← Book details Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 57

Sashe 47

Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunayin Sallar azahar Iklas ta koma dakin Mama time din Omar bai dawo daga masallaciba,Mama na ganinta tace wlh fitar min daga daki yanzu zaku zo Ku addabeni,kai Mama bacci fa nazo yi,Ummi ce ta koro ni,zo ki kwanta to ni dama makwafta zan shiga barka yanzu zan dawo,Mama tayi waje tana saka hijab dinta,
Omar na dawowa dakin Mama ya nufa,Iklas ya gani har tayi nisa a bacci,hawa gadon yayi tare da buga jikin bed firgit ta tashi idonta cike da bacci a shagwabe tace ka dauki hakkina gaskia,bafa zakiyi bacci ba nima haka kike zuwa kina min,mika Iklas tayi me Jan hankali da dare fa baka bari muyi bacci ka barni nayi yanzu dan Allah,
Ni kin manta har ruwa kike zubamin dan kawai kar nayi bacci.murmushi tayi ta wulkita kafafunta ta daurasu gadon bayan Omar,kai bayanka zaiyi dadin duka,cikin sigar wasa a hankali ta dinga yin chanese da bayan Omar da kafafunta,Omar sai kallonta yakeyi kamar ya cinyeta,tana birgeshi akwai son wasan tsiya wajen Iklas kamar yarinya yar 5yrs.

Kafafunta ya hade waje daya ya dagesu ya matsa su da karfi saida ta saki Kara tana bashi hakuri,dankwalin Mama ya dauko ya daure kafafun Iklas tam,
Ya jata jikinsa fitinanniya muyi baccin to gobe zakije schl, yau kuma da dare kin San ba bacci dai.
Murmushi Iklas tayi yawwa honey irin na jiya za muyi style din kwai sweet,daria sosai Omar yayi yace to karfa ki Tara min mutanen unguwa da ihunki,haba wa ya isa ya toshemin baki dole in sakata in wala wlh harda kukan sweet idan ta kama.Omar ya Riga Iklas bacci lallabawa tayi ta dauki gyalenta ta daure kafafun Omar,dankwalin kanta na atamfa ta cire ta kara daure masa hannaye ta koma jikinsa ta makale sai bacci.
4:30 Mama ta dawo ganinsu tayi suna ta bacci kowanne kafa daure da dankwali,shi Omar harda hannu ma.

Dariya suka bawa Mama tana lallai yaran nan naga Alama ciwon hauka ya shigesu,sallah tayi ta wuce kitchen domin shirya abincin dare still su Omar baccinsu sukeyi.
Ummi ce dake taya Mama girki tace bari na yaran nan suje suyi Sallah su leka wajen Haj Rahina su gaisheta. Yayi kyau hakan cewar Mama.

AsmaBaffa

Godiya gareku masu comment. Allah saka muku da alkhairi,ina jin dadi.ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

170-175

By
AsmaBaffa.

Tashinsu Ummi ta shiga da niyyar yi amma sai ta saki baki tana kalonsu kowanne daure da dankwali,toilet din Mama ta shiga ta ebo ruwa kadan ta watsa musu da sauri suka bude ido,sai yanzu suka tuno a gidan Baffa suke fa
Ku je kuyi sallah fetsararru ku shiga sashen Umma Rahina ku gaisheta tana fadin haka tayi waje,Omar kallon hannunsa da kafafunsa yayi yasan aikin Iklas ne ,murmushi ya watsa mata sai ki kwance ni yarinya, hannun daya daura ya kwance,wai yaushe ma kika daureni ban sani ba,murmushin dake kara mata kyau saki masa kana ta bacci ta fada tana kwance masa sannan itama ta kwance nata kafar,

