← Book details Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 57

Sashe 13

Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni kuwa nace su iklas badai iya karya ba.kwanciya sukayi kowannensu cike yake da tunani kala kala,iklas an kalli ceiling anyi kuri da ido ana tuno kasancewarta tare da Omar dazu,duk sonta da aikin gomnati sai taji da tayi tunanin salary ko ta gama schl ta fara aiki,ga mota tana ja,suna zaga kasashe ita da su suhailanta sai taji yanzu kamar tafi jin dadin tunanin oga omar,kawai fuskarsa in ta tuno dadi take ji,a'a juyi ta karayi taja tsaki,yanda omar ke daure fuska ta tuno sai taji sanyi,a ranta tace oh zuciyata yanzu fushin nasa ma birgeki yakeyi tab,da kyar bacci ya sace iklas,bangaren omar kuwa mugun mafarkin da yayi yake tunani,ga tunanin family dinsa musamman mama ko a wanne halin take oho,rayuwar da yake ciki yanzu ya tuno da iklas me kwai sai yaji dan sanyi a ransa,ya yanke shawarar yanda zai sa iklas ta masa wani acting yanda zaiji lafiyar mama da baffansa,hade da kwantar da hankalinsu,yasan iklas tsab zata iya,ko ya wannan abu zai kasance readers oho,za dai muji nan gaba.da wannan shima yayi bacci,

Da safe su iklas sunyi shirin schl,omar kuwa fitowa yayi so yake yaga ya hancin iklas yayi,uniform ya gani sun mata kyau,bai taba ganin wacce uniform yawa kyau haka ba irin iklas,kallo ya kare mata suka gaisar dashi,ummi ma ya gaisheta,iklas ya kalla ya kara fakar idon ummi ya dagawa iklas gira daya,hade da nuna hancinsa yana murmushi me kayatarwa,tasan tsokanarta yakeyi ba wani dubiya,baki ta turo,ta juya masa baya tana yaba muguntar omar,ummi ta juya tana gyarawa suhaila jaka ya dan ja hijab din iklas kadan,waigowa tayi itama ta dage masa gira daya,alama yake mata da hannu kamar kurame,kaka ummi ta tarfa su,sosai sun bata daria,umaru shirmen iklas kake kulawa ko,so kake ka koyi shiriritarta naga alama,ummi kalli hancin ta fa,hmmm umaru baka da dama ai jiya a bayi ta bige da kofa,ta dade tana habo,da kyar ta samu tayi bacci,daria omar yayi sosai jin karyar da iklas ta tafka,kallonta yayi suna hada ido ta kifta masa wai ya rufa mata asiri,kafada ya rike alamar yaki din,kaka ummi na kallonsu tace ohhh yau kuma umaru kurame kuka zama haka,wlh ka daina saurarar iklas,ummi wannan jikar taki bata ji ne cewar omar.

wani yaronsa daban Omar ya kara kira ya gwada masa gidan su iklas,dalleliyar wata motar omar ya dakko ya kai su iklas schl,sai kallon su iklas akeyi a schl.

Shima dai Wanda ya kai su iklas schl bai San daga ina omar ya kirashi ba,gashi ko wanne da new sim yake kiransu,kuma yan amanarsa yake sawa aikin Wanda yasan duk runtsi baza su bashi matsala ba,kowanne sai ya gargadeshi kar ya fadi ya kirashi a waya.

Iklas kam yau daga schl company ta wuce ta saro kaya,yaron omar ne ya kaisu ko ina ya dawo dasu gidansu sannan ya tafi

Kafin su iklas su dawo omar ya fadawa ummi zai aiki iklas gidansu ta gano masa lafiyar iyayensa,umaru kai da kanwarka sai ka nemi izinina,dadi yaji sosai su iklas na dawowa ya sata ta shirya cikin doguwar Riga da mayafinta,wajensa taje yana zaune tsakar gida a kan kujera sanye da Riga armless fara,da black jean gashin kansa ya kara yawa,

Ummi tana Palo suhaila na gefenta suna kallo da cin abinci,envelop ya mika mata nan ya Shiga tsara mata yanda zata yi acting a gidan nasu, hhhhhh iklas ta kama daria yanda taga Omar ya gwada maganar mata, kallonta ya tsaya yi,yanda daria ke matukar yi mata kyau, tsayawa tayi da dariar ganin omar ya kafeta da ido,daga bisani tace action ta fara gwada masa yanda ya koya mata har kara masa idea tayi,sosai sunji dadin moment din,iklas uwar shirme ji tayi inama suyi ta yin wannan film haka me dadi.

