← Book details Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 57

Sashe 33

Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gida yayi gida,bangaren su Umma a cika sosai da yan uwa da abokan arziki masu kwana,kawayen amare makil sashensu daban,bangaren su Mama ta gayyato yan uwanta suma na nesa sunzo da yawa zasu kwana,har a gama biki,Iklas hayaniya ta dameta ta gaji dan haka gani su Ummi na hada hadar biki basu San me takeyi ba kusan gaba daya a part din Omar takeyin komai ko yana nan ko baya nan wucewa takeyi ta dinga uzurinta ba ruwanta,akwatin kayan bikinta ta janyesu ta mayar dakinsa,
Iklas tsabar kadifiri har kawayenta hadaddu ta gayyato guda biyu wata yar gayu yar gidan wani kusar Gomnati suna ce mata ANGEL,sai wata yar wanka kyakyawa itama yar wani babban soja ce wato PRINCESS, unguwarsu taje ta fadawa kawarta arniya DAMI DAMZEL itama za aje da ita dan tana aiki a company tana kashe wanka duk cikinsu babu wacce za ace bata hadu ba.kuma iya dinner Iklas ta gayayyacesu suzo.
Ummi ma ta gayyaci mata tsofaffi irinta na tsohuwar unguwarsu mutum uku,Sa'ade,Hasiya da Maman saleem Haj kyauta.

Komai dai share.
Saleem duniya ta samu har sun canja unguwa ya siya musu gida shida mamansa sun koma cikin Abuja city,har yayi motar kansa,
Mamansa ta uzura masa ta gaji da zaman kadaici ya nemo matar aure,shi kuma Iklas ya fada mata yana so,sai tace ya bari idan taje musu biki zata sanarwa Ummi,sai murna yakeyi.
Umma Rahina yaranta ta Tara,kan kar su nunawa yan bangaren su Omar komai,idan ana bikinma su nuna komai daya, ana zaman lfy,kuma suja Iklas a jiki ayi komai dasu,yanda idan sunyi wata kulla kullar jama'a ba Wanda zai yarda cewar su suka aikata,dan tace ana gama biki zata fara harba makami me linzami na bama baman tsiyarta bangaren Mama,zasu sha wutar bala'oinsu.

An tashi yaune za ayi event har biyu daya 3pm-6pm za a dawo a koma na 9pm-3am ko wanne wajensa daban za ayi, Iklas ce ta wuce Omar a palonsa fiiii zata shige cikin bedroom,jawota yayi baya ina zakije haka,kinfa takurawa room dina, na gaji da wankemin bra da panties naki ke ba matata ba ko kunya bakyaji na gani,

To mene abin kunya a pant da bra amma a t.v settelite ai nagani rannan kana kallon american film da bra da pant jikinta kana kalla me yasa nan banga kaji kunya ba,sai idonka ma da naga ka kara warewa,
Ni ai na saba gani,ke nake nufi,baki ta murguda to Nima bana jin kunya agaban kowa zan iya shanyawa,da masifa Omar yace hey mind ur tongue,kar ki jawo na huce fushina kanki.
Ita Iklas duk haushin Omar takeji yaki cewa yana sonta, ta gaji da jiran sa.

Me zakiyi cikin Room din to, wankan party,no ki bari sai na 9pm zamuje.batayi musu ba tace to Allah kaimu.
Da hannu ya yafitota come come muga lallen da akiyi miki jiya,na mantama ban gani ba,a nutse ta wara masa hannayenta,kalla yayi sosai har na kafa dama gata fara kar, lallen ya gama tafiya da Omar, harda shafa hannun,gashin ma ba a magana, har mamaki yakeji yaushe Iklas tasan wurin gyara a Abuja haka.
Omar bai San aikin Mero Lallausa bane me gyaran jiki.
Zame hannuta Iklas tayi,tabe baki Omar yayi mutum ya biya kudi an hanashi ganin na kudinsa.
Je ki dafa min indomie da kwai,ki hada min coffee. Tafiya tayi cika umarnin Omar,Hips dinta yabi da mayen kallo.

