← Book details Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 57

Sashe 8

Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tabe baki omar yayi daga bisani yace malam kayi sauri ina jiranka,da wata uwar masifa sultan ya juyo ubanwa zaije dakai gidan surukai haka,kamar inyamuri,ga suma duba fa shigarka,tsaki omar yaja ya sake bude layin sababbin jallabiya,wata milk color me mugun tsada ya dauko,siririya me shape dai dai jikinsa ta manyan guys,Turare ya kara fesawa sannan suka fito,mom suka gani a Palo suka mata sallama cike da fara'a hade da jindadi gami da birgewar abotarsu ta musu adduar dawowa lfy,7:30pm suka cinna hancin motarsu cikin gidan su Yasmin,gate man ya wangale musu makeken gate din su yasmin,har katafaren palon baki aka musu iso,kafin wani lokaci an cika gabansu da kayan motsa baki,

Karaar takalmi sukaji das das,sannan kamshinta ya iso,cikin nutsuwa ta shigo da sallama,sultan ne ya amsa,ba laifi Yasmin kyakyawace fara ba kal ba amma tafi sultan haske,sun gaisa da omar ya dan jira for 15mnt ya fice ya koma mota,karfe 9pm sultan ya kira omar har umma da abbun su Yasmin suka gaisar.omar ranar gidan su sultan ya kwana.

Asmabaffa
[17/03, 21:45] Hadiza Sani Fbk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

9

By
Asmabaffa

Wannan page din dominku nayi shi readers masu yabo da jinjina.

Da safe tare sukayi break sultan,omar da mom sultan,sannan omar ya wuce office.bayan kwana biyu da zuwan omar gidan su iklas,wasu ma'aikata suka zo da kayan gini a motoci cewar oga omar ya turosu za suyi musu kitchen a canja toilet da sauran wasu abubuwa,abin har kaka ummi ya daure mata kai amma me zasuyi,nan da nan cikin 3days anyi toilet ta zamani tasha tiles,kitchen ma haka,rooms dinsu ma daga baya ya bada umarnin a sake sababbabi,kai readers gidan dungurugum aka sake ginawa komai sabo na zamani,2room da Palo tsakiya,toilet kitchen duk a tsakar gida yanda suke kawai Palo aka kara musu,ansa kofofi da windows na zamani,gidan tiles da tiles dan dagwas dashi gwanin birgewa,sai murna ake tayasu,su kuwa sai suce dan uwansu ne ya Gina musu,Palo sun maida kayansu na da, sai ya tashi haduwa,daya room din kuwa gani sukayi ankawo bed mirror sip new yan gaske aka shirya,duk rooms din an sa musu labile na zamani,next day suka kara ganin mota guda ta kayan abinci a tsorace suka yarda suka shirya kayan a kitchen komai akwai,dama suna da fridge me kyau da girma da tsada,

Har gas da kayan kitchen kamar amarya an kawo an shirya musu,shifa omar kawai kudi yake bayarwa da umarni,next day aka kara kawo wasu kayan a Ledoji wai inji oga,dayar kaji,kifi da naman rago,a fridge suka zuba,harda lemuka masu tsada a takaice readers komai yaji a gidan na jin dadi,

Next day kuwa wasu kayan aka sauke,ai iklas kuka tasa kaka ummi ma haka su dai karfa ace watarana su biya,dadi ya zama wahala,duk Wanda ke musu har anfi 1wk basu ga keyarsa a gidansu ba,sun shiga uku karfa ko ba nasu bane,ko aljanune ma,

Kayan suka bude bayan sun gama kukan,uniform suka gani na wata schl dake kusa dasu schl din me tsadace,iklas dai dai ita,itama suhaila kamar an gwadata,mamaki sukeyi wai to a ina yasan size dinsu,uniform din har kala 4-4 ya musu,ga books din kowa a schl bag kala 3-3,takalman schl ma kala 3-3,a cikin jakar iklas yasa takadda me dauke da rubutunsa,

Da sauri ta dauko ta fara karantawa kamar haka.
ki duba cikin wata Leda akwai envelop in kunje schl din da ita zaku tafi, ki bawa p.c din,7:30 za kuga me kaiku yazo,banda talla a titi,ki gaisar da ummi.
Omar

Ai tsalle suka fara da ihu suka cika gidan,wlh ummi shine yayi mana komai,lailatul Qadari Allah maka albarka,ai duk sallah sai na ma addua cewar iklas,kaka ummi babaLola science sec schl fa ya biya mana kinga receipt har na gama an biya min,suhaila iya js3 ya biya mata,..

