← Book details Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 57

Sashe 7

Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uummi ce tace samari lfy kuwa?har kasa ya duka ya kwashi gaisuwa,lfy ummi yaji sunanta wurin suhaila,ummi magana nazo muyi in ba damuwa.to shigo daga ciki cewar ummi,wani kamshin dadine ya bigi omar,kal kal yaga gidan,komai tas a tsare ga kamshi Wanda bai taba ji ba dukkan gidan nayi,Palo ummi ta kaishi mamakin kayan palon yayi,masu dan tsada tsada danshi a wajen omar masu dan tsada zai ce, ga kamshi na gaske komai tsab,ga wata fanka ta kasa me iskar niima,ga ta sama ma.

Numfashi yaja yace ummi dama akan maganar yarinyarku ne me tallan apple,na ganta sai naga sana'ar bata dace da ita ba,kai yaro ko Kaine lailatul qadarin da tace ta gani,me gidan kaji?daria ce ta kwacewa omar ba tare da ya shirya ba,ae ummi nine,Allahu akabar kabira,dan nan ya sunanka? Omar mohd omar Allah sarki umaru,sannu da kokari Allah ya kara budi,ameen ummi,mikewa ummi tayi ta kawo masa zobo me sanyi da dadi,yasha kayan kamshi,da ruwa pure water,shikam kodan su saba da shi zai sha, sosai yaga kalar gidan ba kyankyami,har lumshe ido yakeyi dan dadin zobon,suna zaune kaka ummi sai satar kallonsa take tana jin dadin yanda ya sha abinsu ba tare da ya ji kyankyaminsu,gashi me kudin gaske amma sam bai kyamacesu ba,kaka ummi ce tayi tunani tace kai yaro ko kai dan gidan mohd omar ibrahim ne dattijon kirki,murmushi yayi yace ummi kin sanshi dama?

Ae ai muna jinsa a radio muna ganinsa a labarai,waye bai sanshi ba,ai ya zaga duk fadin nigertia,nan kaka ummi ta karkace ta bawa omar tarihinsu kaf,har halayen iklas da yanda iklas ke tunaninsa sabo da tayi masa rashin kunya tana son bashi hakuri.

Shuru yayi yana sauraren maganganun kaka ummi,ya tausaya musu matuka gaya,ya sa a zuciarsa zai dinga taimaka musu dan ba karamin tausayinsu yaji ba,can ummi tace ai mutuniyarka na bamu labarinka,yanzu zaka ga ta shigo,ko 5mnt ummi batayi da rufe baki ba iklas ta shigo da sallama tana kwalawa kaka kira?kaji ta ko umaru cewar kaka,shi kam omar guntun murmushi yayi,yagafa kaka ummi akwai surutu,shi kuma ba ma'abocin son surutu bane,fuskarsa tamke take dama ba wata fara'ace da shi ba,sai ka Dade dashi baka ga dariarsa ba,kaka ummi ma ta gano hakan,ga izza da takama.

Ummi ina suhaila wai tana daki tayi bacci,yau nace baza taje islamiyya ba ta kwanta ta huta,haba ummi so kike naje nasha rana a titi ga kunya da tozarci ruwan sama,iska,sanyi,rana su kare min akai,kema kina naki wahalar mun biya kudin schl din nan duk da ba me tsada bace amma kin San asarar kudin zamuyi ko,alhmdllh ni na samu dai dai gwargwado na addini,amma ummi suhaila fa kin San yarinyace,ni gaskia bazan bari ta taso a jahilci ba.sabo da schl fa nake talla a titi.dole taje schl wlh,bari na shiryata ummi zauna Palo ki dauko min Biro da jotter lissafi za muyi,

Ke dalla rufemin baki ni cewar ummi tare da shigewa Palo wajen omar dake zaune,duk yaji hirarsu da iklas gaskia ta birgeshi,tasan me takeyi.