8pm sai shirin dinner party akeyi, su Abdallah shi ke yawo dasu Suleim 8:30 sunyi shirunsu kajifa yara, bangaren Amare mafa nan ake cakarewa.
Iklas zata shiga wanka Omar ya sa key a toilet din wai baza suje da wuri ba,haka ta koma na Mama duk shirye shirye akeyi,ita kuma baza ta shiga toilet din da wasu yan biki suke shiga ba,sauran rooms du Mama tasa musu key.
Dolenta ta jira Omar sai abinda yace.9pm sannan Omar yace tayi wanka,10pm sun gama shiri tuni frnds din Iklas sunje can,sai waya suke mata,Sultan da amaryarsa Yasmin, Raj ma yaje.

Kwaalliyar su Iklas fa

INA TARE DAKU MUTANENA

Asmabaffa

ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

125-130

By
Asmabaffa

Iklas ce tayi shiri idan ba mugun saninta kayi ba baza ka gane ta ba,wani tsadajjen material tasa na nunawa a gari,Red ne da zanen Arsh color jiki, yayi mugun kyau,duk yafi na amare kyau da tsada,dan Omar ba karamin kudi ya zuba ya siya ba,Riga da skert ne,tasha kyau kamar Ku saceta dan tsayawa ma fadar yanda shape dinta ya fito bata baki ne, Omar yasan size dinta mayene.takalmi me tsini arsh da wata shegiyar pose yar gaske same color da shoe,Omar ya fito daga wanka sai da kyar ya tabbatar wannan Iklas ce,
Iklas fa har gwagwaro itama ta kai aka Nada mata na kece raini,gashin nan ta gyara jelar na reto a tsakiyar baya murtukekiya,ta fito da ita ta tsakiyar goggoro,dama ga jiki yasha gyara ko ina kyalli takeyi,turaruka kuwa sai da Omar ya koreta,zama tayi tana jiransa yana shiryawq tana ta guntse dariarta wai ganin sandar girman Omar a short wando,yana kalonta ta gefen ido,kin San Allah zanyi maganinki ki koma Palo ki jirani kan me zaki sani gaba ki dinga kallona kina daria,baki ta rufe da tafin hannu nayi shuru to.

Harara ya watsa mata yana ta shirinsa tana satar kallon jiki da kira me kyau irin na Omar, Allah ya bashi diri da kyau ga skin dinsa kalarta ta kwashewa Iklas Imani,
Wani rantsatsen yadi me taushi Omar ya sa,shara shara sosai arsh color kalar material din Iklas komai Arsh yasa,dinkin zamani dai dai jikinsa wandonma,Omar uban yan wanka suma taci wani gyara me kyau,tayi luf,turaruka ya fesa sosai,ya fito kwas rike da waya,Iklas ma wayarta fankaceceiya a hannunta,mikewa tayi daram ta isa wajensa yaya Omar kalli fa kayanka shara shara har singlet ana gani,wandonka ma dan an masa landing daga samane amma ai sai adinga hango uhmmm.....uhmm....da ka canja shadda ma ,ke jikinki ko nawa ina ruwanki cewar Omar.kowa ance miki irinki ne me kurawa mazan wasu ido,let's go idan zakije if not na tafi,
Ita Iklas kar a kallar mata kyallin fatar miji,gashi tasan dole Sahar tana can.