Sallah sukayi sannan suka nufi sashen Haj Rahina,dukkansu yan matan Umma suna palonta har Sadiya da Aisha sunzo gaida Ummansu,Iklas sai da ta kara cin Uban kwalliya me kyau,ta kashe dauri tare da kara fesa turaruka,hannunsu sakale da juna sukayi Sallama palon Umma,yuuuuuuu suka zuba musu Ido,Najja ce ta maka uban tsaki tare da Hararar Iklas da Omar,
Suma kannensu su biyu su Amina harara suke kawai aikowa da Iklas,Sadiya da Aisha sun Lula tunanin duniya,a ladafce suka gaishe da Umma ta amsa kadaram kadaham,ba yabo ba fallasa,duk sauran kannen Sadiya iya Omar suka gaisar,Iklas tana kallonsu bata kulasu ba itama,

Kallon Amina Iklas tayi tace yan mata an girma sai aure,haka kika kara girma,kallonta ta mayar kan Sadiya da ta yamushe a gefe daya,tace a'a Ashe kina nan ya kk,ga Maman yan biyu ma,gaskia Aisha kinyi saurin samun ciki,daga kaiki sai ciki.duk wannan maganar da Iklas ke musu Amina karama ta girmi Iklas bare su Sadiya,

Gaba daya su Sadiya ganin yanda Iklas ta kara komawa,ta mirje ta kara yar kiba,ga kyau komai yaji duk sai suka raina kansu,musamman irin tsadajjiyar atamfar dake Jikin Iklas,sai kallon Takalmanta sukeyi,
Komai na jikin Iklas unique ne,abin sai ya birge Sadiya da Aisha da suke jin jiki a dakin miji,shi yasa rainin hankalin ma da Iklas tayi musu basu damu ba Sam,sai su Najja yan mata da Amina su suka dauki zafi,ganin sun girmi Iklas amma tana raina musu hankali dan kawai tana auren yayansu,Haj Rahina kuwa sake sake takeyi Aranta gaba daya jikinta ya mutu taga lallai baza ta iya samun Nasara ba,amma zata nemi shawarar kawarta Haj binta.ko da wani taimako da zatayi mata.
Umma sai mamakin rashin kunyar Iklas takeyi a ranta tace yarinyar nan jaraba ce naga Alama tafi karfinmu.
Umma ce tayiwa Najja Signa da Ido kan ta rama abinda Iklas tayi musu,a masifance cike da rashin tarbiya Najja tace Ya Omar kayiwa matarka kashedin fada mana magana anyhow,duk cikinmu ba sa'anta,dan kina matarsa bazaisa ki samu damar raina mu ba,banza a banza yar matsiyata daga zuwa cin arziki an mallake mutum da tsafi,

Aisha ce ta bige bakin Najja dalla rufe mana baki,Iklas tace nafi karfin na tsaya ja inja dake,ta karkace dauri taci gaba baki isa ki kirani yarinya ba,saboda na fiki sanin duniya,yarinya baki San komai ba tunda baki aure ba,Sadiya ce cike da sanyin jiki tace pls a bar zancen ya isa haka kiyi hakuri Iklas ki kyalesu yara ne basu inda duniya tasa gaba ba.daga har Iklas sunyi mamakin Sadiya da Aisha,sun canja kamanni da hali.

Umma harara ta Dallawa Sadiya,Omar mikewa yayi tare da Jan hannun Iklas ransa bace,Najja ce ta biyosu a baya ta sha gaban Iklas tare da narka wata ashar uban me kika sani a aure, ke karamar yar iska ce,
Kallonta Iklas tayi ta dan saki murmushi yarinya kenan,Najja ce ta kara karfin muryarta mene abunda kika sani Wanda ni ban sani ba,me zaki nuna min?
Iklas a nutse take fadanta silent killer ce,nasan tsayinta nasan kaurinta what of u?oh nasan zaki sani tunda ke taki ba Sadaki kika sani dole kinga da banbanc.....shut up a tsawace Omar ya furta,banza yar Tasha me tallan kwai da Apple cewar Najja,maganar ta konawa Iklas rai,wato Omar ya gama bazawa a danginsa ita tayi talla,ga zahiri kowa idan ya tashi yi Mata gori da yar matsiyata yar talla suke Mata, Sahar ma ta fada mata,a ina sukaji har ta saida Apple da Egg tabbas Omar ne zai fada,wani bakin ciki ne ya lullube Iklas,