Kudi ya mika mata na taxi tare da address ta tafi kuwa.yau zata ga gidan su oga da family nasa,ya za aga haduwar su cewar iklas.

Sahar kam sai Allah ita cewa tayi Omar makaryacine yana can London munafiki za a ce ya bata kato dashi,to saceshi za ayi dan haka iyayenta suka ce ta dawo gida tayi zamanta tayi aikinta.haka kuwa akayi ta kwashe komai nata tas ta bar gidan cike da nishadi ta samu yanci.

Tun daga waje iklas take kallon haduwar gida kamar baza a mutu ba,gate ta buga,masu gadi wajen biyar suka leko ganin tsaleliya iklas suka ce wannan da gani kawar yan gidan nan ce,suma mamakin kyan iklas sukeyi kamar larabiya,gashi da ganin rigarta ta masu kudi ce,dama a rigunan da Omar ya batane tasa daya,

Da sauri sukace ta shiga suna ciki,tana shiga nan ta rantse a ranta da zata yi bacci ta farka ta ganta a wannan gidan to cewar zatayi ta mutu tana aljanna.

Asmabaffa
[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

25-30

By
Asmabaffa

Page din nan naki ne DIYAR KATIBI.

Tunani iklas tayi domin omar ya gwada mata yanda gidan nasu yake ba tare da tasha wahala ba ta gane part din maman omar,shiga tayi dakin part din tare da danna door bell din da omar ya fada mata,abdallah ne ya bude kofar,iklas dauke da hand bag a hannu an wani shanye hannu irin na wayayyun mata,kallon abdallah tayi da ganinsa kasan kanin oga omar ne,

Kallonsa iklas tayi pls mama nake nema,OK shigo tana ciki cewar abdallah sai bin iklas yakeyi da kallo yanda yaga baby me kyau haka,shiga ciki tayi salati take maimaitawa a ranta yanda taga tsaruwan palon,a kujera ta zauna abdallah kuma ya hau sama domin kiran mama,suleim ce ta fito cikin shirin islamiyya,sannu da zuwa ina yini cewar suleim,lfy zo mana mu gaisa cewar iklas,zama tayi kusa da iklas,can iklas ta kunna video recording a wayarta tana daukan suleim,wani katon pic din omar ta gani a palon,suleim waccen yayankine?ae anty amma ya bace,an nemeshi ba a Ganshi ba,mama kullum sai ta yi kuka tana ta addua,dady ma addua yace mana mu dinga yi,kinga su anty sadiya kuwa nurma sukeyi sosai,har kida suka kunna a gidan nan,suleim kwai surutu.

Yanzu in suka ganmu da mama suyi ta mana daria,kuma anty sahar matar yaya omar ta gudu gidansu wai ba za ta zauna gidansa ba,gaban iklas ne ya yanke ya fadi jin an ambaci matar yaya omar,dama yana da mata? Take taji wani bakin ciki a ranta,gabaa daya jikinta yayi sanyi,cikin kankanin lokaci suleim ta bawa iklas labarin gidansu,duk da batasan su waye anty sadiya ba,suna haka mama ta fito ita da abdallah,yi tayi kamar tana latsa waya nan kuwa video take musu,tsugunawa tayi cike da ladabi ta gaisar da mama,mama kuwa me aiki tasa ta kawowa iklas kayan motsa baki,

Ganin kalar girkin hadadde yasa iklas sauka kasa ta baje kamar gidan ubanta ta kama cin abincin cikin dabara takewa kanta video record tana cika baki da abinci,

Mama da abdallah har suleim daria sukeyi ita kuwa iklas tana sani tayi haka dan su saba da ita,sai da taci ta koshi sannan ta kalli mama tace mama wlh har na dawo hayyacina bakuga wahalar Dana sha ba kafin na gano gidan nan,kwashe kayan mama tasa akayi,yan mata meke tafe dake ne? inji mama,sultan ne yayi sallama ya shigo palon,iklas taso ta ganeshi amma ta rasa Inda ta sanshi,shima bangaren sultan hakan take sai kare mata kallo yakeyi ya kasa ganeta,domin tun iklas na tallan kwai ya taba ganinta,yanzu kuwa ta kara haske,kiba,kyau da girma.