Daya ledar suka jawo gaba daya kayan suhaila English wears masu kyan gaske kala 10,takalma masu kyau harda kayan baccinta kala biyu,pant itama dasu vest kala 10.kuma nan ma kamar an gwadata.

Tsalle kawai takeyi tana murna,saura wata ledar atampopi kala biyar dinkakku diff stile,shaddoji kala 4 yan gaske suma sunsha aiki,lace kala 3 sunsha dinkin zamani,da material kala 6,suma gaba daya an dinkasu dai dai jikin iklas,lace2,shadda2 mayafai manya masu tsada kala Biyar, ba a dinka ba takadda manne jikinsu anyi rubutu kamar haka.

Na ummi ne ki bata ta dinka,ga kudin dinki nan cikin lace,mayafaima nata natane.karamar ledar karshe suka bude,hijabaine masu hannu kala biyar size din iklas dagwas,kala uku na suhaila,kala uku manya na ummi,mayafai suka Ciro yan madaidaita masu kyau da tsada kala 6 na iklas,sai uniform din islamiyyarsu da ya gani jikin suhaila ya canja musu new kala 2-2.

Yau har nafila sukayi suka dinga godewa Allah tare da yiwa Omar addua da iyayensa,next day kayan kwalliya iri iri Dana gyaran gashi da turaruka aka kawo musu,3days tsakani ya turo da wasu latest takalman roba na mata da jakankuna cikin Ghana must go babba,da address din company gashi nan suyi business,su dinga siyarwa a cikin gida babu zuwa talla,ai kuwa haka akayi,iklas an kulla alaka da company nasu omar,banda jaka da takalmi har wasu abubuwan take sarowa suna saidawa a cikin gida ake zuwa ana siya,sai schl tana kaiwa.sosai suke samun kudi,ga schl me kyau,sutura me kyau,ci da sha zam zam,ga tsabta da kwalliya suna bugawa,gasu wayayyu sai suka kara kyau haske da kiba.

Tun zuwan omar na farko bai kara zuwa gidan su iklas ba,komai da yayi musu aike yayi dasu,su kuwa sun matsu su ganshi ko godiya suyi masa,amma shuru,gashi basu da number sa bare su nemeshi dan iklas ta siyawa ummi wata karamar tecno sabuwa,ita kuma ta siyi wata Samsung me kyau touchscreen,haka kawai iklas ta ji ta shiga damuwa na rashin ganin omar,

Kullum sai ta tunashi,shi kuwa omar a ganinsa har ga Allah ya taimaka musu badan wani abuba,me zaije gidansu yayi,me zaice dasu yayi aikin ladansa suzo suyi zarginsa ko da wata manufa yayi.shi yasa tace Sam bazai kuma lekasu ba,tunda komai yayi dai dai shike nan.amma me zuciyarsa kawai sai yaji yana son yaga lafiyarsu musamman iklas,yana so ya ganewa idonsa ya suka koma,

Baffan su omar yayo waya cewar bazai dawo ba sai nan da 2mnths,dan haka ya umarci daya daga cikin matansa ta bishi Russia, ai rahina wuta ta bude dole itace ta tafi Russia wurin baffa Wanda Sam baiso itace zata zo ba amma ya zaiyi.

A can ta dage tana ta kulla makirci,hade da kiran tsofaffin bokayenta tana danna musu kudi suna sheka aikinsu,sun bata tabbacin maman omar ba abinda zai iya cinta na tsafi dole tana nan daram,kuma baffa bazai daina sonta ba,dan haka tace to danfa a koreshi ya bar gidan,nan ma sukace shi zai iya tafiya amma bazai nisa da gidan ubansa ba,kuma dole zai dawo,cewa tayi koma yane ayi mata ya bar gidan.

