba taji wahala, Mama tace sannu yanzu Likita zaizo, Iklas ta Kalli Mama ta fara tooooooo.......yayi sauri yazo yamin Allura ta kwandala. Shi kansa Omar ta bashi dariya dannewa yayi.

Ummi ce tsuguna a jikin gadon ai kuwa Iklas Neman abin rikewa takeyi ta tugewa Ummi dan kwali ta jefar,da Sauri Ummi ta matsa ta dauki abinta tana daurawa tace harda ciremin dankwali?Iklas tana cijewa tace idan....dan kwalin na kwandala ne to a bani......lallai.... Nace a bani.
Nurses da likitoci sunzo sunce Kaine mijinta? Da sauri Iklas tace yana ina bakin mugu azzalimi,ta fashe da wani irin kuka me karya zuciya.Omar hankalinsa ya kara tashi gashi kusa da Iklas hannunta cikin nasa amma take nemansa bata ganeba.

AsmaBaffa

Ku kwashe min da tafi readers.

Tnx all nayi delay ban cika alkawari ba, amin afwa nima ko ta kwandala ce.ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

190-195

By
AsmaBaffa

Ciwon daya taso ne gadan gadan yasa Iklas ta daina kuka sai muzurai da cijewa kawai kuka ya gagara,likitoci sun bazu a kan Iklas yayinda Gomnati ke sambatu karfinta ya kusa karewa a hankali tace doctor kayi min Allurar guba tunda dai haihuwar nan baza ta zo ba,Omar ya rude addua kawai yake tofa mata,
Iklas tace Ku fadawa mijina ya yafemin bazan warke ba,irin wannan ciwon nasan sai dai na tafiya lahira,Omar ne ya rungumeta yana hawaye am sorry wifey insha'allah zaki tashi,kan Omar ta shafa tace kamar Omar dina,nine matata Honey dinki ne,kayiwa Mama biyayya sosai,idan baka bita ba dole kaci wutar jahannama,domin bakusan Haihuwa ba.
Sakinsa tayi,likita yace ya basu waje ga wani sabon ciwon daya taso mata,Ummi tace kiyi fa a Hankali Iklas Maza suna jinki, da karfi tace Maza? Maza basu San Haihuwa ba....wayyo Maza basu San Haihuwa ba.
Likita ne yace su Ummi su fita duka zasuyi Aiki,Omar yace bazai yuwu namiji ya duba masa mata ba,dole suka kawo mace da mata nurses,harda shahararriyar nurse din nan Subby,Maman waleeda ma anyi mata Transfer Hospital din ita ce ta karbi haihuwa da gaggawa,Subby ta Daura drip,Hajiya Jamila,Jamila Sule duk a asibitin suke aiki sai kaiwa da kawowa sukeyi wurin Iklas,

Tun safe ake abu daya Har yamma Iklas bata haihu ba,bakar azaba take sha kawai,Subby tayi gumi sosai,Iklas kuwa da taji shuru sai tace kuji na fada muku bazan Haihu ba kawai kuyi min Allurar guba,Omar ya rasa Inda zai sa kansa,Sallah sai da yayi rafkannuwa da yawa,
Babbar likita King ita ta zo ta kawo wasu dabaru cikin Ikon Allah 5pm kan yaro ya danno kai,Iklass ido yayi jajir yayo waje,ansata nishi ana fush,babu bakin magana ya mutu murus,nishi ake ta sata suna taimakawa,Rabin Rabin jikin Baby yayo waje aka taimaka ya fito du da komai a hannun Subby,
Zukeken Namiji ta santalo me kama da Ubansa,lafiyayye katon gaske, yaro na fitowa Iklas ta sume, sai da tayi 5mnt ta farfado,nan akayi mata Allurai kala kala,nan danan nurses suka gyara yaro tsab,sannan aka fara yiwa Iklas aikin fito da jinin cikinta tas,tare da gyarata ta Huta sosai sannan Ummi ta shigo ta taimaka mata a bayi tayi wanka sosai ta gasa mata ko ina nan ma Gomnati harda kukan ruwan zafi,kafin su fito room din sai kamshine ke tashi,abinka da private hospital me tsadar gaske kai ka rantse Hotel ne,baza kace a asibiti kake ba,Iklas ita kadai ce a room din ba a hada mutane room daya,kowa da nasa.

An canja bedsheet ma sabo,tana fitowa suka fada toilet ma'aikata suka gyara shima,kamshin dadi ne kawai ke ratsa ko ina,
Iklas ta hana a fadawa Omar ta haihu wai sai ta shirya,a cikin jakar kayan haihuwa harda body lotion da su turare,da man gashi da handdrier,wata nurse da tazo domin sauran sun tafi,tace lallai haihuwar fari ce wannan shiri haka.
Chapter 51 · 0% Book details