Bata San sanda ta cakumo Najja ba,Omar ya fara tafiya ya zata Iklas na bayanshi sai yaga wayam, hangosu yayi rukume da juna suna dambe, dama ga Najja garin jiki ne da ita narkekiyace ga tsayi ga kiba,Iklas kamar biri ta dafalfale Najja,Najja ce ta dage ta ciji Iklas a hannun da ta shaketa, fatar hannun Iklas ta dauke sai jini,Iklas ma bata bari an shata a banza ba,Najja ta gartsawa cizo a kunne sai jini Shar ta Kunnen Sadiya,
Samu tayi iya karfinta ta lankwasa yatsan Najja na tsakiya ji kake rukus, da sauri Najja ta durkushe kasa tana wayyo ta ballamin yatsana wayyo Umma na shiga Uku,

Omar da sauri ya karaso wajen bai wani tsaya bata lokaci ba ya fyallawa Iklas wani lafiyayyen mari,cik Iklas ta tsaya dafe da kunci,Najja na ganin haka tayi luf ta daina kuka sai dariar mugunta ma da takewa Iklas a boye,gwalo tadinga yiwa Iklas,Omar kuwa Najja ya kama ya Mikar ta tsaye,yana antaya mata zagi banza shashasha jaka,dabba wuce ki bani waje kafin na kwadeki,Baku da aiki sai jaye jayen fada da gulma,wlh idan Iklas tazo gidan nan kika kara tararta da fada sai na karyaki haka Omar yayiwa Najja tas,

Ido suka hada da Iklas wacce har yanzu tsaye take kamar gunki,suna kallon juna Iklas ma tayiwa Najja gwalo ta rama itama harda itama dariyar duk abinda Najja tayi Mata sai da ta rama,Kafin Omar ya juyo Iklas ta Nutsu bai San me sukeyi ba,
saida Najja tayi nisa ta juyo tacewa Iklas Apple and egg ta shige gida.Omar yayi Dana sanin Marin wifey dinsa da yayi yaga tabbas Najja yar iskace itama,ashe tuggu ta hadawa Iklas dinsa gashi ya jangwalo tsiya,taya zai lallasheta duk da yasan itama wifey din tasa tsokanar tsiya gareta.

Matsawa yayi wajenta fuskarsa ba rahma yace muje ke kuma ai yana magana Iklas ta rushe masa da kuka ji kake Tim ta fadi kasa tana ta birgima da shure shure,wayyo wayyo wayyo zasu kasheni dangi sunyi min taron dangi,dama ba sona yakeyi ba,yafi son danginsa dani,an zalinceni,zai kasheni,miji me dukan mata aka aura min dama, ni gwara na koma titi talla na,baya tausayina wayyo Allah na tun ina yar mitsilata an fara yi min tabo ajiki akan dangin miji.
Tsakaninta da Allah Iklas ke shure shurenta,Mama da Ummi sunji kamar hayaniya da gudu sukayo waje, su Umma ma dasu Sadiya duk sun fito,Iklas suka gani tana shure shure Omar na tsaye gefe guda yana tintsira dariya danshi dariya abin nata ya bashi.

Ummi ce fara magana ke meye haka lfy?kunamace ta harbeki, Umaru mene haka?da Sauri Iklas ta kalli Omar still kuka takeyi,ido Omar ya mintsina mata wai ta rufa masa Asiri.

Tana sheshekarta tace ba...ba...cinnaka bane ya cijeni,kuma Honey ya kwace min wayata,mene kuma honey inji Ummi, wani farin ciki ne ya lullube Omar shikam abin kunyane ace ya mari Iklas da hannunsa,
Kowanne cikinsu tsaki yaja Mama tace naga ranar da zakuyi hankali, Ita Sadiya birgeta sukayi ita yanzu ta isa tayiwa Alhaji Balarabe haka.ai ranar sai dai gawarta,gata tana aiki tana daukan salary amma jin dadi da zaman lafiya ya gagareta,duk sun tashi a banza.
Chapter 47 · 0% Book details