Sahar kuwa tunda ta dawo yanzu tafi da fita gantali,dan yanzu tafiyar kwananki takeyi.tun omar na fada da damua ya gaji ya kyaleta.kowa harkarsa yakeyi.

Yau watan omar 1 da zuwa gidan su iklas,ya gaji da daurewa,yau dole ne yaje ya ga lafiyansu.saturday ba islamiyya ya sani,sanye yake cikin pencil wandon jean arsh color da farar Riga me rubutu da baki jiki,ga suma taci kudi,kai ka rantse bature ne 4:30pm ya parker wata jibgegiyar sabuwar motarsa a kofar gidan,da kyar ma ya gane gidan,dan ma ma'aikatan sun nuna masa a waya ne,knocking yayi suhaila ce ta bude sanye take da vest da wandonta iya Rabin cinya,gashinta yasha gyara,tun daga kallon suhaila yasan sunci gaba wlh.

Baki ta washe ta daka tsalle ta daneshi,oyoyo uncle,muna ta nemanka baka zo ba,to ai gani beauty yana murmushi kadan,sama ya shilla suhaila ya sabata a kafada suka shige gidan da sallama,kaka ummi ce ta fito tana amsa sallama..turus taja birki da mamaki tabbas wannan umaru ne da suke nema ido rufe domin suyi masa godiya,ummi baki har kunne ohhh dan nan yanzu sai yau kazo,muna ta jiran ganinka shuru,abubuwan arziki sai barkowa sukeyi ta hannunka,nanfa kaka tahau zuba godiya harda kukanta,daga nan ta fara yi masa hira,shi omar a bai son labari da yawa amma haka yake amsawa a dole,

Kuma yana jin dadin labarin da take masa domin masu amfanine sosai a wurin dan Adam,dan ita ummi bata surutun shirme a nutse take,suhaila kuwa tana cinyarsa ta lafe,

Iklas sanye take da wando 3qutr tight fari kal da riga dark blue,siririn gyale ta daura a kanta fari,tana kitchen ta gama shirya musu abinci ta gyara kitchen,sai surutun ummi take jiyowa dan ita bata ma San anyi wasu bako ba,wanka take so tayiwa suhaila itama tayi domin ita ke yiwa suhaila wanka saboda da wai suhaila jika jika takeyi kawai.fada sukeyi da suhaila sosai kan wanka,dan suhaila tace ta iya wankanta ita.

Da sauri ta fada palon da sallamarta....ummi wai surutun me kikeyi hakane?ina suhaila tazo na mata wank......bata karasa ba takai kallonta kan 2seater ai cik ta tsaya ganin Wanda ko a mafarki bata zata ba,ganinsa tayi ya kara kyau da kwarjini,ai da Saudi ta durkusa sannu da zuwa sir,ina yini,ya hanya? Da kyar ya amsa da lfy yana shan kamshi,ga fuskarsa ba rahama tamke,

Ganin yanda ya amsa mata bata samu karbuwa ba a wulakance,kamar bai Santa ba yasa ta mike tare da fadin taso suhaila na miki wankan,kafada suhaila ta make a jikin omar...ni anty na iya wankana fa zanyi da kaina,no ban yarda ba jika jikar da kikeyi,kinga baby dont waste my time ki taso na miki,ina da wurin zuwa.

Omar a ransa mamakin iklas yakeyi yanda takeyi acting kamar babbar mace bayan ita kanta iklas din bata wuce a mata wankan ba.

Ganin suhaila bata da niyar tashi yasa ta karasa wurin omar ta jawo hannun suhaila nan suka fara kokawa,suhaila ta tura hannun iklas da karfi ta hade hannun da kirjin omar sai kiciniya sukeyi iklas na kokarin zaro hannunta wani azabar bala'in shock ne ya shigi omar,bai San sanda yace shishsh a hankali,tana janyo hannun ta fara masa sannu da bada hakuri duk ta dauka bigeshi tayi yaji zafi,...tsawa ya buga mata get lost stupid kin takurawa yarinya,
Chapter 8 · 0% Book details