Asmabaffa
[17/03, 21:45] Hadiza Sani Fbk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

8

By
Asmabaffa

In hakane to iklas na da nutsuwa da hankali,yarinya karama,ummi ce ta katse masa tunani sannu umaru kaga shashashar can bata ma kula da bako ba ita kawai ta makaranta takeyi,yarinyar nan da jarabar son makaranta take,rai ba hutu,ummi ai yanzu ilmi shine gaba,Allah kyauta cewar omar,iklas ta yiwa suhaila wanka,ta shiryata a uniform din islamiyyarsu Wanda shi kanshi wandon ya yage ta gwiwa kayan sun tsufa tukuf,amma a wanke a goge kal,sam iklas bata kula da takalmin bako ba,kawai abinda ke ranta take tunani,har Palo taja hannun suhaila wani mahaukacin kamshi ne ya daketa,kallon palon tayi,da sauri ta zabura tana zare ido,ta zata a mafarki ne sai taga tabbas a gaske ne,idonta ta kara murzawa,

Dan rusunawa tayi kasa sannu ina yini,lfy kawai yace yana shan kamshi,tunda taga bata samu tarba me kyau ba ta mike,ta dauki Biro da jotter tace pls tsohuwa yi sauri muyi lissafin nan ina da aikinyi,iklas ke naga dan ana ce miki gomnati kanki rawa yakeyi ke a dole jinki kike kamar wata ma'aikaciyar gomnati,wlh ki cire wannan haukan ko kunya bakyaji kin fara girma kina cin kasa,baki ta cuno haba ummi dan Allah ni ki daina cewa na girma,dan uwaki ke bakya gani makauniyace jibi fa kirjinki iklas,wata kunya ce ta rufe iklas a gaban omar,kun San tsofaffi akwai baro zance,shi kuwa omar murmushi yayi ya kara wani nutsewa hade da tabe baki,a ransa yace wai wannan ce ta girma,ina abin yake,breast kamar gudan lemon tsami.

Kasa kallon inda yake tayi sabo da kunya,da kyar ta fara rubuce rubucenta,tana ta faman buga lissafi a paper,kudin ta ebo tana turo baki gashi nan ummi wannan kin San ranar Saturday zanje kasuwa dasu,ungo wannan ki hada Dana wajenki na cefanen gida na fada miki ummi kullum ko naman 100 a dinga girki dashi ko kifi idan bani zan dafa ba dole ki dinga dafawa dashi,bana son muna cin garau garau ina shan wahala a rana a banza,blood dina zai kare a banza,kuma ban son skin din suhailata ya lalace ko babyna ta kalli suhaila,murmushi suhaila tayi tace anty ranar Monday za muyi debate a schl fa,kuma ance mu fadawa mom and dad Wanda sukaci akwai gift,muje da masu karba mana,ok suhaila Allah kaimu zanje ai cewar iklas.

Ummi kuwa tabe baki tayi kwaji dashi can,daria suhaila tayi,iklas kuwa cewa tayi ummi yau daga islamiyya zan wuce siyowa,a'a iklas wlh baza ki wani gidan kaji da magribaba,ban yarda ba duniya ta lalace.mutane ba tsoron allah ne dasu,suje su lalata minke,a jawo mana masifa,dan yanzu da kike ganinki karama sai samu matsala.ba musu tace to ummi nifa tunda na dan Tara na abinci zanyi hutun 1wk bazanje tallaba.

Ina ruwana da in na ce ki huta ai kin yarda kikeyi Yanzu gashi ai kin bi shawarata.kwantawa tayi jikin ummi tsohuwa zaki ci girki me dadi na zamani har na 1wk.daria ummi tayi oh ni jikar luba ta kaiwa iklas rankwashi.

Omar kuwa birgeshi sukeyi,baren ma acting iklas tana abu kamar namiji magidanci,ga iya planning rayuwa,kai Wanda ya aureta yaji dadi,ga yanda take kula da kanwarta.ummi ce ta katse masa tunani da umaru kayi shuru,ba komai ummi ni zan tafi sai wataran,to har zaka tafi mun gode Allah saka da alkhairi,mun gode kwarai da kulawarka,hannun suhaila ya rike zo ki rakani beautyn anty.dadi suhaila taji dan gayu yace mata beautyn anty.