Zama yayi suka gaisa da mama,iklas ma ta gaisar dashi,shi dai sultan wannan bai taba ganin me kyau irinta ba sai me tallan kwai da apple ta Frnd dinsa omar,kai har muryarma suna kama,amma wannan da gani yar masu kudi ce,waccen talakace haka Allah ke ikonsa wani ba dangi yayi kama da wani duk a ransa sultan ke wannan tunani.

Iklas ce taga sultan na kallonta,shima sai da ta masa video record,mama iklas ta kalla tace mama dama wannan na hoton tayi nuni da yatsanta jikin pic din omar dake jikin bango ne,harrrrr su mama sukayi aka zubawa iklas ido a ji bayaninta,naje company dinsu Neman aiki da dan dadewa,shine aka turani office dinsa naje interview,shine yace bazan samu aiki a company dinsu ba,amma nayi hakuri kuma yana Neman alfarmata na kawo wa mamansa sako,

Shi zaiyi tafiya ne,har naki karba amma ya dage,mama baki gani ba har kuka yayi kan sai nazo gida wajenki na baki sakon,Baku gani ba abin tausayi har kuka ya min cewar bashi da kowa da sukafi mama da baffa,sune farin cikinsa iklas ta karashe tana matsar kwalla,mama tace Allahu akbar da su suleim tuni hawaye na ambaliya a fuskarsu jin labarin omar,tabbas iklas ta tausaya musu amma ta dau alkawarin gano wannan lamarin dake faruwa da omar da family sa ko zata tallafa.

Sultan ke bawa su mama baki bayan sun nutsu iklas ta zaro envelop daga jakarta ta mikawa mama,wannan yace na kawo miki,Allah bai bani iko ba sai yau,

Mama batasan karantawa don bata so ta karantowa kanta bacin rai,sabo da wannan ta mikawa sultan takarda,sultan nutsuwa yayi yana karantawa can su mama suka ga yana daria da fara'a wannan ya nuna sakon dadi ne bana bacin rai ba.

Kwace takar dar mama tayi taga guntun rubutu ne ma,fara karantawa tayi kamar haka:

SALAM......MAMA NAYI MATUKAR KEWARKI BURINA KI DAGE MIN DA ADDUA INA DA MATSALA A LFYR JIKINA,KI BAWA BAFFA YA KARANTA DA KANNENA SULEIM DA ABDALLAH,NAYI KEWARKU,SULTAN MA ABASHI HAKURI,INA NAN A NIGERIA MAMA CIKIN KOSHIN LFY,BANYI NISA DAKU BA,ZAN DAWO SOON,KUNSAN BAZAN TABA YIN ABU BA KWAKWARAN DALILI BA,A SANARWA BAFFA NASAN SHIMA ZAI FAHIMTA.

Dadi mama taji dukkansu sai murna da jin dadi sukeyi,iklas kuwa sai video take musu,mama ce ta rungumeta yata yar albarka mun gode kwarai,kowa godiya yakewa iklas,mama tace yaushe ya baki sakon?ya kai week nawa?sati dayafa kenan cewar iklas,,take kowa ya kara cika da murna,suka tabbatar da Omar yana kusa kuma lfy yake,hankalinsu ya kwanta,

Dakin baffa mama ta nufa yana ciki ta shiga ta labarta masa komai tare da mika masa takardar,yana gamawa ya dago fuska cike da annuri,dama na fada miki ki kwantar da hankalinki yana nan ni nasan son namijin gaske ne, sai mu dage masa da addua,kira min yarinyar na ganta,
Chapter 13 · 0% Book details