Hannunta ya rike suka fito duk gidan Shuru sai yan aiki da suke aikin gyara gida kafin a dawo.
Wata sabuwar mota fil arsh color itama Omar ya bawa driver key a baya suka kame kamar sune amarya da angon,kajifa yan fassion
Har wajen driver ya kaisu,tun daga waje zaka San wajen ya girmi me karamin karfi.
Sahar da frnds dinta an kwafe a kujera tana baza idon ganin Omar,dama su gulma ce ta kawosu da niyar wulakanta Iklas gaban mutane,
Amare da Angwaye ana kujera an fara shagali suna kallon masu rawa da liki,su Kansu Omar suke son gani saboda frnds dinsu su kalli haduwa,najja da sauran kannensu sai iyayi akeyi a fili ana kada hips,kaji kannen Amarya fa.Iklas ce ta masa rada pls ka fita munzo fa idan ka fita ka bude min kofa na fito a Gomnati ta.
Driver ne ya budewa Omar kofa.
Murmushi Omar yayi tare da fita cike da kasaita,omar kuwa zagayawa yayi ya budewa Gomnati itama ta fito,tana fitowa zuruf ta sakalo hannunta Dana Omar ta kara shigewa jikinsa kamar zata shige jikinsa gaba daya ba space da ko tsinke zai iya shiga.wani kar kar kawai Omar ke ji a cikin jininsa kawai Iklas yake bukata, kara manneta yayi suka tafi domin shiga hole din,

Duk Wanda yayi tozali dasu sai ya saki baki da ido dan kallon kyau irin nasu,ga iya wanka,ga shiga me tsada da ka gani ba sai ance ba,gasu sun birge masoya da gani wannan real love ne,dama Iklas tace bikine daga mota sai hole shi yasa taki daukan gyale,

Sultan da Raj suka fara gani cikin wurin,daria suka dinga yi sun San Iklas sarai, wuyan Sahar da frnds dinta kamar zai tsinke dan kallon su Omar,suma su Najja sai nunawa frnds Omar sukeyi ga yayansu babba,wajen da aka tanadar masa najja ta nuna masa suka zauna,Mama da Ummi suna can baya sunga su Omar har murmushi sukayi,Iklas ba dama cewar Ummi.

Duk Iklas ta kasa sakewa yanda taga yan mata na kallon Omar,kamar tayi kuka,shi kam Omar ta kansa yakeyi ganin Saleem a wajen su Angel kawayen Iklas,
Yayan amare aka kira kan ana so ya chashe a fili dama Iklas ta matsu su shiga fili rawar Igbo zatayi yau tace, ai kuwa kafin Omar ya juyo sai gani yayi Iklas har ta danyi doro kamar zatayi ruku'u tana ta kada hips,tafi da ihu fili ya dauka kafin kace me an rufeta da liki maza da mata,su Kansu su Sadiya ta birgesu rawar,
Maman waleeda ma sai liki takeyi sai da ta karar da yan kudin cefanen da Baban waleeda ya bayar na 1mnths,kinga ta kanki da me zasuyi girki,Jamila sule,Haj jamila duk sai balle bakin jaka sukeyi,Zulaihat da su Juwairiya duk an Hallara a fili,sai Diyar katibi me gyara fili ce tazo ta koresu kasa tukunna.

Omar sannan ya fara likiwa Iklas yan dubu dubu,itama mikewa tayi ta gama rawar ta fara barin kudi musamman Omar ya bata dama,masu DJ sun washe da Naira, Omar ne ya janye Iklas suka koma mazauninsu sai radar masifa yake mata kan tayi rawa,
Angwaye da Amare na fitowa suma sai da su Iklas suka yi ruwan kudi.su Aisha ransu ya fara baci fa anzo gidansu ana satar musu dukiyar Uba ana bawa wata banza,
Sahar takaici ya kamata ganin inda Iklas ke barin kudi Omar ne kuma yake bata,a gabansu ma ta karbi wasu,ita kuwa sahar taga ko time din da take matarsa baya bata haka.

Da kyar ya bar Iklas taje wajensu frnds dinta da saleem suka gaisa sai kiranta yake a waya ta dawo wajensu,komawa tayi ta barsu suma suna kallon ,tana zama Sahar ta karaso wajen,hararar Iklas Sahar tayi,Iklas ma ta rama harda karin Jan tsaki,
Chapter 33 · 0% Book details