Har mota sukaje da suhaila kudi ya dauko bundle guda na dubu dubu yace gashi beauty ki bawa ummi kice suyi cefane,ya kara dauko wasu manyan kwalayen sweets masu dadi da tsada da biscuits yan gaske da wasu snacks cikin katuwar Leda gashi wannan duka nakine,har kasa tace tnx uncle tana ta murna,wata ledar ya kara daukowa katuwa wannan suhaila baza ta iya dagawa ba,yace jeki ki kai wa ummi kisha sweets dinki,sannan ki cewar antynki tayi sauri ina kiranta,kafin ya rufe baki ta fada gidan da gudu,ummi murna da dadi ya rufeta,kakarsu ta yanke saka,tsalle sukeyi da murna kaka harda rawa da juyi,Riga damammiya pink bodyhug ce jikin iklas da wani jean skert shima da kadan ya haura gwiwa,

Kallonta yayi ya tabe baki,mika mata kayan yayi gashi nan kuyi manage kafin na dawo,godiya ta shiga jerowa,juyowa yayi cikin hade rai da kakkausar muryar dake firgitata karki sake na ganki kan titi kina talla wlh,sannan ki daina yawo tsirara ga kaya nan,daure fuska tayi har zatayi magana sai kuma taji tsoro gani tayi yayi mata kwarjini.

Amma aranta tace kuji min iyayi da shishigi,ina ruwansa da tallana,uba nane shi,shi zai dauki nauyinmu in banje talla ba,wai ina yawo tsirara kut..yayi sa'a shi ya fada min haka ina ganin mutuncinsa da wanine wlh sai ya San wace gomnati.

Kafin ta gama wannan zancen zucin nata tuni omar ya Dade da figar motarsa ya bar layin, bayan motar ta hango kadan.gida ta wuce itama,

Nan fa murna sabuwa gidan su iklas, ready made dogayen riguna ne masu tsada da kyau dai dai iklass kamar an aunata kala biyar,Riga da skert kala uku readymade suma,takalma kala uku flat,da yan gyale,brst basu isa sa bra ba panties kawai ya siyo kala 10,vest da tight wando guda uku,rigar bacci na yaran gida kala uku,bai San iklas Nada kanwa ba shi yasa bai siyo da ita ba,sai ya bata sweets da snacks din,atampofi kala biyar masu tsada du iklas tace kaka ummi ta dinka nata ne.

Murna wurin kaka ummi ba a magana ita kuwa suhaila ta sweets kawai takeyi,omar Kuwa wurin sultan ya tafi gaisar da mom din sultan,sannan suka je wajen wasu frnds nasu,sultan yayi yayi omar ya rakashi wurin Yasmin budurwarsa amma omar Sam yaki zuwa,sultan ne yaja tsaki wlh zan rama omar,Yasmin din da zan aurace baza kaje wajenta ba?shuru omar baice uffan ba,sau daya fa ka ganta Frnd shima a hospital office dina kuka hadu.malam karka dameni kafi kowa sanin waye omar bana zuwa rakon zance,so pls excuse me cewar omar,nasan halinka mana maramutunci,miskilanci,da rashin damuwa da matsalar wani sai in matsalar ta me tallan egg ce.headphone omar yasa a kunnensa yana jin wakar Chris brown.

Kallonsa sultan yayi dan iska tashi ka tafi gidanku ka bar min daki ba abinda ka iya bakin hali ba annuri a fuska,gaka da mata amma baka da maraba da gwauro,gwauron banza kawai.murmushi omar yayi ya mike tare da shigewa toilet din sultan wanka ya fesa,wani closet din sultan ya duba da yake ajiye sababbin singlet dasu boxers,3quater dan bangaren new da ba a taba sawa ba daban suke,sultan ma kwai kyau tsabta da daukan wanka,sultan shi ba fari bane chocolate ne,ya danfi omar kiba da kadan,shi yasa size dinsu kusan daya,

Farar singlet omar yasa da 3quater ya fesa turaruka,sultan na shan kallonsa,kayan jikinsa daya cire ya eba ya zuba a mota,ya dawo room din sultan karar ruwa yaji yasan sultan na toilet,wajen mom din sultan ya wuce yaci abinci suna ta hira a kayataccen kantamemen palonta kamar aljanar dunia,30mnt yawa mom sai da safe ya wuce room din sultan,sultan ya hango jikin mirror ya hade cikin wata arniyar gezna sai turaruka yake fesawa,
Chapter 7 · 0% Book details